’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo
Published: 3rd, November 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta ayyana ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Wannan mataki da rundunar ta ɗauka na zuwa ne bayan zargin Sowore da yunƙurin ta da zaune tsaye da kawo hargitsi da sunan zanga-zanga a Jihar Legas.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olorundare Jimoh, ya bayyana cewa tun da fari rundunar ta gargaɗi Sowore kan kada ya jagoranci wata zanga-zanga da aka gudanar kan wani rusau da hukumomi suka gudanar a yankin Oworonshoki na jihar.
Sai dai rundunar ta bayyana cewa Sowore ya yi wa gargaɗin nata kunnen-uwar-shegu, inda ya shirya mutane suka fita tituna domin gudanar da zanga-zanga duk da cewa shi bai halarta ba.
Ana iya tuna cewa dai, Sowore, wanda shi ne jagoran “Take It Back Movement”, ya yi barazanar gudanar da zanga-zanga a makonnin baya domin nuna adawa da rusa gidajen da gwamnati ta yi da sunan shirin sabunta birni a Jihar Legas.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Legas
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande da shugaban CMG Shen Haixiong, sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo.
A cewar ministan na Nijeriya, cikin shekaru 5 da suka gabata, dubban matasan kasar sun ci gajiyar tallafin karatu da shirye-shiryen horo da na musaya da Sin ta samar, kuma wannan hadin gwiwa da ake yi a aikace ya kara fahimta da aminci tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, a shirye ma’aikatarsa take ta karfafa hadin gwiwa da sassa masu ruwa da tsaki na kasar Sin wajen ci gaba da fadada shirye-shiryen musaya da na hadin gwiwa da suka shafi matasa.
A nasa bangare, Shen Haixiong ya ce a matsayinta na babbar kafar yada labarai dake watsa shirye shiryenta ga sassa daban daban na duniya, tashar talabijin ta CCTV dake karkashin CMG da abokan huldarta, za su yayata shawarar Sin ta jagorantar harkokin duniya da gabatar da tafarkin Sin na zamanantar da kanta da karfinta na kirkire kirkire a sabon zamani ga al’ummar duniya. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA