Daga Aminu Dalhatu

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, bisa shirin tallafawa jama’a domin dogaro da kai da kuma inganta rayuwarsu.

Ta yi wannan yabo ne yayin bikin kaddamar da kayan tallafi a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa, kayayyakin da aka raba sun haɗa da motoci, babura, injinan dinki, injinan niƙa, keken guragu, kayan abinci da kuma tallafin kuɗi a fadin ƙaramar hukumar.

Ta bayyana shirin a matsayin abin yabo da ke tallafawa iyalai, wanda ke karfafa dogaro da kai, tare da rage matsin tattalin arziki a tsakanin al’umma.

Uwargidan Gwamnan ta taya waɗanda suka amfana da shirin murna, tare da shawartarsu da su yi amfani da kayan yadda ya kamata domin inganta rayuwarsu da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’umma.

A wani bangare kuma, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta karɓi tawagar mata da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun siyasa daban-daban zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki.

 

Uwargidan Gwamnan ta tabbatar wa sabbin mambobin jam’iyyar da cewa za a ba su dama da haɗin kai a dukkan harkokin jam’iyya, tare da kira gare su da su ba da goyon baya ga hangen nesan gwamnatin wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban tattalin arziki da dorewar cigaba a fadin jihar.

A nata jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, ya ce an shirya wannan tallafin ne domin taimakawa masu buƙata su  dogaro da kansu.

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Zamfara Uwargidan Gwamnan

এছাড়াও পড়ুন:

Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari.

 

Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance addini ko kabila, don haka bama bambantawa wajen bayar da tallafin. in sha Allah zamu ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a fadin jihar Kaduna baki daya.”

 

A nasa jawabin, Shugaban hukumar KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna muhimmancin dangantaka tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma dorewar tsarin inshorar lafiya ga kowa.

 

Ya kara da cewa kaddamar da inshorar lafiya kyauta na shekara guda babban ci gaba ne a cikin gyaran fannin lafiya da ake gudanarwa a jihar, inda ya yaba da kokarin gidauniyar IRM wajen tallafawa rayuwar al’ummar  Kaduna – Musulmai da Kiristoci.

 

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin daga Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen Kaduna da kuma kungiyar ci gaba ta Darikar Tijjaniyya ta jihar Kaduna sun bayyana farin ciki da godiya ga gidauniyar da kuma gwamnatin jihar, inda suka ce inshorar lafiya kyauta za ta rage musu nauyin kashe kudin magani tare da karfafa hadin kai a tsakanin al’umma da samar da zaman lafiya.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025 Ra'ayi Riga A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya? November 2, 2025 Labarai Maganin Nankarwa (3) November 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
  • Trump ya jaddada shirin Amurka na kai hari a Najeriya
  • Majalisar Karamar Hukumar Bubura Ta Kai Tallafin Kayayyakin Abinci Cibiyar Gyaran Hali
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
  • Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci Daga Yanzu