Iran Ta Ti Watsi Da E3 Da Yadda Suke Tunkarar Shirin Nukliyar Kasar
Published: 6th, October 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei ya soki kasashen Faransa, Jamus da kuma Burtania da yadda suka yi dirar mikiya a kan shirin Nkliyar kasar Iran a cikin yan watannin da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Bghaei yana fadar haka a yau Litinin, a taron da yan jarida da ya saba gabatarwa a ko wace rana irin ta yau.
Baghaei ya zargi kasashen guda uku da amfani da tsarin SnapBack wanda ya zo cikin yarjeniyar JCPOA na shirin Nukliyar kasar Iran a inda baida dace ba. Ya kara da cewa kasashen sun yi amfani da Snapback kan kasar Iran ne don biyan bukatun Amurka na tursasawa gwamnatin JMI ta mika kai ga bukatun ta.
Banda haka ya ce sharuddan da kasashen uku suka shimfiyawa kasar don dakatar da amfani da snapback ma ba abin amincewa ne ga kasar Iran. Kuma ba wani mai hankali da zai amince da wadan nan sharuddan.
Daga karshe sai suka hada batun shirin nukliyar ta kasar Iran da tattaunawa da Amurka, wadanda basu hadu ba. Yace kofar diblomasiyya a bude take, amma kuma Iran ba zata saryar da hakkin na amfani da fasahar makamashin nukliya ba.
Daga karshe Baghaei ya bukaci ya bukaci kasashen duniya su yi watsi da takunkuman tattalin arzikin da aka sake dorawa Iran saboda Snapback.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aragchi Ya Bayyan Kokarin Ma’aikatarsa Na Bukatun Iran A Shirinta Na Makamashin Nukliya October 6, 2025 Lebanon: Shahidai Biyu Sanadiyyar Hare-Haren HKI A Lardin Nabatia A Kudancin Kasar October 6, 2025 HKI Ta Tabbatar Da Cewa An Kashe Sojojinta Fiye Da Dubu Daya A Yakin Gaza October 6, 2025 Kwamandan Dakarun IRGC Ya Ce: Suna Lura Da Duk Wani Motsin Abokan Gaba October 6, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Fitar Da Sanarwa Kan Batun Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 6, 2025 Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Jaddada Aniyarta Ta Gwagwarmayar Neman ‘Yancin Falasdinawa October 6, 2025 Kungiyar Human Righs Watch Ta Yi Tsokaci Kan Shirin Trump Na Batun Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 6, 2025 Hukumar Samar Da Abinci Ta MDD Ta Yi Gargadin Rage Tallafin Jin Kai A Kasar Somaliya October 6, 2025 Janar Pakpour: Duk wani shishigi a kan Iran zai fuskanci martani mai tsanani October 6, 2025 Iran na goyan bayan duk wani shiri da zai samar da ‘yancin Falasdinawa October 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau
Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.”
Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Dama kafin hakan Shugabannin tawagar masu sa ido kan zaben na Guinea Bissau na kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS, sun bayyana ” matukar damuwa game da sanarwar da sojoji suka yi na yin juyin mulki a kasar.”
A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, shugabannin sun ce gabanin sanarwar, kasar na cikin shirin sauraron sakamakon zaben da aka yi, wanda suka ce ya gudana lami lafiya.
A halin da ake ciki dai Sojojin da suka kwace mulki a Guinea-Bissau sun rantsar da Horta N’Tam a matsayin sabon shugaban riko na tsawon shekara daya.
Janar N’Tam ya sha rantsuwa ne yau alhamis a hedikwatar sojojin da ke babban birnin kasar Bissau, bayan da suka hambarar da shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo a jiya Laraba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bin diddigin lamarin da “matukar damuwa,” tana kira da a girmama bin doka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci