2025-10-14@08:25:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 901
«Layya»:
An yi kiciɓus da gawar wata budurwa mai shekaru 14 a cikin gidansu da ke unguwar Dandinshe a Ƙaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano. Lamarin dai ya ɗugunzuma mazauna unguwar yayin da Aminiya ta riski iyaye, ’yan uwa da kuma maƙwabta cikin alhini a yayin ziyarar da ta kai har gida. Hisbah ta haramta...
Albarkacin taron koli na Kungiyar Hadin Kan Shanghai (SCO) na 2025, an yi bikin kaddamarwa na kasashen SCO, da shiri mai taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” da CMG ta shirya a yau Litinin a nan birnin Beijing. Tun daga yau, za a fara watsa shirin a manyan gidajen talibijin na Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Pakistan,...

Sin Ta Shiga Jerin Kasashe 3 Dake Sahun Gaba Wajen Gudanar Da Cinikayya Da Kasashe Da Yankunan Duniya 157
Shugabar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta ce Sin ta shiga jerin kasashe uku dake sahun gaba wajen gudanar da cinikayya da kasashe da yankunan duniya 157. Sun Meijun, ta bayyana hakan ne a Litinin din nan yayin taron manema labarai da ta gudana, inda ta ce a shekarar 2024 darajar hada-hadar...
Matasa da dama a garin Kafanchan, da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, sun yi aikin gayya domin gyara hanyar garin. Sun yi amfani da gatari, fatanya, diga da sauran kayan aiki wajen yi wa hanyar gyara. Ɗaliba ta haɗu da ajalinta a hatsarin mota a Yobe Japan za ta bai wa Najeriya rancen...
Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe, ta sanar da korar tsohon ɗan takarar gwamnanta na shekarar 2015, Nafiu Bala, bisa zargin yi mata zagon ƙasa. Shugaban ADC na jihar, Auwal Abba Barde, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a Gombe. An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi Mutum...
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar da cewa gobe Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025, ita ce za ta zama 1 ga watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugaban kwamitin kula da harkokin addini a majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda ya bayyana...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka yi nasara a zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar a mazabu 16 a jihohi 12 na ƙasar nan. Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa shugaban...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Suna sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Kudancin Caucasus cikin lura Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i, ya yi nuni da yadda Iran ke daukan abubuwan da ke faruwa a yankin arewa maso yammacin kasar da muhimmanci, yana mai jaddada cewa: “Suna...

Babban Sakataren Majalisar Tsaron Kasar Iran Ya Bayyana Cewa; Ba Zasu Amince Da Shiga Tsakanin Iran Da Iraki Ba
Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba zasu yarda wasu kasashe su shiga tsakanin Iran da Iraki ba Yayin da yake magana game da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakanin Iran da Iraki, babban sakataren majalisar koli na tsaron kasar Iran Ali Larijani ya yi nuni da cewa: Bai kamata a...
Kungiyar AMA Foundation, tare da hadin gwiwar Kwalejin Gwamnatin Tarayya FGC Kaduna, sun hada karfi da karfe wajen ilmantar da marayu a jihar Kaduna. Ta wannan hadin gwiwa, marayu da suka kammala makarantar firamare a Hauwa’u Memorial School, wadda AMA Foundation ta kafa a Tudun Wada, Kaduna, suna samun damar shiga Makarantar Sakandare...
An bayyana sakamakon zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Zariya da kewaye, da kuma Mazabar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna. Zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da rahoton tashin hankali ba. Isa Haruna Ihamo na APC ya yi nasara A zaɓen da aka gudanar a Zariya,...
Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, ritaya Manjo-Janar Muhammadu Sani Sami, ya rasu yana da shekaru 81 a duniya. Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Garba Umar-Dutsinmari, ne ya tabbatar da rasuwar mai martaba a cikin wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi ranar Lahadi. Ya bayyana cewa Sarkin ya rasu ne...
Wata kotun tarayya a kasar Canada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan...
“Manufar ita ce a ninka adadin likitoci, ma’aikatan jinya, masu hada magunguna, kwararrun dakunan gwaje-gwaje da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya. Wannan ko shakka babu zai kara habaka harkokin kiwon lafiya a kasar,” in ji shi. Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bayyana cewa, a bana, TETFund ta samu tallafinta mafi girma na Naira Tiriliyan...
Ministan Ma’aikatar Kula da Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabon asibitin dabbobi, da cibiyar ajiye dabbobi, tare da samar da allurar rigakafi a Jihar Kwara. Ministan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon nazarin taswirar fadin jihar(Geospatial Mapping) da aka gudanar a Ilori babban...
Wata kotun tarayya a kasar Kanada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan...
Sabuwar mai bada shawara kan harkokin lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Maryam Bukar-Hassan (Alhan_islam) ta bayyana cewa samar da dauwamammen zaman lafiya a duniya shi ne fatansu. Maryam ta bayyana hakan ne a lokacin da babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohammed Malick Fall, ke maraba da ita...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya Bayyana cewa: Shugabannin gwamnatin nuna wariyar al’umma suna kokarin yaudarar al’ummar Iran A martaninsa ga fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ya yi a baya-bayan nan, shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Kasar Iran a yayin da yake gabatar da wasu takardu kan matsalar karancin ruwa da kuma matsalar...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Manufar Shugaba Trump Ta Korar Marasa Galihu
Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ya kuma nuna cewa, kaso 92 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na bayyana matukar damuwa game da tsaron rayukan al’ummun Amurka, yayin da kaso 81.7 bisa dari suka ce muggan laifuka, da karuwar masu kwana a kan tituna sun zamewa manyan biranen Amurka alakakai, lamarin da ya zamo...
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su. Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar...

Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Kan Batun Saka Wasu Sassa Cikin Wadanda Ta Sanyawa Takunkumin Sayar Musu Da Kayayyaki
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana a yau Talata 12 ga wata cewa, bisa dokoki ko ka’idojin da suka shafi saka wasu sassa cikin wadanda aka sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, ma’aikatar ta fitar da sanarwa mai lamba 21 da ta 22 a ranar 4 da kuma ranar 9...

Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm
Biyo bayan sanarwar hadin gwiwa bayan taro kan tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin Sin da Amurka a birnin Geneva a ranar 12 ga watan Mayun 2025 wato sanarwar Geneva, da tarukan da aka yi a birnin London a ranekun 9 da 10 ga watan Yunin 2025, da wanda aka yi a Stockholm...

Mahukuntan Iraki Sun Bayyana Cewa: Akwai Yiwuwar Masu Ziyarar Arba’een Na Imam Husaini {a.s} Zasu Zarce Miliyan 4
Birnin Karbala mai tsarki na sa ran karbar bakwancin masu ziyara sama da miliyan 4 daga kasashen ketare domin gudanar da juyayin Arbaeen Jama’a masu dimbin yawa na tururuwa zuwa birnin Karbala mai tsarki daga Najaf domin halartar yuyayin ranar Arbaeen a cikin tsauraran matakan tsaro da na hidima. Wakilin Al-Alam da ke kan titin...
Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen ruwan sama mai karfi da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 15 na Arewacin Najeriya da wasu wurare 68, a cikin kwanaki biyar masu zuwa. Wannan gargadi ya fito ne daga Cibiyar Lura da Gargadin Ambaliya ta Kasa, karkashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, inda aka bukaci hukumomi da al’umma...
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan...
Don haka, kwamishinan ya gode wa ƙungiyar bisa wannan ziyara tare da bayyana shirin Ma’aikatar na yin haɗin gwiwa da haɗin gwiwa ta fuskar horarwa, wayar da kan jama’a, da wayar da kan jama’a game da SGBƁ. Tun da farko, Misis Achimugu ta bayyana cewa ziyarar bayar da shawarwarin ita ce kashi na biyu na...

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar
Jakadan kasar Sin da ke Najeriya, Yu Dunhai, ya gana a kwanan nan da ministar kula da harkokin masana’antu, da cinikayya, da zuba jari ta tarayyar Najeriya, madam Jumoke Oduwole. Jakada Yu ya bayyana cewa, tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci kasar Sin tare da halartar taron koli na Beijing na dandalin...
Ganawar da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan da shugabannin wasu ƙasashe biyar dake nahiyar Afirka, ita ma ta janyo hankalin al’ummun duniya. Inda shugaba Trump ya yabawa shugaban ƙasar Laberiya Joseph Boakai kan yadda ya iya Turancin Ingilishi sosai, lamarin da ya bayyana rashin fahimtarsa kan alaƙar tarihi tsakanin ƙasar Laberiya da Amurka....
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta...
Hukumar NAHCON mai kula da sha’anin aikin Hajji a Nijeriya NAHCON, ta bayyana cewa an ƙayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alƙalami na kuɗin kujerar aikin Hajjin 2026. NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin...
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta bayyana alhinita kan kisan gilla da aka yi wa Umar Abdullahi Hafizi, dalibi da ke matakin karatu na 3 a Sashen Ilimin Zamantakewa (Sociology), wanda wasu masu kwacen waya suka daba wa wuka har lahira a gidansa da ke unguwar Dorayi a ƙaramar hukumar Gwale. Wannan na ƙunshe...
Matasan Kauru Sun zargin Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin tabuka komai Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa. A...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana bukatar samar da wata sabuwar hanyar yin mu’amala da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, inda ya bayyana cewa, ba a kayyade lokacin shiga wasu shawarwari da Amurka ba, ya kuma tabo batun muhimmancin dangantakar dake tsakanin Iran da kasashen Rasha, Sin...
Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba. Alkali, na fama da rashin lafiya tun a bara wanda hakan ya sa bai sake bayyana a bainar jama’a ba. Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi Gwamna ya...
Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba. Alkali, na fama da rashin lafiya tun a bara wanda hakan ya sa bai sake bayyana a bainar jama’a ba. Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi Gwamna ya...
Ofishin jakadancin kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kausasan kalamai kan rahotannin dake cewa tsohon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ziyarci yankin Taiwan na Sin da kiran da ya yi wa kasashen yamma su kulla huldar tattalin arziki da yankin. Wani kakakin ofishin jakadancin ya bayyana a jiya cewa, suna adawa matuka da...
Za a fara watsa shirin talabijin na musamman mai mai taken “Karfin Al’adu – Tushe da Aikace-Aikacen Tunanin Al’adu na Xi Jinping a Zhejiang”, ta kafar tashar telabijin ta CCTV-1 ta kamfanin CMG, daga yau Laraba 6 ga watan Agustan nan. Za a rika watsa shiri daya duk rana, daga shirin mai jimillar kaso hudu....
Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya. Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi...
Malaman jami’o’i sama da 100 daga Isra’ila sun bayyana cewar jan kafar da ƙasar Jamus ke yi wajen ɗaukar matakin matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila na iya bai wa ƙasar damar ci gaba da aikata manyan laifuffuka a Gaza. Wata wasika da masanan suka rubuta wa ɗaya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar SPD da ke...
A dai dai lokacinda ake yaki na kwanaki 12 tsakanin Iran da HKI da Amurka, daga ranar 13-24 na watan Yunin da ya gabata, cibiyoyin yakin yanar gizo na kasar Iran sun gwada karfinsu da kuma kwarewansu a wannan fagen fama. Kanfanin dillancin labarai na Tasnim na kuma kasar Iran ya nakalto sharhin wasu kafafen...
Dokta Muhammad Tahir da aka yi wa barazanar kisa ya bayyana abin da ya gani na masifa a Gaza Dr. Muhammad Taher ya dauki kashe-kashe da kakaba yunwa da ke faruwa a Gaza a matsayin abin tunawa da abin da ya faru da Imam Husaini (a.s), kuma Gaza ita ce Karbala ta wannan zamani. A...
Rahotanni sun bayyana cewa, fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda Bello Turji ya mika wuya tare da sako wasu mutane 32 da aka yi garkuwa da su, biyo bayan wani shirin zaman lafiya da malaman addinin musulunci suka yi a jihar Zamfara. Wani fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah ne...
Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle. Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu....

Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida a matsayin martani ga harajin Trump
Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida da kashi 30% na bangaren da harajin Amurka ya shafa a wannan makon, tare da kebe wasu ka’idojin samun wannan tallafin kudi. Kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kwashe watanni tana kokarin tattaunawa da Washington, inda ta yi tayin sayen...
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina zagin malaman addini da a yanzu ya zama ruwan dare a ƙasar nan. Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin zarafi malaman addini na iya lalata zamantakewa da tubalin zaman lafiya a tsakanin...
Jaridar Le Monde ta bayyana cewa: Tallafin kayan da jiragen sama suke saukarwa a Gaza tamkar digon ruwa ne idan aka kwatanta girman bukatun al’ummar yankin Jaridar Le Monde ta ruwaito cewa, ko da yake hukumomin mamayar Isra’ila, a karkashin matsin lamba na kasa da kasa, sun ba da izinin saukar da kayan agajin abinci...
Shirin Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa (MNCH) a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ya samu gagarumar nasara, inda mata da yara da dama suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta iri-iri. Wannan kamfen na mako guda, wanda Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa suka tallafa masa, na...
Tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Wukari/Ibi ta jihar Taraba a majalisar wakilai, Hon. Shiddi Danjuma Usman ya fice daga jam’iyyar APC. Usman ya bayyana rikicin cikin gida na jam’iyyar da rashin bin ka’idojin dimokuradiyya a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar. ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara Gwamnatin...

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Bayyana Cewa: Masu Shirin Halaka Gaza Suna Son Mamaye Duniyar Musulmi Ne
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Masu shirin halaka Gaza suna neman hadiye duniyar Musulunci ne Dakarun kare juyin juya halin Musulunci nanIran sun yi gargadin cewa; Bangarorin da ke shirya kisan kiyashi a Gaza ba wai kawai halakar al’ummar Falastinu ba ne kawai, a’a suna neman mamaye yankuna masu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp