Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar
Published: 14th, August 2025 GMT
Sabuwar mai bada shawara kan harkokin lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Maryam Bukar-Hassan (Alhan_islam) ta bayyana cewa samar da dauwamammen zaman lafiya a duniya shi ne fatansu.
Maryam ta bayyana hakan ne a lokacin da babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohammed Malick Fall, ke maraba da ita a ofishin majalisar da ke Abuja.
Mohammed ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, yana mai cewa zaman lafiya wani abu ne da ake buƙata don jin daɗin rayuwar ɗan Adam, kuma idan ba a same shi ba, ci gaban dimokuraɗiyya da kuma ’yancin ɗan Adam ba zai samu ba.
Ya bayyana damuwarsa kan yadda aka sake samun ɓullar tashe-tashen hankula a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya, yana mai cewa hakan koma baya ne ga ci gaban da aka samu tun kafuwar MDD shekara 80 da suka gabata.
Da take nata jawabin Maryam Bukar Hassan ta ce, akwai buƙatar a samar da wani shiri na kawo sauyi wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Har ila yau, Mohammed Fall ya yaba da yadda aka naɗa Maryam Bukar-Hassan a matsayin, ya ce hakan yazo a daidai lokacin da ya dace kuma mai mahimmanci, yana mai bayyana irin ƙarfin gwiwar da yake da shi akanta na za ta sauke nauyin da aka ɗora mata, mussaman wajen isa ga al’umma da matasa ta hanyoyin diflomasiya.
Yana mai cewa, “Ku ne muryar matasa, muryar jagorancin mata,” in ji shi. Ya kuma jaddada irin rawar da taka wajen tsara makomar neman zaman lafiya.
Ya kuma bayyana cewa, nauyin da ke kanta ya yi fice a Nijeriya har zuwa ayyukan da duniya ke yi. Duk da irin rawar da take takawa a duniya, Fall ya ba ta tabbacin goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya.
Hakazalika Maryam Bukar-Hassan ya jaddada cewa, idan har ba zaman lafiya ba, yadda za a iya cimma muradun ci gaba mai ɗorewa (SDGs) kuma zai kasance mara amfani.
“Ba maganar talauci idan zaman lafiya da yin adalci sun tabbata,” in ji ta,
Ta kuma ƙara da cewar, tabbatar da yunƙurin zaman lafiya ta hanyar haɗa harsunan asalin ƙabilu da al’adu na gargajiya ne fatanmu dole mu haɗa da harshen Ingilishi,” in ji ta.
Idan har muna son mu kai ga cimma nasara dole ne, mu komo hanyar yadda da al’ummominmu suka tsara. Wannan hanya na nufin tabbatar da gina zaman lafiya mai ɗorewa, musamman a yankunan da asalin al’adu ke taka muhimmiyar rawa a cikin zamantakewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Ɗinkin Duniya Zaman lafiya Maryam Bukar Hassan zaman lafiya mai ɗorewa
এছাড়াও পড়ুন:
An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies.
Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci.
An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara baDokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci gaba ɗaya.
Indonesia na daga cikin ƙasashen da har yanzu ake cin naman karnuka da kyanwa, duk da cewa wasu birane sun daina wannan al’ada a ’yan shekarun nan.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi sun yaba da sabon matakin, suna mai cewa ya dace da manufofin kare lafiyar al’umma.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce mutane da dama kan mutu da cutar rabies a kowace shekara a Indonesia, inda rahoton Ma’aikatar Lafiya ya nuna cewa mutane 25 suka mutu daga watan Janairu zuwa Maris 2025.
Duk da cewa a yawancin yankunan Indonesia ana kallon karnuka a matsayin dabbobin da ba su da tsabta, wasu ƙananan ƙabilu na ci har yanzu, musamman ma saboda samun naman a farashi mai sauƙi.