2025-07-23@22:33:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 174

«wakiltar shiyyar»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48. Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa. “Ina kira ga hukumomin Aljeriya da su yi watsi da wannan matakin, inda ya kara da cewa: “Idan har aka ci gaba da yanke shawarar korar wakilanmu, ba mu da wani zabi illa mu mayar da martani cikin gaggawa.” Shekaru da dama, alakar diflomatoyyar da ke tsakanin Aljeriya da Faransa ta yi tsami. A farkon watan Afrilu, ministan harkokin wajen Faransa ya je kasar Aljeriya,...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa:  Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage. Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.
    Rahotanni da suke fitowa daga Nigeria sun ce, a kalla mutane 7 su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar fashewar wasu abubuwa masu karfi akan hanyar Damboa-Zuwa Maiduguri. Rahotannin sun ce abubuwan su fashe ne dai a lokacin da wasu ayarin motoci da suke wucewa ta hanyar tare da rakiyar sojoji a jiya Asabar da hakan ya haddasa asarar rayuka da kuma jikka. Hanyar Damboa zuwa Maiduguri tana zuwa kananan hukumomi da dama a kudancin Jahar ta Borno, a lokaci daya kuma yanki ne da ya yi kaurin suna a matsayin matsugunin ‘yan Bokoharam. An dade da rufe hanyar saboda matsalar tsaro, amma gwamnatin Babagana zulum ta sake bude ta, da kuma dawo da...
    Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce APC ba ta girgiza ba, kuma ta mayar da hankali ne kan karfafa madafunta. A cikin wani bidiyo, a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan bayan ya jagoranci masu ruwa da tsaki na APC zuwa ganawa da Buhari a gidansa, Ganduje ya ce sun ziyarci Buhari ne don sanar da shi irin nasarorin ci da jam’iyyar ta samu tun bayan barinsa mulki da kuma tabbatar da kudirinsu na tabbatar da ci-gaban ayyukansa. “Ba mu ba damu ko kadan. Mun zo...
    Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP. Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya bayyana cewa rikicin cikin gida na jam’iyyar kotun ba ta da hurumin sauyaran karar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jam’iyyar Labour (LP) ta yi barazanar dakatar da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da ɗan takarar shugaban kasa na 2023, Peter Obi, idan ba su daina abin da aka kira “aikin da ba a goyon baya” ba. Wannan barazanar ta fito ne bayan taron kwamitin zartarwa na Jam’iyyar (NEC) da aka gudanar a Abuja, inda aka zargi Otti da shirya taron ba bisa ƙa’ida ba da kuma shirin raba jam’iyyar gida biyu. LP ta kuma nuna damuwa kan shirin Otti na kiran wani taron NEC a ranar 9 ga Afrilu, 2025, wanda aka ce zai kawo cikas ga haɗin kai na jam’iyyar. Haka kuma, jam’iyyar ta gargaɗi Peter Obi game da matakan da za su iya kawo rushewar jam’iyyar, tana...
    A rana ta 21 da Isra’ila ta sake komawa yaki da al’ummar Falasdinu a Gaza, jiragen yakinta sun kai hare-hare munanan a yankin Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama, da kuma jikkata wani adadin Falaasidinawa  mai yawa. Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai kungiyar  ta mayar da martini ta hanyar harba makamai masu linzami akan matsugunin ‘yan share wuri zauna a Asqalan da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar ‘yan sahayoniya. A gafe daya ana gudanar da yajin aiki na gama gari a yankin yammacin kogin Jordan saboda nuna kin amincewa da yadda ‘yan sahayoniya suke yi wa al’ummar Falasdinu kisan kiyashi. Kungiyoyin fararen hula ne su kirayi wannan yajin aikin, wanda ya game yankin na...
    Tun daga ranar 1 ga watan Afrilu, dakarun rundunar sojojin ’yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar ta kaddamar da atisayen hadin gwiwar rukunoni masu kunshe da sojojin kasa, da na ruwa, da na sama da dai sauransu a kewayen tsibirin Taiwan. Atisayen da ya kasance wani salo na jan kunne mai karfi ga mahukuntan gwamnatin Lai Ching-te dake rajin “’yancin kan Taiwan”, kana mataki mai karfi da ya wajaba na kare ikon mulkin kai da cikakkun yankunan kasar Sin. Kamar yadda aka sani, Taiwan wani sashe ne na kasar Sin, wanda ba ta taba zama kasa ba, kuma ba zai taba zama ba a nan gaba. Sunan yankin Taiwa a MDD shi ne “Lardin Taiwan...
    “Muna shirye-shiryen bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa.   “Ina kuma yabawa mutanen jihar Kano da daukacin arewa saboda rashin daukar doka a hannunsu da kai harin ramuwar gayya,” inji shi.   Ya yi addu’ar Allah ya jikan mafarautan da suka mutu.   Gwamnan Edo ya kara, da cewa, tuni aka fara cafke wadande ake zargi da aikata wannan aika-aika.   “An riga an kama kimanin mutane 14 da ake zargi, za mu ci gaba da bin diddigin lamarin har sai an gurfanar da su a gaban kotu an yi wadanda aka kashe adalci”. In ji Okpebolo Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025. A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a cikin jahoji 33 na fadin kasar, kuma bincike da aka yi akan wadanda ake tsammanin ta kama, ya tabbatar da cewa an sami mutane 645 da su ka kamu da ita. Ita dai wannan cutar mai yaduwa a Nigeria, ana kamuwa da ita ne ta hanyar cudanya a tsakanin mutane ko kuma taba kayan gida da su ka gurbana daga bahaya ko fitsari na mutane...
    A Faransa, an haramta wa Marie Le Pen yin takara har na tsawon shekaru biyar kuma hakan na nufin ba za ta yi takarar shugabancin kasar ba a shekarar 2027. An dai samu yar siyasar ne da laifin almubazzaranci da kudaden jama’a wajen daukar nauyin jam’iyyarta ta National Rally mai tsaurin ra’ayi.   An tuhumi Le Pen tare da wasu manyan yan jam’iyyar tata guda 20 da daukar masu taimaka musu aiki wadanda suka yi wa jam’iyyarta aiki maimakon Majalisar Turai wadda ita ce ke biyan ma’aikatan albashi.   Ms Le Pen, mai shekaru 56, ba za ta iya shiga zaben shugaban kasa mai zuwa da aka shirya gudanarwa a shekara ta 2027 ba, inda a yanzu ake ganin ita...
    A jiya Asabar dubun dubatar ‘yan hamayyar siyasa su ka yi gangami a birnin Stanbul bayan da jam’iyyar “National Party” ta gayyace su, domin ci gaba da yin tir da kamun da aka yi wa Akram Imam Uglu wanda shi ne magajin garin na Stanbul. Shugagan jam’iyyar “Turkish National Party’ ta adawa, Uzgur Ozil ya bayyana cewa adadin wadanda su ka halarci gangamin sun kai miliyan 2.2. Daga cikin mahalarta gangamin da akwai mata da mahaifan Akram Ima wadanda su ka rika bayar da taken cewa za a ci gaba da yin gwgawarmaya ako’ina.” Tun da asubahin jiya Asabar ne dai mutane su ka fara yin tururuwa a cikin birnin na birnin Sitanbul suna dauke da tutocin turkiya da kuma...
    Rikicikin ya turnuke jam’iyyar SDP a yayin da aka samu shugabanni bangare biyu a Jihar Kogi, rikicin ya kunno kai ne bayan da wani bangare ya kaddamar da kwamitin gudanarwa a Lakwaja. Taron da aka gudanar a sakateriyar jam’iyyar na jihar, an zabi tsohon shugaban sashi na APC, Hon. Ahmed Attah a matsayin sabon shubagaba, tare da Alhaji Idris Sofada a matsayin sabon sakatare na jam’iyyar a jihar. Wakilai 3,890 ne daga kananan hukumomi 21 na jihar suka zabi shugabanni 21 na jam’iyyar. Sannan kuma jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) sun kasance a wannan wuri lokacin zaben. A jawabinsa na farko, Attag ya yi alkawarin zai yi gaskiya da adalci tare da daga martabar jam’iyyar SDP...
    A cikin shekaru da ya yi a masana’antar, Karkuzu ya nuna ƙwarewa wajen kawo canji da kuma nishaɗantar da al’umma. A madadin gwamnatin Kano da al’ummar jihar, gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin, ‘yan Kannywood, da masana’antar. Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙan jarumin, Ya kuma Aljanna Firdausi ta zama makomarsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai Bai Wa Gwamnan Sakkwato Shawara kan Harkokin Karkara, Malami Muhammad Galadanchi (Bajare), ya bai wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar, kyautar Naira miliyan 22 domin gudanar da shagalin Sallah Karamar. Yayin bayar da kyautar a ranar Alhamis, Bajare ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiyarsa ga jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, da Gwamna Ahmad Aliyu, bisa damar da suka ba shi don ba da gudunmawarsa ga ci gaban jihar. An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu “Wannan tallafi saƙon godiya ne daga shugabanninmu zuwa gare ku. Idan ba su ba mu dama ba, ba za mu iya wannan ba. “Kuma muna shirye mu ƙara...
    Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto cewa; An kai harinn ne wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar wasu sojoji da dama a wasu sansanoni biyu dake Jihar Borno. Mayakan kungiyoyin Boko Haram da Daesh suna kai wa fararen hula hare-hare a kasashen yammacin Afirka daga ciki har da Najeriya, inda suke kashe fararen hula da jami’an tsaro.  Majiyar ta kamfanin dillancin labarun “Reuters’ ta ce, kungiyoyin na “Da’esh’ da Boko Haram sun kai harin ne a yankin Wajiroko dake jihar borno, tare da cinna wuta a wurin da hakan ya yi sanadiyyar konewar kayan soja. Wani soja ya bayyana cewa, a kalla 4 daga cikin sojoji ne su ka wanta dama sanadiyyar wannan harin, tare da jikkata wasu...
    Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu wanda a halin yanzu yake a gidan kurkuku. Imam Uglu dan shekara 53 shi ne muhimmin dan takarar shugaban kasa a tsakanin ‘yan hamayya da ake hasashen cewa  zai iya bugawa da shugaba Rajab Tayyib Urdugan a zabe mai zuwa. ‘Yan jam’iyyar ta adawa sun kada kuri’ar tsayar da Imam Ugulu a matsayin dan takararsu a zabe mai zuwa, inda ya sami kuri’u miliyan 1.6 a tsakanin miliyan 1.7. Shugaban jam’iyyar ta “National Party” Uzgur Uzil wanda ya sanar da hakan, ya kuma bayyana cewa an yi zabe na gwaji da miliyoyin mutane su ka...
    Ita maganar bada damar tsayawa takara ba tare da zaben fidda gwani ba an dauki matakin ne saboda yadda aka ga ‘yan adawa ko jam’iyyun adawa suke kokarin tayar da babbar kura mai hayaki,wa ita jam’iyyar mai rike da kambun mulki a 2027 domin “Ba a san maci Tuwo ba sai Miya ta kare”. Ana dai ganin tarurrukan da aka yi na mambobin APC,wadanda suke ganin ba,a kyauta masu ba da kuma Shugabannin adawa suna yin wani shiri wanda zai iya sa wasu daga cikinsu su yi jerin Tururuwa na komawa jam’iyyar SDP,kamar dai yadda tsohon Gwamnan Jihar Kaduna,Malam Nasiru El Rufa’i ya fara kasancewa na farko wanda ake ganin akwai wadanda za su iya goyo masa baya. Idan dai...
    Lamido ya kasance tsohon sakataren jam’iyyar SDP, ya sake jaddada alkawarinsa ga PDP, yana mai cewa bai ga dalilin barinsa jam’iyyar ba. Lokacin da na kasance sakataren jam’iyyar SDP, ina El-Rufai yake? Ina Shehu Gabam, shugaban jam’iyyar na kasa na yanzu? Duk da kalubalen da PDP ke fuskanta, a nan ne aka haife shi a siyasa. Idan yana ikirarin cewa PDP ta mutu, to ya manta da asalinsa.” Yana jaddada cewa El-Rufa’i ya samu nasara ne a siyasa ciki har da mukamin minista da ya rike sakamakon jam’iyyar PDP ne. A cewarsa, duk abin da ya mallaka a yanzu, ya samu ne ta sanadiyyar jam’iyyar PDP ne. Lamido ya ce ya samu damar barin PDP ciki har da lokacin da...
    Majiyar ‘yan aware ta kasar Mali ta sanar da cewa wani hari da sojojin gwamnati su ka kai a arewacin kasar ya yi sanadiyyar kashe mutane 18 a arewacin kasar Yemen, sai dai sojojin gwamnatin ta ce, ‘yan aware ta kai wa hari. Kungiyar Azbinawa ‘yan aware ta ce sojojin gwamnatin kasar sun kai hari ne a garin Lerneb mai nisan kilo mita 50 daga birnin Timbuktu, a ranar Litinin da ta gabata kuma bayan mutane 18 da su ka kwanta dama, wasu 7 sun jikkata. Kungiyar ta Azbinawa ta bayyana abinda ya faru da cewa; “Dabbanci” ne irin na zamanin jahiliyya. Sai dai sojojin gwamnatin kasar ta Mali sun wallafa a shafinsu na X cewa; sun kai harin ne...
    Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙwace wani fili mallakar sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja. Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen kula da filaye na Abuja, Chijioke Nwankwoeze. Nwankwoeze ya ce an yanke hukuncin ƙwace filin ne sakamakon gazawar babbar jam’iyyar adawar na biyan kudin gini na shekara shekara. Wasiƙar ta ce PDP ta gaza biyan kuɗin tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2006 zuwa 1 ga watan Janairun 2025, duk da sanarwar da hukumar gudanarwar babban birni (FCTA) ta wallafa a jaridu da dama tun daga shekarar 2023 kan buƙatar biyan kuɗaɗen. Aminiya ta ruwaito cewa filin na Jamiyyar PDP na daga cikin filaye 4,700 da Ministan ya ƙwace a...
     Rahotanni Daga Gaza sun ce adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da safiyar yau sun haura 200 Wata sanarwar da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta fitar a yau Talata ta ce; Adadin shahidan sanadiyyar sabbin hare-haren HKI sun kai  244.  Sai dai har yanzu ba a kammala tantance adadin adadin shahidan ba, da kuma wadanda su ka jikkata. Gabanin wannan harin na safiyar yau, an bayyana cewa fiye da Falasdinawa 150 ne su ka yi shahada tun bayan tsagaita wutar yaki. Babban jami’i mai kula da harkokin watsa labaru a yankin Gaza Isma’ila Sawabita ya sanar da cewa; Tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 19 ga watan Janairu zuwa yanzu adadin Falasdinawa da su ka yi shahada...
    Ya ce fim ɗin tarihin zai nuna nasarori, ƙalubale, da darussan da aka koya a wannan tafiya.   Ya ce: “Na yi farin cikin ganin ƙoƙarin da IPAC da shugabannin ta suke yi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya, musamman ta hanyar fim ɗin wanda zai zama wata muhimmiyar shaida ta tarihi, domin girmama jaruman siyasar ƙasar mu da kuma nuna jajircewar Nijeriya a harkar dimokiraɗiyya. A kan haka, Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, za ta goyi bayan shirya wannan fim na musamman.”   Ya jinjina wa IPAC kan jajircewar ta wajen cigaban dimokiraɗiyya tare da jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyun siyasa bayan zaɓe domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da cigaba.   “Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed...
    Wannan lamari ci gaban da haifar da zazzafar martani daga jam’iyyun adawa da manazarta siyasa wadanda suka yi zargin cewa hakan ya saba wa dokar zabe da kundin tsarin mulkin 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima. Masana harkokin shari’a da masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa irin wannan kamfen da ba a kai ba, yana kawo cikas ga dimokuradiyya, da bin doka da oda da kuma tsarin zabe. A watan da ya gabata ne jam’iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa, Tinubu da Gwamna Nasir Idris a Jihar Kebbi as zaben 2027. Taron wanda aka gudanar a babban filin wasa na garin Birnin Kebbi, ya samu halartar ministan kasafi da tsare-tsare na tattalin arziki, Sanata...
    Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya yi ganawar sirri da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. Taron ya gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, sai dai ba a bayyana manufar taron ba. Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja Obi ya isa Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tarbe shi. Rahotanni sun nuna cewa Obi da Gwamna Mohammed sun tattauna wasu batutuwa da suka shafi babban zaɓen 2027 da kuma makomar siyasarsu. Wannan ganawa ta wakana ne a daidai lokacin da ’yan siyasa...
    Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, na ganawar sirri da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi. Taron na gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, amma ba a bayyana manufarsa ba tukuna. Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja Obi ya isa Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tarbe shi. Rahotanni sun nuna cewa Obi da Gwamna Mohammed za su yi magana da ’yan jarida bayan kammala ganawar tasu. Wannan ganawa na faruwa ne a daidai lokacin da ’yan siyasa ke shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027....
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya tabbatar da cewa ya bar jam’iyyar APC ne da sanin Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari. El-Rufa’i ya bayyana komawarsa jam’iyyar SDP a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook. ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja Ya ce bai gamsu da yadda ake tafiyar da APC ba cikin shekaru biyu da suka gabata. Yayin da yake zantawa da BBC Hausa, El-Rufa’i ya bayyana cewa ya sanar da Buhari kafin ya fice daga APC. “Na faɗa masa game da shawarar da na yanke a ranar Juma’a. Ina yawan tuntuɓarsa kan harkokin siyasata,” in ji shi. El-Rufa’i ya kuma tuna cewa...
    Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da rabon shinkafa da sauran kayayyaki ga gidaje sama da 30,000 dake fadin kananan hukumomi 23 na jihar.   Da yake kaddamar da rabon a Sokoto, Sanata Tambuwal ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya sake ganin watan Azumin Ramadan tare da tabbatar da ganin an gudanar da Ramadan cikin kwanciyar hankali.   Ya jaddada mahimmancin tunani, karamci da addu’o’in ci gaba da lafiya da wadata.   Tambuwal wanda shi ne Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu a jam’iyyar PDP ya ce wannan shiri na kara jaddada kudurin jam’iyyar na hadin kai, tausayi da goyon bayan al’umma a cikin wannan wata mai alfarma.   Ya yaba da jajircewar...
    Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Daniel Bwala, ya ce akwai yiwuwar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koma jam’iyyar APC mai mulki. Bwala ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC, inda ya ce babban aminin Obi, Valentine Ozigbo, ya koma jam’iyyar APC domin yin takarar gwamna. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? ’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina “Kun san muna rage ƙarfin jam’iyyar LP kuwa?” in ji Bwala. “Valentine Ozigbo ya shigo jam’iyyarmu, Balami ma haka, Peter Obi ma zai zo....
    Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da tallafin kayan abinci ga magidanta dubu 30 a fadin jihar. A yayin da yake kaddamar da tallafin tare da bayar da jari ga masu kananan sana’oi a gidansa a ranar Litinin, ya bayyana cewar tallafin wani mataki ne na saukakawa mabukata halin kunci a watan Ramadan mai girma. Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Masanin Aikin Jarida, Kabir Ɗangogo Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa, ya bukaci wadanda za su rarraba kayan abincin da su gudanar da gaskiya da adalci wajen tabbatar da tallafin ya kai hannun wadanda suka cancanta a mazabu 244...
    Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta sake ɗage babban taronta na ƙasa (NEC), zuwa ranar 15 ga watan Mayu, 2025. A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, wanda babban sakatarenta, Sunday Ude-Okoye, ya bayyana hakan. Iyalan Abacha sun gargaɗi Babangida kan ɓata sunan mahaifinsu An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba Tun asali, an tsara gudanar da taron ne a ranar 13 ga watan Maris 2025, amma aka ɗage shi saboda wasu zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a jihohi daban-daban. Tun a shekarar da ta gabata ne PDP ta tsara yin wannan babban taro karo na 98, amma ana ci gaba da ɗagewa. Rahotanni na nuni da cewa matsalolin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta, kamar rikicin...
    Rahotanni sun bayyana cewa, ya kammala yunkurin komawa jam’iyyar SDP.   Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ofishin yada labarai na Atiku ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya na nan dan jam’iyyar PDP na gaskiya.   Yayin da yake bayyana rahotannin a matsayin “karya”, ofishin yada labaran ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da rahoton sauya jam’iyyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi Allah-wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan cin zarafinta. A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta ce dakatarwar wata hanya ce ta ɓoye zargin da ake yi wa Akpabio. Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu “Wannan mataki ba wai kawai ya hana Sanata Akpoti-Uduaghan damar kare kanta ba ne, har ma yana nuna cewa majalisar na kare rashin ɗa’a,” in ji PDP. Jam’iyyar ta kuma ce dakatarwar ba adalci ba ce ga al’ummar yankin Kogi ta Tsakiya, waɗanda yanzu suka rasa wakilci a majalisa....
    Jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi Allah-wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan cin zarafinta. A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta ce dakatarwar wata hanya ce ta ɓoye zargin da ake yi wa Akpabio. Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu “Wannan mataki ba wai kawai ya hana Sanata Akpoti-Uduaghan damar kare kanta ba ne, har ma yana nuna cewa majalisar na kare rashin ɗa’a,” in ji PDP. Jam’iyyar ta kuma ce dakatarwar ba adalci ba ce ga al’ummar yankin Kogi ta Tsakiya, waɗanda yanzu suka rasa wakilci a majalisa....
    Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabannin Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatissunnah, musamman Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, da duk al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Daga ƙarshe, ya yi addu’a ga Allah da ya gafarta wa marigayin, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Har ila yau Wang Yi, ya ce Sin da Amurka za su kasance a doron duniya na tsawon lokaci, don haka dole ne su nemi yadda za su yi zaman jituwa cikin lumana. A cewar Wang Yi, mutunta juna muhimmiyar ka’ida ce ta hulda kasashen biyu. Da yake tsokaci game da matakin Amurka na sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Sin bisa fakewa da batun Fentanyl, Wang Yi ya ce, bai kamata Amurka ta saka alheri da sharri, ko kuma kakaba haraji ba. Yana cewa, tu’ammali da maganin Fentanyl a Amurka, matsala ce da ya kamata kasar ta warware da kanta. Ya kara da cewa, ba zai yiwu a yi tunanin za a danne kasar Sin, sannan kuma a ci...
    Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadin ta ga gwamna Inuwa Yahaya kan rabon kayan abinci da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar a matsayin tallafin azumin watan Ramadan.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar Abdulkadir Ahmad ya fitar a Gombe.   Jam’iyyar ta caccaki gwamnatin jihar kan rashin amincewa da rawar da gwamnatin tarayya ta taka, wanda hakan ya sanya ake yaudarar jama’a wajen ganin cewa tallafin na jiha ne kawai.   Jam’iyyar adawa ta ba da shawarar cewa yin shiru ya sa ayar tambaya game da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kayayyakin agaji.   Ta kuma yi zargin cewa sukar da Gwamnan ya yi a...
    Kazalika, wannan kimiyya abar maraba ce ga masu kiwon Shanu, musamman ga wadanda ke bukatar fadada samar da ingantacciya kuma wadatacciyar Madara a guraren kiwonsu. Kirkirar kimiyyar, ta zo kan gaba duba da kokarin niyyar da Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi ta sanya a gaba, ta zamanantar da kiwon dabbobi da kuma habaka samar da wadatacciyar Madarar Shanu a kasar nan. Ana dai ci gaba da bukatar ingantacciyar Madarar Shanun a fadin wannan kasa, sai dai ana ci gaba da fuskantar kalubalen lafiyayyun Shanun, musamman a kasa irin Nijeriya. Sabuwar kimiyyar za ta bayar da damar saurin sanya ido kan yadda kiwon lafiyarsu ke tafiya, saurin gano ko sun harbu da wata kwayar cuta da kuma kula da lokacin nakudanarsu. “Wannan...
    Jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Amurka zasu sake haduwa a gobe Alhamis 27 ga watan Fabarayru a birnin Istambul na kasar Turkiyya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yana fadar haka a kasar Qatar, ya kuma kara da cewa a haduwarsu na gobe kasashen biyu zasu maida hankali ne wajen sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a kasashensu. Ministan ya kara da cewa, dangantaka tsakanin Rasha da Amurka bai taba yin kyau ba tun lokacin tarayyar Soviet, amma ta dan kyautata a lokacin shugabancin Trump na farko.  Sannan bayan sake dawowan Trump da alamun dangantakar zata yi kyau. A gobe Alhamis dai bangarorin biyu zasu dubu abubuwan da suke hana...
    Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci samar da sabon ginin sakatariyar jam’iyyar na kasa, ya kuma bayyana irin kokarin da jam’iyyar ke yi na kula da mambobinta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jam’iyyar APC mai mulki, ta gudanar da babban taronta na ƙasa a Abuja, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar daban-daban. Duk da kasancewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a waje taron, wasu manyan shugabannin jam’iyyar ba su halarci taron ba. Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Daga cikin waɗanda ba su halarci taron ba akwai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi. Dalilin Rashin Halartar Buhari Dangane da dalilin da ya sa Buhari bai samu halartar taron ba, tsohon mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa...
    A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ta shirya taron kwamitin zartaswa na kasa wanda ake sa ran za ta yi ranar Laraba, jam’iyyar ta musanta rade-radin da ake yi na cewa shugaba Bola Tinubu na iya neman shugaban jam’iyyar, Dakta Abdullahi Ganduje, ya sauka daga mukaminsa. Sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ya karyata jita-jitar a wata hira da aka yi da shi, inda ya jaddada cewa, jam’iyyar ta saba gudanar da irin wannan taron, ba wai sai don shirin zabe ba. Amurka Za Ta Illata Kanta Bisa Tsara Matakan Kayyade Samar Wa Sin Sassan Na’urorin Laturoni Na Semiconductor Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa A halin da ake ciki, tsohon gwamnan jihar...
    Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da ƙara a kotu tana ƙalubalantar shugaban majalisar, Godswil Akpabio, kan zargin ɓata mata suna. Natasha ta shigar da ƙarar ne gaban Babbar Kotun Tarayya a ranar Talata, tana mai ƙarar Akpabio da babban mai taimaka masa Mfon Patrick. Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu Ta nemi Kotun Tarayyar da ta umarci waɗanda ake karar su biya ta diyyar naira biliyan 100 kan zargin ɓata mata suna, sannan a biya ta naira miliyan 300 a matsayin kuɗin shigar da ƙara. Akpoti, wadda lauyanta Victor Giwa ya shigar da ƙarar a madadinta, ya yi ƙorafi kan...
    Ministan ya yi zargin cewa, furucin Shugaban na daya daga cikin dalilan da suka sa Allah ya karbe mulki daga jam’iyyar duk da nasarar da ta samu a zaben gwamna na 2023.   Amma da yake mayar da martani, Abbas ya yi zargin cewa Ata ya yi wa jam’iyyar zagon kasa a zaben 2023, kuma sun bayyana haka ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.   Abdullahi Abbas ya ce, “A gare mu ‘yan APC Yusuf Ata ba dan jam’iyyar APC ba ne. Ba mu ma san dalilin da ya sa aka nada shi minista ba. Duk fadin jihar Kano a karamar hukumarsa ne muka zo na uku a zaben 2023.   “Ba mu san cewa an nada shi minista ba. Mun...
      Barazanar Ata Kan Ficewa Daga APC A cikin bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, Minista Yusuf Ata ya yi magana da magoya bayansa, yana mai cewa idan ba a sauya shugabancin APC a Kano ba, to zai fice daga jam’iyyar. “Muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi,” in ji Ata. Ya ƙara da cewa, “Idan suka dawo da shi, za mu fice, kuma na rantse da Allah jam’iyyar za ta sake faɗuwa a zabe.” Wannan rikici na ƙara nuna rabuwar kai a cikin APC a Kano, wanda ka iya shafar ƙarfi da tasirin jam’iyyar a jihar nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Pars Today – Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa za a gudanar da taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran). Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Reza Aref, a wata ganawa da ya yi da shugabannin jami’an diflomasiyyar Afirka a birnin Tehran ya bayyana cewa, raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya da nahiyar Afirka, na daya daga cikin muhimman batutuwan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanya a gaba. Aref ya kara da cewa, shirya taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Jam’iyyar adawa ta NNPP ta rasa ɗaya daga cikin mambobinta a Majalisar Wakilai zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram ta Jihar Jigawa, Yusuf Shitu Galambi. Shi ne ɗan jam’iyyar NNPP na farko da ya sauya sheƙa ya koma APC. Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Idan dai za a iya tunawa, ’yan jam’iyyar adawa na PDP da LP da dama sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. Ɗan Majalisa Galambi ya bayyana cewa, ya bar jam’iyyar NNPP ne saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar wanda ya haifar da wasu ƙararraki da suka shafi ayyukan jam’iyyar. Ya kuma ƙara da cewa, Jam’iyyar NNPP...
    Wani sabon rikici ya sake kunno kai a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu a Jihar Zamfara. Rigimar wadda ta kunno tsakanin APC da PDP ta samo asali ne tun bayan da wasu matasa suka yi yunƙurin hana wani taro na ɗan Majalisar Wakilai da za a gudanar a garin Maru. Mutum 10 sun rasu, an lalata dukiyar N11bn yayin zanga-zangar yunwa a Kano — Rahoto Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno Hakan ya sa Gwamnatin Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki wani matakin da take ganin zai kawo lafawar lamarin. Sai dai kuma matakin da gwamnatin ta ɗauka bai yi wa jam’iyyar APC daɗi ba, inda ta nuna rashin gamsuwa tare da zargin ba a...
    Mujallar “Qiushi” da aka buga a yau Lahadi, ta gabatar da muhimmin sharhi na sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping mai taken “Inganta tsarin daukar kwararan matakai wajen tafiyar da jam’iyya a dukkan fannoni”. A cikin sharhin an nuna cewa, har yanzu ana fuskantar matsanancin yanayi da sarkakiya wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta dade tana fuskantar wannan jarrabawar. Saboda haka, dole ne dukkan mambobin jam’iyyar a ko da yaushe su sa lura da nuna karfin zuci, da daukar kwararan matakai wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar na dukkan fannoni, ta yadda za a iya raya jam’iyyar yadda ake bukata. Ban da haka, ya kamata...
    Gwamnatin Jihar Zamfara ta haramta gudanar da tarukan siyasa a faɗin jihar har sai abin da hali ya yi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan mataki ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda jam’iyyar adawa ta APC ta koka cewa an kai wasu daga cikin jami’anta hari. Janar Musa ya fallasa ƙasashen da ke ɗaukar nauyin Boko Haram Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Dalilin Haramta Tarukan Siyasa Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’amuran Jama’a, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa an ɗauki mataki ne, sakamakon wata hatsaniya da ta auku a Ƙaramar Hukumar Maru. Ya ce: “Daga yanzu, an haramta duk...
    Gwamnatin Jihar Zamfara ta haramta gudanar da tarukan siyasa a faɗin jihar har sai abin da hali ya yi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan mataki ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda jam’iyyar adawa ta APC ta koka cewa an kai wasu daga cikin jami’anta hari. Janar Musa ya fallasa ƙasashen da ke ɗaukar nauyin Boko Haram Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Dalilin Haramta Tarukan Siyasa Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’amuran Jama’a, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa an ɗauki mataki ne, sakamakon wata hatsaniya da ta auku a Ƙaramar Hukumar Maru. Ya ce: “Daga yanzu, an haramta duk...
    Tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa guguwar sauyin sheƙa da ta fara kaɗawa a tsakanin jam’iyyun siyasa a Arewa maso Yammacin ƙasar na da alaƙa na son zuciyar ’yan siyasar yankin. Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a taron ƙusoshin jam’iyyar PDP da ya gudana yau Asabar a Jihar Kaduna. Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto Makwabta sun kai karar ma’aurata saboda carar zakaransu Tambuwal ya zargi ’yan siyasar da ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar da son zuciya waɗanda ya ce ba sa kishin al’umma. Tsohon gwamnan ya ce akwai dalilai da ’yan siyasa ke sauya sheƙa daga wannan jam’iyyar zuwa...
    Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ita ma ta shiga cikin rikici, inda ake zargin Kwankwaso ne ke jagorantar daya daga cikin bangarorin jam’iyyar. A makon da ya gabata ne wani bangare na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin wanda ya assasa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam ya gudanar da babban taro a Legas, inda aka zabi sabbin mambobin kwamitin zartarwa na kasa. Kwankwaso ya tabbatar da ganawarsa da Aregbesola a wani sako da ya fitar. Ya ce, “A yammacin yau na yi farin cikin ziyartar tsohon gwamnan Jihar Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a gidansa da ke Legas. Taron ya ba mu damar tattaunawa a kan harkokin siyasar kasar nan da gudanar...
    Alhaji Ahmad Haruna Zago da aka fi sani da Ɗan zago, gogaggen ɗan siyasa ne da ya fara siyasa tun a Jamhuriya ta biyu. Bayan dawowar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999, ya shiga Jam’iyyar APP, inda ya kasance na gaba-gaba a tafiyar siyasar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki ɗaya. Yana daga cikin waɗanda suka jawo Muhammadu Buhari shiga cikin harkokin siyasa. 2003. Gabanin zaɓen 2003, Alhaji Ahmadu Haruna zago ya taka rawa a tunja-tunjar da ta biyo bayan zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APP, da ta kai ga karɓe takarar gwamna daga hannun tsohon shugaban jam’iyyar, Ibrahim Al’amin Little, aka bai wa Malam Ibrahim Shekarau. 2007 Sai dai tun ba a je ko’ina ba,...
    Fitaccen ɗan siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda, ya ce ya yi nadamar mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2023. Yayin da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, Kwamanda ya ce Shugaba Tinubu ya watsar da waɗanda suka sha wuya a kansa, duba da halin da ƙasa ke ciki a yanzu. Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta Ya bayyana cewa, a duk tsawon rayuwarsa, bai taɓa yin nadamar wani abu kamar yadda ya yi nadamar mara wa Tinubu baya ba. “Da ciwo, amma dole a faɗi gaskiya. Ni cikakken ɗan jam’iyyar APC ne,...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Besse/Maiyama daga Jihar Kebbi, Salisu Garba Koko, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Koko, ya sanar da wannan mataki ne cikin wata wasiƙa da ya aike kuma aka karanta a zauren majalisa. N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum Ya bayyana rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya tilasta masa barin ta. Wannan sauya sheƙa ya biyo bayan ficewar wani ɗan majalisar Kaduna, Amos Gwamna Magaji, wanda shi ma ya fice daga PDP sabida rikice-rikice. Sai dai shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya musanta zargin jam’iyyar na fama da rikice-rikice....
    An tafi da shi tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ɗan uwansa da matarsa da ɗansa a yayin harin.   An tattaro cewa, jigon na APC ya kai ziyara gidan ɗan uwansa ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin.   Sai dai, an tsinci gawar matar dan uwansa ​​mai suna, Madam Esther, a kusa da unguwar Ijah-Gbagyi da ke karamar hukumar Tafa a jihar Neja da safe.
    Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Zangon Kataf/Jaba daga Jihar Kaduna, Honorabul Amos Gwamna Magaji ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki. A safiyar Talata Shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar da sauya shekar, yana mai bayyana rikicin cikin gidan PDP a mastayin dalilin ficewar dan majalisar daga jam’iyyar. Dan majalisar ya  bayyana cewa kafin ya sauya shekar sai da ya tuntubi al’ummar mazabarsa inda suka ba shi hadin kai da kuma amincewa.
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Namibia, Nangolo Mbumba, bisa rasuwar shugaban kasar na farko, Sam Nujoma. A madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, shugaba Xi Jinping ya bayyana jimami tare da yin ta’aziyya ga iyalan Nujoma da ma gwamnati da al’ummar kasar Nambia. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas. Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya. Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke kira ga haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027. A watan Oktoban 2024, jam’iyyar APC a Jihar Osun ya dakatar da Aregbesola bisa zargin cin amanar jam’iyya da sukar shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan...
    A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ta gudana a birnin Beijing na Sin, a shekarar 2022. An ce, gasar wasannin kankara ta wannan karo ta samu halartar ‘yan wasa fiye da 1270 da suka zo daga kasashe da yankuna 34 dake nahiyar Asiya, alkaluman da suka kai matsayin koli a tarihi. Inda har wasu kasashen da ba sa samun yanayi mai sanyi da muhalli mai kankara a cikin gida, kamarsu...
    Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dakta Ajuji Ahmed, ya tabbatar da shugabancinsa, inda ya yi watsi da ikirarin wani bangare na jam’iyyar, inda ya bayyana cewa shi ne wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da shi. Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Ahmed ya tabbatar da cewa, jam’iyyar na nan a karkashin shugabancinsa da kuma kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da aka kaddamar a shekarar 2022. Sin Ta Yi Watsi Da Tsegumin Da Marco Rubio Ya Yi Kan Hadin Gwiwarta Da Latin Amurka ‘Yansanda Sun Kama Mutum Uku Da Kokon Kan Mutum A Imo Dakta Ahmed ya jaddada cewa, INEC jam’iyyar NNPP daya ta sani, mai tambarin launin ja,...
    A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe, yayin da rahotanni ke cewa faɗa na kara yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar, sannan take hakkin ɗan’adam na ƙara munana. Jakadan Congo a Geneva ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar MDD ta gudanar da cikakken bincike kan hakan. Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun yi amannar cewa ƴan tawayen M23 da sojojin Rwanda da na Congo duk sun aikata munanan laifuka. Sai dai har yanzu Rwanda...
    Masana kimiyyar kasar Sin sun kirkiro wani sabon samfurin kirkirarriyar basira ta fasahar AI domin yin hasashen zuwan mahaukaciyar guguwa, wanda hakan ya ba da sabuwar fa’ida da kara haskaka hanyoyin inganta shirin tunkarar bala’o’i a duniya. A kwanan baya, masu bincike daga cibiyar nazarin teku a kwalejin kimiyya ta kasar Sin sun wallafa wannan binciken a cikin mujallar da ke wallafa harkokin kimiyya ta kasar Amurka, watau “Proceedings of the National Academy of Sciences.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
    Masu zanga-zanga a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Dimokaradiyyar Kongo sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashe da suka hada da Amurka da Faransa Masu zanga-zangar sun kai hare-hare a wasu ofisoshin jakadanci a birnin Kinshasa, fadar mulkin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar a makon da ya gabata, don nuna adawa da yadda ake ci gaba da ruruta wutar rikici a shiyar gabashin kasar. Shafin sadarwa na yanar gizo na Russia Today ya bayyana cewa: Al’ummar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da suke cikin fushi sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashen Rwanda da Faransa da Belgium da kuma Amurka, yayin da hayaki ke tashi daga ginin ofishin jakadancin Faransa. Masu zanga-zangar sun kona tutar Amurka tare...
    Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta kori Tsohon Gwamnan Jihar kuma Tsohon Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola, bisa zargin cin amanar jam’iyyar. Wannan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da shugabannin jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Ilesa ta Gabas suka gabatar. Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok bayan Hisbah ta daina kamensu Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau Sun nemi a ɗauki mataki a kan Aregbesola saboda zargin kafa ƙungiyoyin da ke raba kan jam’iyyar da yin haɗin gwiwa da jam’iyyun adawa don raunana APC a Osun. A cikin wata wasiƙa da kwamitin zartarwa na APC na Osun ya aike wa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, sun bayyana cewa Aregbesola ya kafa wata ƙungiya mai...
    Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin  kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
    Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka kasa daukaka kasar. Ahanotu ya kara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bai wa matasa damar gyara matsalolin da suka faru a baya. Ya ce, “Gaskiya ni ba masoyin Buhari ba ne kuma ban taba tsammanin zai yi abin kirki ba. Don haka ban yi mamakin cewa bai yi komai tsawon shekaru takwas ba. Amma abin da nake...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin shure-shure Jam’iyyar PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara ɗigaayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye ta. NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai nazari don bankado abin da yake faruwa da jam’iyyar yayin da 2027 take kara matsowa. Domin sauke shirin, latsa nan
    Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
    Bayan hare haren da mutane suka kai kan ofisoshin jakadancin kasashen Ugandan, Rwandan, Kenyan, Japan, Amurka da kuma Faransa a birnin Kinshasa na kasar Democradiyya Congo masu zamga-zanga sun fara kwasar ganima a manya-manyan shaguwa a birnin. Masu zanga-zangar sun fara tada hankali a kasar ne saboda irin saurin ci gaban da yan tawayen M23 suke mamayar kasar. Kuma suna ganin wadannan kasashe suna da hannu a tallafawa yan tawayen wadanda suke ci gaba da kwace garuruwa daga hannun sojojin Gwamnati. Labarin ya kara da cewa an ga hayaki na tashi a ofishin jakadancin kasar Faransa a Kinshasa, kuma suna yin haka ne don nuna turjiya ga halayen mulkin mallaka na kasar faransa, wacce take daga cikin wadanda suke goyon...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, da sauran jagororin kasar, sun taya tsoffin jami’an da suka yi ritaya murnar bikin Bazara, tare da musu fatan karin lafiya da kuma tsawon rai. A nasu bangaren kuwa, tsoffin jami’an da suka yi ritaya sun yaba da ayyukan kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a shekarar da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansu...