Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe
Published: 24th, August 2025 GMT
Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe, ta sanar da korar tsohon ɗan takarar gwamnanta na shekarar 2015, Nafiu Bala, bisa zargin yi mata zagon ƙasa.
Shugaban ADC na jihar, Auwal Abba Barde, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a Gombe.
An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a SakkwatoA cewarsa, kwamitin ladabtarwa na unguwar Nasarawo ya binciki Bala, inda ya same shi da laifukan cin amanar jam’iyyar wanda hakan ya saɓa wa dokokinta.
Ya ce an gayyaci Bala domin ya kare kansa a gaban kwamitin amma ya ƙi bayyana.
Barde ya ƙara da cewa kwamitin zartarwa na jihar, ya tabbatar da wannan hukunci, kuma sun aike wa shugabancin jam’iyyar na ƙasa domin ɗaukar matakin na gaba.
Haka kuma ya bayyana cewa wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar a jihar an tsige su daga muƙamansu.
Duk da ɗaukar wannan mataki, Nafiu Bala, ya yi watsi da shi, ya bayyana cewa shi ne halastaccen shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa.
Ya ce an zaɓe shi ne bisa tsarin jam’iyyar bayan taron gangamin da aka gudanar.
Bala, ya ƙara da cewa tun daga shekarar 2022 aka kori Auwal Abba Barde daga jam’iyyar, don haka ba shi da ikon ladabtar da shi ko ɗaukar wani mataki a kansa.
Ya yi nuni da cewa kundin tsarin mulkin ADC da dokokin Najeriya sun buƙaci duk wanda aka kora daga jam’iyya ya sake yin rajista daga matakin unguwa kafin ya dawo cikinta.
A cewarsa, hakan ya sa bai ɗauki hukuncin da aka ɗauka a kansa da muhimmanci.
Ya kuma bayyana cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta amince da shi a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa.
Bala, ya jaddada cewa zai ci gaba da jagoranci domin tabbatar da gaskiya da haɗin kai a jam’iyyar, sannan ya gargaɗi waɗanda ke ƙoƙarin tada zaune-tsaye a ADC.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jam iyya a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Sarki Sanusi II ya koka kan yawan cin bashin Najeriya
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya koka bisa yawan bashin da Najeriya ke ciyowa da kuma yadda gwamnati ke facaka da kuɗaɗen.
Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya kuma bayyana cewa cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi shi ne mafi alheri, yana mai cewa da Gwamnatin ba ta cire tallafin mai ba, da Najeriya ta daɗe da tsiyacewa.
“Adawata a ɓangaren shan man ne, saboda muna ba da aikin yi ga matatun mai a Turai. Muna ba da aikin ga masu tace ɗanyen man,” in ji Sarki Sanusi.
Da yake jawabi a Taron Adabi na Duniya na Kano (KAPFEST) da aka gudanar a Kano ranar Asabar, masanin tattalin arzikin ya bayyana cewa ɗabi’ar yawan cin bashin Najeriya za ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin ƙasar na tsawon lokaci.
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Gidauniyar Misilli ta mayar da yara 150 makaranta a GombeMasanin tattalin arzikin ya bayyana damuwa musamman kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen da ta ciyo bashin.
Zuwa ƙarshen watan Maris, yawan bashin da ake bin Najeriya ya haura Naira tiriliyan 150.
A yayin taron wanda cibiyar Poetic Wednesdays Initiative (PWI), ta shirya, Sarki Sanusi II ya ce, ya ce, “Ina muke kai wannan tulin bashin da muke ciyowa a ƙasar nan?
“Zan yi farin cikin ganin an yi amfani da kuɗaɗen a fannin ilmantar da matasanmu, saboda su ne za su biya. Amma bai kamata mu yi ciyo bashi muna lafta wa tattalin arzikin ƙasa ba tare da zuba jari a fannin ilmantar da waɗanda su ne za su biya bashin ba.
“Nan da shekara 20 za mu faɗa a matsala a dalikin cin bashi. Dole a zuba jari a fannin inganta rayuwarsu domin samar da abubuwa.”
Ya bayyana cewa Najeriya ba ta yi sa’ar shugabanni nagari ba a tsawon lokaci, yana mai cewa yawancin shugabannin ƙasar ragwage ne masu yawan kawo uzuri.
Sarki Sanusi II ya bayyana kyakkyawan shugabanci a matsayin muhimmin abin da zai ceto Najeriya daga halin da take ciki, wanda ya kira na rashin sa’a.
Da yake sukar yanayin koma-bayan Najeriya alhali wasu ƙasashe sun yi gaba ta fannin kimiyya da fasaha da ci-gaban zamani, Sarki Sanusi II ya buƙaci matsala da su tashi domin karɓar ragamar shugabancin ƙasar, yana mai jaddada cewa hakan abu mai yiwuwa ne idan matasan suka jajirce.