Yadda matata ta ɓace a Abuja aka tsince ta a Sakkwato
Published: 3rd, November 2025 GMT
Wani magidanci, Malam Jibrin Rabi’u, ya bayyana yadda matarsa, Khadijat Ado, ta ɓace a gidansu da ke unguwar Life Camp a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, sannan kuma aka gano ta a Sakkwato washegari.
Ya shaida wa wakilinmu da yammacin Lahadi, cewa ya dawo gida a ranar Alhamis, sai ya tarar da matarsa ba ta nan.
Malam Jibril ya ce, ya kira wani abokinsa ɗan sanda, wanda ya sanar da ofishin ’yan sanda na Life Camp, Gwarinpa da sauran sassan yankin bayan bincike na farko ya gagara gano inda take.
A cewarsa, na’urar CCTV da ke gidansu ta nuna yadda matarsa ta fita daga gidan cikin natsuwa, har sai da ta fita daga inda kyamarar ke iya ɗauka.
Allah Ya yi wa Malam Nata’ala rasuwa Fursunan da aka yanke wa hukuncin kisa ya tsere daga gidan yari a YobeMalam Jibrin ya ce duk da ƙoƙarin da suka yi na gano ta a ranar Alhamis ɗin, ba su samu nasara ba.
Sai dai ya ce da yammacin Juma’a aka kira shi aka shaida masa cewa an gano matarsa a Sakkwato, amma ba ta iya magana.
Ya ce, “Yanzu ma har yanzu ba ta iya magana ba, amma ta dawo cikin hayyacinta. Muna tattaunawa ta hanyar rubutu ne kawai.”
Ya bayyana cewa matarsa ta rubuto masa cewa a ranar da ta ɓace, ta ji kamar wani ana kiranta ne, sai ta buɗe ƙofa ta fita — daga nan kuma ba ta san abin da ya faru ba, sai da ta tsinci kanta a Sakkwato.
A cewar Malam Jibrin, “Ta ce da ta isa Sakkwato, ta haɗu da wata mace wadda ta roƙi takarda da biro, sannan ta rubuta mata abin da ya faru domin ba ta iya magana.”
Ya ce daga nan ne wannan matar ta kira shi, inda ya nemi ta da ta kai matarsa wurin danginsa da ke Sakkwato.
Malam Jibrin ya ce har yanzu matarsa tana Sakkwato, kuma ba ta samu damar yin magana ba, amma ya shirya tafiya Sakkwato yau domin ya dawo da ita gida.
Wata majiyar ’yan sanda a Life Camp ya tabbatar da cewa an kawo rahoton ɓacewar a ranar Alhamis, amma ya ce duk wani ƙarin bayani sai an tuntuɓi hedikwatar rundunar.
An kuma bayyana cewa kiraye-kirayen da aka yi wa jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sanda ta Abuja, DSP Josephine Adeh, ba ta ɗaga wayarta ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ɓace Sakkwato a ranar Alhamis
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura IsaTrump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.
“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”
Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.
“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.