Sojojin Sudan Sun Zargi Rundunar “RSF” Da Kai Hari Akan Cibiyoyin Fararen Hula
Published: 5th, October 2025 GMT
A yau Lahadi sojojin na kasar Sudan su ka sanar da cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta kai hari akan cibiyoyin fararen hula a birinin al-Abyadh, wanda shi ne babbar cibiyar gundumar Jahar Kurdufan Ta Arewa.
Bayanin na sojojin kasar ya kara da cewa; rundunar ta RSF ya kai hari da jiragen sama marasa matuki na kunar bakin wake, akan wasu sansanoni na farar hula da su ka hada Asibiti da makarantu, da hakan keta dokokin kasa da kasa ne.
Sojojin sun kuma ce, wadannan hare-haren sun kuma yi barna akan gidajen fararen hula a cikin unguwannin gari, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka.
Sojojin na Sudan sun kuma bayyana cewa Abinda ya faru ba nasara ba ne ga rundunar kai daukin gaggawar, asara ce ta fuskar kyawawan halaye domin cutar da ‘yan kasa ne da ba su ji ba su gani ba.
A cikin watan Febrairu ne dai sojojin na Sudan su ka sanar da yin nasarar kawo karshen killace garin Abyadh da rundunar kai daukin gaggawar ta yi.
Garin na Abyadh yana cikin manyar biranen kasar ta Sudan, kuma anan ce babar shalkwatar rundunar ta 5 ta sojan kasa take.
Tun a tsakiyar watan Aprilu na 2023 ne dai yaki ya barke a tsakanin rundunar kai daukin gaggawa da sojojin Sudan wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan da sun kai 130,000 kamar yadda MDD ta bayyana. Da akwai wani adadin mutanen kasar da sun kai miliyan 15 da su ka yi hijira.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga- zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A London October 5, 2025 Dakarun Sojin kasar Yamen Sun Harba Makamai Masu Linzami A HKI October 5, 2025 Masar Ta Zargi Habasha Da karya Dokokin Kasa Da Kasa Kan Rikicin Madatsar Ruwan Kogin Nilu October 5, 2025 Shugaban Hamas Ya Bayyana A Fili Tun Bayan Harin Isra’ila A Kasar Qatar October 5, 2025 Dubban Mutane Ne Suka Yi Zanga -Zanga Nuna Adawa Da Isra’ila A Athens. October 5, 2025 The Guardian: Isra’ila ta azabtar da Greta Thunberg ‘yar kasar Sweden mai fafutuka October 5, 2025 Iran ta bukaci a haramtawa Isra’ila shiga harkokin wasanni na duniya October 5, 2025 Sheikh Qassem: Falasdinawa ne suke da hakkin yanke shawara kan makomar Gaza October 5, 2025 An yi gagarimar zanga zangar goyan bayan Falasdinu a Barcelona, Rome, da Paris October 5, 2025 Malawi : Mutharika ya yi rantsuwar kama aiki October 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: rundunar kai daukin
এছাড়াও পড়ুন:
ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau
Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.”
Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Dama kafin hakan Shugabannin tawagar masu sa ido kan zaben na Guinea Bissau na kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS, sun bayyana ” matukar damuwa game da sanarwar da sojoji suka yi na yin juyin mulki a kasar.”
A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, shugabannin sun ce gabanin sanarwar, kasar na cikin shirin sauraron sakamakon zaben da aka yi, wanda suka ce ya gudana lami lafiya.
A halin da ake ciki dai Sojojin da suka kwace mulki a Guinea-Bissau sun rantsar da Horta N’Tam a matsayin sabon shugaban riko na tsawon shekara daya.
Janar N’Tam ya sha rantsuwa ne yau alhamis a hedikwatar sojojin da ke babban birnin kasar Bissau, bayan da suka hambarar da shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo a jiya Laraba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bin diddigin lamarin da “matukar damuwa,” tana kira da a girmama bin doka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci