Aminiya:
2025-08-14@07:10:37 GMT

Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda

Published: 14th, August 2025 GMT

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su.

Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu a Nijeriya Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3

A ranar Laraba, ya ziyarci ƙauyuka biyar da abin ya fi shafa; Banga, Sakajiki, Kuryar Madaro, Maguru, da Tambarawa, inda mutane da dama suka rasa ’yan uwansu.

Bayan samun labarin hare-haren, nan da nan ya tura mataimakinsa ya je ya jajanta wa mutanen da abin ya shafa.

Bayan dawowarsa Gusau, ya je da kansa ya duba ɓarnar da aka yi tare da yi wa iyalan mamatan ta’aziyya.

Ya bayyana maharan a matsayin maƙiyan zaman lafiya da ke son haifar da tsoro da rikice-rikice, sannan ya roƙi jama’a su ci gaba da addu’a don kawo ƙarshen aikata laifuka a jihar.

Gwamnan, ya yi alƙawarin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ’yan bindiga ta hanyar amfani da sabbin dabaru da ƙarfafa haɗin gwiwa.

Sarkin Kauran Namoda, Dakta Sunusi Ahmad, ya yaba wa gwamnan bisa ziyarar da ya kai, inda ya bayyana cewa hakan ya ƙarfafa guiwar mutanen yankin.

Haka kuma, Gwamna Lawal, ya sanar da shirin inganta rayuwar jama’a ta hanyar gyaran hanyoyi, samar da wutar lantarki, ruwan sha, da inganta sadarwar wayar salula a yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gwamna Dauda hare hare Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

An Yi Allah Wadai Da Hana Amfani Da Hijabi A Jami’ar LandMark, Omu-Aran Kwara

Kungiyar Muslim Media Watch Group ta Najeriya ta yi Allah-wadai da wata sanarwa da ake zargin Bishop David Oyedepo kan amfani da hijabi da daliban Musulman Jami’ar Landmark ta Omu-Aran ta Jihar Kwara suka yi.

 

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun wakilinta na kasa Sheikh Abu Sheriff, kungiyar ta yi Allah wadai da Bishop David Oyedepo da take hakkin dalibai musulmi da ma’aikatan cibiyar da ke da hakkin dan Adam kamar yadda sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar.

 

A cewarsa a cikin wani faifan bidiyo da aka yada sosai, Oyedepo ya yi kira ga iyaye da masu kula da Musulmai da su janye ‘ya’yansu mata idan suka dage ba za ayi amfani da hijabi ba.

 

Kungiyar ta bayyana dokar hana amfani da hijabi a jami’ar Landmark Omu-Aran a matsayin ‘wani abin da ba za a lamunta dashi ba’ kuma tauye hakkin addini ne.

 

Ya yi nuni da cewa ba a daukar musulmi aiki a wannan jami’a, kuma idan aka dauki shi bisa kuskure, to ba za su barshi yin salloli sau 5 ko azumin watan Ramadan ba.

 

Kungiyar ta ci gaba da cewa haramta wa dalibai musulmi ‘yancin yin amfani da hijabi cin zarafi ne ga ‘yancin yin imani da ibadarsu.

 

Sanarwar ta bayyana cewa neman iyaye da su janye ‘ya’yansu saboda amfani da Hijabi yana tauye musu hakkinsu na dan Adam.

 

Kungiyar ta kuma yi kira ga ma’aikatar ilimi ta tarayya, NUC, NBTE da sauran su da su binciki duk masu take hakkin dan adam a cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan.

 

REL/ALI MUHAMMAD RABIU

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwaman Zamfara
  • Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan
  • Gwamna Bago Ya Yabawa Tinubu Kan Kama Shugaban Kungiyar Ta’addanci A Neja
  • EFCC Ta Bayar Da Belin Tambuwal, Ta Yi Allah-wadai Da Zargin Da Jam’iyar ADC Ta Yi
  • Iran ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa ‘yan jarida a Gaza
  • An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK
  • Mahukuntan Iraki Sun Bayyana Cewa: Akwai Yiwuwar Masu Ziyarar Arba’een Na Imam Husaini {a.s} Zasu Zarce Miliyan 4
  • U Reporters Sun Gudanar Da Taron Wayar Da Kan Jama’a Game Da Shayarwa A Kano
  • An Yi Allah Wadai Da Hana Amfani Da Hijabi A Jami’ar LandMark, Omu-Aran Kwara