Tetfund Ta Samar Da Naira Biliyan 100 Don Inganta Ilimin Likitanci – Masari
Published: 15th, August 2025 GMT
“Manufar ita ce a ninka adadin likitoci, ma’aikatan jinya, masu hada magunguna, kwararrun dakunan gwaje-gwaje da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya. Wannan ko shakka babu zai kara habaka harkokin kiwon lafiya a kasar,” in ji shi.
Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bayyana cewa, a bana, TETFund ta samu tallafinta mafi girma na Naira Tiriliyan 1.
Masari ya bayyana cewa, daga cikin Naira Tiriliyan 1.65, an fitar da Naira biliyan 225 zuwa asusun bayar da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND), domin shirin rancen daliban gwamnatin tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Masari
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Majalisa Na Ba Da Cin Hancin Har Naira Miliyan 3 Kafin Su Iya Gabatar Da Ƙudiri – Kamfani.
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi.
“Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, sai an biya kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, sai ka bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.”
Dan majalisar ya kuma yi watsi da zarge-zargen da ake masa na cewa, ya yi watsi da shirye-shiryen tallafawa matasa a mazabarsa, inda ya ce galibin ayyukan da yake yi suna amfanar da matasa kai tsaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp