Wata Kotun kasar Canada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci
Published: 16th, August 2025 GMT
Wata kotun tarayya a kasar Canada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun.
Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan Yunin 2025, ta hana dan siyasar izinin shiga kasar bayan samun shi da gaza cika sharudan dokar shige da fice ta kasar.
A cewar alkalin, “Dabi’ar wasu ’yan siyasa ’yan PDP, wadanda wasu daga cikinsu ma kusoshi ne a jam’iyyar, da wadanda suka aikata laifukan siyasa ko aka yi da yawunsu, ta yi yawan da ba zai yiwu a ki alakanta shugabancin jam’iyyun da ita ba.”
Ana sa ran dai nan ba da jimawa ba gwamnatin Najeriya za ta fitar da sanarwa kan matsayinta a hukumance, kamar yadda wani babban jami’in gwamnati ya tabbatar mana, yana mai bayyana hukuncin a matsayin abin takaici.
Ita kuwa jam’iyyar PDP, ta bakin mamba a kwamitinta na zartarwa, Timothy Osadolor, ta ce kotun na da ’yancin fadin albarkacin bakinta, amma hukuncin nata ba yak an gaskiya.
“Amma babu wata hujja a cikin ra’ayin nasu da zai sa dukkan abin da suka fada a cikin hukuncin nasu ya zama gaskiya,” in ji Timothy.
Ya ce a maimakon ayyana jam’iyya gaba dayanta a matsayin kungiyar ta’addanci, kamata ya yi kotun ta fadi sunan masu alaka da ta’addancin kai tsaye, musamman a cikin jam’aiyyar APC.
Ya kuma bayyana hukuncin a matsayin na yanke kauna da salon shugabancin gwamnatin Najeriya a karkashin Shugaba Bola Tinubu, inda ya bukaci gwamnatin da kada ta dauki lamarin da wasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah Ta Ce Ba Zata Ajiye Makamanta Ba August 15, 2025 China Tace Bata Goyon Bayan A Sake Dorawa Iran Takunkuman MDD August 15, 2025 An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza August 15, 2025 India Ta Dage Kan Maida martani da hana Shigowar Kayakin Amurka Kasar August 15, 2025 Duniyarmu A Yau: Ranar 40 Ta Imam Hussain (a) A Bana August 15, 2025 Larijani: Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari August 15, 2025 HRW; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne August 15, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Wani Mummunan Hari Kan Gaza August 15, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Kansu August 15, 2025 Gwamnatin Mali Ta Bankado Wata Makarkashiyar Janyo Hargitsi A Kasar Tare Da Wargaza Shi August 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Za’a Fara tattaunawar Kasa Dangane Da Talauci da Kuma Rashin Adalci A Rabin Arziki A kasar
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu zata fara tattaunawar kasa dangane da talauci da kuma rashin adalci a rabon arziki a kasar.
Gwamnatin kasar ta ware kimani dalar Amurka miliyon 40$ don gudanar da tattaunawar. Inda ake saran dukkan mutanen Afrika ta kudu suna da damar bayyana ra’ayinsu dangane da wadannan matsaloli. Na talauci da rashin adalci a rabon arzikin kasar.
Ana fatan masana daga ciki da wajen kasar zasu gabatar da ra’ayinsu ta shafukan sadarwan da za’a samar a cikin taron.
A halin yanzu fiye da shekaru 30 kenan da fita karkashin mulkin wariya na launin fata tsiraru a kasar, amma har yanzun kasar tana fama da matsalolin talauci, rashin aikin yi aikata laifuka da sauransu.
Mutane da dama suna ganin ba abinda taron zai amfana. Amma shugaba Cyrel Ramamposa ya bayyana shirin taron tun watan yunin da ya gabata. Yana kuma ganin, a cikin ra’ayoyin da za’a tattara mai yuwa a sami mafita daga.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’ August 14, 2025 Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’ August 14, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara August 14, 2025 Hizbullahi Ta Yaba Wa Iran Kan Irin Gudumawarta Ga Lebanon Da Gwagwarmaya August 14, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Fatali Da Batun Kafa Gwamnatin Hadaka A Kasar Sudan August 14, 2025 Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon August 14, 2025 Masar ta yi Allawadai da furucin Netanyahu kan shirin kafa Isra’ila Babba August 14, 2025 Hamas ta aike da sakon jinjina ga al’ummar Yemen kan goyon bayan Gaza August 14, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129 August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci