Kungiyar AMA Foundation, tare da hadin gwiwar Kwalejin Gwamnatin Tarayya FGC Kaduna, sun hada karfi da karfe wajen ilmantar da marayu a jihar Kaduna.

 

Ta wannan hadin gwiwa, marayu da suka kammala makarantar firamare a Hauwa’u Memorial School, wadda AMA Foundation ta kafa a Tudun Wada, Kaduna, suna samun damar shiga Makarantar Sakandare na Gwamnatin Tarayya kai tsaye.

 

Yayin taron Annual Speech and Prize-Giving Ceremony na makarantar, Shugaban makarantar Hauwa’u Memorial, Nasir Musa, wanda ya wakilci AMA Foundation, ya bayyana cewa yanzu haka ana daukar nauyin marayu 120 a makarantar firamare, wasu 120 a Makarantar Sakandare na FGC Kaduna, sannan dalibai 16 sun samu gurbin shiga Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).

Ya jinjina wa wanda ya assasa wannan makarantara Alhaji Musa Bello, saboda kafa wannan gagarumin aikin da ke mayar da hankali wajen kula da marayu, yana mai cewa hakan zai basu damar cika burinsu.

 

Babban malamin makarantar FGC Kaduna, Prince Adewale Adeyanju, shi ma ya yaba wa AMA Foundation saboda daukar nauyin karatun marayu daga firamare har jami’a, yana mai bayyana shi a matsayin kyawawan abubuwan da mutum zai iya bayarwa ga al’umma.

 

Ya bayyana cewa dukkan daliban da aka dauki nauyi a wannan shekara sun kammala da sakamako mai kyau, wanda zai ba su damar samun gurbi a manyan jami’o’i a duniya.

 

A nashi jawabin, a madadin Shugabar Asibitin Ido na Tarayya dake Kaduna, Dr. Amina Hassan, Dr. Sadiq Muhammad ya bayyana gamsuwarsa da irin ilimin da aka ba wa wadannan marayun.

Ya kuma yi kira ga sauran masu hali su yi koyi da wannan irin wannan kyautatawa.

 

Shugaban Daliban Maza wato Head Boy, Ibrahim Usman Waziri, da ta bangaren mata, Hafsat Adam Waziri, sun nuna farin cikinsu da kasancewa cikin daliban da suka kammala.

 

Sun yi kira ga iyaye su tabbatar da ganin ‘ya’yansu sun samu ilimin addinin Musulunci da na zamani tare.

 

Iyaye da ‘yan uwa na wasu daga cikin daliban da suka kammala, ciki har da Asmau Ahmed da Sabi Yusuf (uwa da kawu), sun gode wa AMA Foundation saboda damar da ta ba ‘ya’yansu wajen canza rayuwarsu.

 

A yayin bikin kaddamar da littafi da aka gudanar a wajen taron, Babban Daraktar na AMA Foundation, Aisha Yusuf Mamman, wacce ba ta samu halarta ba ta aiko da sakon fatan alheri, yayin da Mataimakiyar Babban Darakta, Fatima Bala Jafar, ta bada gudunmawar naira ₦50,000.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jihar Kaduna Marayuy Tallafawa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Nada Kwamishina Na Farko A Ma’aikatar Cigaban Kiwon Dabbobi

Gwamna Malam Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana harkar kiwon dabbobi a matsayin babbar harkar tattalin arziki ta biyu a jihar baya ga noma.

Ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamishina na farko na ma’aikatar ci gaban kiwon dabbobi da aka kafa kwanan nan, Farfesa Salim Abdurrahman Lawal, a zauren majalisar zartarwa na gidan gwamnati da ke Dutse.

A cewarsa, baya ga noma, kiwon dabbobi shi ne babban abin da mutanen jihar Jigawa suka sanya a gaba.

Malam Umar Namadi ya kara da cewa kafa wannan ma’aikata na cikin shirin gwamnati na bude manyan damarmaki da ke cikin wannan bangare.

“Mun dauki mataki na musamman domin ingantawa da bunkasa bangaren kiwon dabbobi. Mun yi hadin gwiwa da dama, mun yi tuntuba da dama, kuma nan gaba kadan za a fara ganin sakamakon wannan tuntuba. Bisa wannan dalili muka ga ya dace mu kafa ma’aikatar da za ta jagoranci wannan aiki gaba.”

Game da zaben kwamishina na farko, Gwamna Namadi ya bayyana kwarin gwiwa a kan kwarewar Farfesa Salim Abdurrahman.

“Mutumin da aka rantsar a matsayin kwamishina na kiwon dabbobi, kwararre ne kuma masanin a wannan fannin. Daga digirinsa na farko zuwa na biyu  har na uku (PhD), duk ya yi su ne akan ilimin dabbobi. Don haka babu wani da ya fi dacewa da wannan aiki fiye da Farfesa Salim.”

Yayin da yake taya Farfesa Salim Abdurrahman murna, Gwamnan ya tunasar da shi muhimmancin wannan mukami na farko da yake rike da shi, yana mai kira gare shi da ya yi aiki domin amfanin jama’ar jihar Jigawa.

“Ina sanar da kai cewa kana daf da kafa tarihi domin kai ne kwamishina na farko na wannan ma’aikata. Don haka idan ma’aikatar ta yi tasiri ga rayuwar mutanen jihar Jigawa, tarihi zai yi alfahari da kai”.

Namadi ya yi addu’ar samun nasarar wannan ma’aikata wajen inganta rayuwar al’umma a fadin jihar.

 

Usman Mohammed Zaria

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sarkin Zuru ya rasu yana da shekara 81
  • Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa
  • An kafa dokar hana zance tsakanin saurayi da budurwa a Kano
  • Tetfund Ta Samar Da Naira Biliyan 100 Don Inganta Ilimin Likitanci – Masari
  • Ma’aikatan Sufurin Jiregen Sama Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Shirin Sayar Da Filayen Jiragen Sama
  • Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Asibitin Dabbobi A Jihar Kwara
  • Gwamna Namadi Ya Nada Kwamishina Na Farko A Ma’aikatar Cigaban Kiwon Dabbobi
  • Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe
  • Gidauniya Ta Rabar Da Buhun Takin Zamani 6,000 Ga Manoma A Bauchi