Aminiya:
2025-11-27@21:14:37 GMT

APC ya lashe zaɓen cike gurbi a Zariya

Published: 17th, August 2025 GMT

An bayyana sakamakon zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Zariya da kewaye, da kuma Mazabar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna.

Zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da rahoton tashin hankali ba.

Isa Haruna Ihamo na APC ya yi nasara

A zaɓen da aka gudanar a Zariya, Isa Haruna Ihamo na jam’iyyar APC ne ya samu nasara da ƙuri’u 26,613.

Nuhu Sada Abdullahi na jam’iyyar SDP ya zo na biyu da ƙuri’u 5,721, yayin da Mahmud Abdullahi Wappa na PDP ya samu ƙuri’u 5,331.

Tun watan Ramadan muke cikin duhu — Al’ummar Jauro Jatau NNPP ta lashe zaɓen Bagwai/Shanono a Kano

Farfesa Balarabe Abdullahi, wanda ya bayyana sakamakon zaɓen, ya tabbatar da cewa Isa Haruna Ihamo ya cika dukkan sharuddan da ake buƙata don lashe zaɓen.

APC ta ƙara yin nasara a Mazaɓar Basawa

A Mazaɓar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Farfesa Nasiru Rabi’u ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen da ƙuri’u 10,926, sai PDP ke biye da ƙuri’u 5,499.

Zaɓe cikin kwanciyar hankali

Rahotanni sun tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin lumana ba tare da wata hayaniya ko rikici ba, lamarin da ya kara tabbatar da sahihancin sakamakon.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: lashe zaɓen

এছাড়াও পড়ুন:

Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas

Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta.

El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya

Bayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya.

Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin cewa matar ta kashe yarinyar ce a gidanta bayan ta je har makarantarsu ta ɗauko ta ba tare da izinin mahaifiyarta ba.

Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce an kai gawar yarinyar ɗakin ajiye gawa domin bai wa likitoci damar kammala bincikensu na kimiyya gabanin soma nasu binciken.

“Mun ziyarci wurin da abin ya faru, mun ɗauki hotuna, kuma an garzaya da su asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsu.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
  • Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina