An yi kiciɓus da gawar ’yar shekara 14 a cikin gida a Kano
Published: 26th, August 2025 GMT
An yi kiciɓus da gawar wata budurwa mai shekaru 14 a cikin gidansu da ke unguwar Dandinshe a Ƙaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano.
Lamarin dai ya ɗugunzuma mazauna unguwar yayin da Aminiya ta riski iyaye, ’yan uwa da kuma maƙwabta cikin alhini a yayin ziyarar da ta kai har gida.
Hisbah ta haramta al’adun gargajiya yayin bukukuwan aure a Bauchi Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin AmurkaBayanai sun ce an yi arba da gawar Fatima Sulaiman rataye a jikin wata taga a cikin gidansu, lamarin da ya jefa shakku da ayoyin tambaya kan musabbabin mutuwarta.
Aminiya ta zanta da mahaifiyar marigayiyar, Malama Madina Inuwa Makwalla, wadda ta bayyana ganawa ta ƙarshe da ta yi da ’yarta.
“A ranar Asabar da yamma, muna shirin kai ziyara asibiti domin duba wani ɗan uwanmu.
“Da muka shirya tafiya, sai Fatima ta ce za ta shiga bandaki sannan ta biyo mu. Ashe ban sani ba, wannan ne karo na ƙarshe da zan gana da ita,” a cewar Madina tana faɗa cikin hawaye.
Mahaifiyar ta bayyana cewa har suka dawo daga asibiti Fatima ba ta biyo su ba, inda suka tarar da ƙofar gidan an kulle ta daga ciki, kuma duk wani yunƙurin buɗewa da suka yi da safayar makullin da ke hannunsu ya ci tura.
A wannan lokacin ne mahaifinta, Malam Sulaiman, wanda ya dawo daga kasuwa, ya haura ta katanga ya shiga gida, inda ya yi arba da abin da ba zai taɓa mantawa a rayuwarsa ba kamar yadda Malama Madina ta bayyana.
“Ya tarar da ɗiyarmu a rataye, babu rai. Ya yi matuƙar firgita, nan da nan ya kira ni, wanda ihun da na yi ya ankarar da maƙwabta suka yi ta taruwa,” in ji Malama Madina.
Mazauna unguwar da suka yi dandazon ganewa idanunsu wannan abun al’ajabi, sun bayyana shakku kan lamarin da cewa da yiwuwar akwai hannun wani, saboda alamu sun nuna an karya wuyanta kafin a rataye ta.
Mahaifin marigayiyar ya tabbatar cewa nan take suka sanar da ’yan sanda, waɗanda suka iso wurin, suka ɗauki gawar zuwa Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad, inda likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi mata halinsa tun kafin su kawo ta.
A cewarsa, “ba mu san wanda zai aikata wannan mummunan aiki ba. Amma muna kira ga hukumomin tsaro da su binciki lamarin sosai domin a gano masu hannu a ciki.
“Mun bar wa Allah wannan lamari. Muna roƙonSa Ya tona asirin duk wanda ya aikata wannan laifi. Allah Ya sa Aljannah ce makomarta.”
Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun soma cikakken bincike domin gano haƙiƙanin abinda ya faru domin tabbatar da adalci.
Maƙwabta da suka zanta da wakilinmu sun bayyana Fatima a matsayin yarinya mai ladabi, biyayya da girmama kowa.
“An santa da mutunci da zaman lafiya da kowa a unguwa. Wannan mutuwa ta girgiza mu gaba ɗaya,” in ji wani maƙwabci.
Tuni dai an binne gawar Fatima bisa koyarwar addinin Islama, inda ɗaruruwan jama’a suka halarci jana’izarta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: budurwa Jihar Kano
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.
Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.
Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.
Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.
Sai dai kasa da wata guda da kulla yarjejeniyar, an tattaro cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a Zamfara inda suka yi awon gaba da masallata da dama.
Wata majiya ta cikin garin, ta shaida cewa, harin ya afku ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa masallacin, suka kewaye shi, sannan suka tattara masallatan zuwa daji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp