Masana Sun Bayyana Yadda Yakin Neman Zaben 2027 Ke Barazana Ga Harkokin Tafiyar Da Gwamnati
Published: 3rd, May 2025 GMT
A cewar kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi,
“Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta fitar da jadawalin ayyuka na babban zaben shekarar 2027 ba, inda ta kayyade lokacin da jam’iyyun siyasa za su yi yakin neman zabe a bainar jama’a, don haka bai dace ba, kuma ya saba wa doka, a ce wata jam’iyyar siyasa ta fara yakin neman zaben 2027.
Sai dai wasu lauyoyin da suka zanta da LEADERSHIP sun ce amincewa da ‘yan takara ba magana ce da za a ayyana a matsayin kamfe ba.
A cewarsu, cin zarafin dokar zabe ne kowa ya fara yakinn neman zabe a yanzu.
A nasa jawabin, Dr Wahab Shittu (SAN) ya danganta lamarin da rashin bin doka da oda da ‘yan siyasa ke da shi.
Shittu ya ce, “Batun ba wai na ita kanta doka ba ce, kawai a aiwatar da ita, sashe na 94 na dokar zabe ya fito karara kuma babu shakka, amma ‘yan siyasa da alama suna bin ka’idojin da suka kafa ne kawai.
“Abin takaici ne yadda ake yin watsi da dokokinmu, musamman a tsakanin ’yan siyasa, maimakon a kiyaye su, dole ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fara sanya ido tare da hukunta masu karya doka don ya zama an hana.”
Babban Lauyan Nijeriya, Abdul Balogun, ya ce ana sa ran ‘yan siyasa su san ka’idojin: ba za a fara yakinn neman zabe ba sai ya rage kwanaki 150 kafin zaben.
“Zaben 2027 ya rage kusan shekaru biyu, to me ya kowa tattauna batun yakin neman zabe a yanzu? Lokacin da aka amince da da hakan bai zo ba, abin da kuke gani yana faruwa a yanzu kokari ne na kawai daidaitawa, ‘yan siyasa sun san ba za su iya fara kowane irin yakin neman zabe ba tukuna,” in ji shi.
Wani Lauya masanin tsarin mulki Barista Samaila Abu ya zargi ‘yan siyasa da karkatar da robmon dimokuradiyya daga wadanda suka zabe su.
A cewarsa, ‘yan Nijeriya ba su amfana da komai daga ‘ yan siyayar ba tun bayan hawan su karagar mulki a shekarar 2023, amma duk da haka sun fara tattaunawa kan 2027.
“Shin hakan na nufin kwace mulki ne wanda shi ne abin da shugabanninmu suka damu da shi? Da na yi tunanin cewa, da a ce a yanzu jama’a sun amfana daga ‘yan takarar da suka zaba a 2023. To da hakan iya zama rashin abin nuna damuwa, kuma ya zama abu ne da ‘yan siyasa za su daidaita tare da kulla dangantaka kafin kowane zabe; wannan ba zai zama ana nufin yakin neman zabe ba,” in ji shi.
A nasa tsokaci, Dr Wahab Shittu (SAN) ya danganta lamarin da halayyar rashin bin doka da oda da ’yan siyasa ke nunawa wajen kin bin doka da oda.
Don haka, rusassun shugabannin matasan jam’iyyar Congress for Progressibe Change (CPC) da shugaban yankin Neja-Delta, Oweizide Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, sun yi fatali da tikitin takarar Tinubu/Shettima na zaben 2027.
Shugabannin matasan jam’iyyar CPC na jihar, daya daga cikin jam’iyyun da suka kafa jam’iyyar APC, sun yi kira ga jiga-jigan ‘mambobin da su mara wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima baya kafin shekarar 2027.
Shugabannin matasan CPC Nna kasa sun cimma wannan matsaya ne a karshen taron da suka yi a karshen mako a Abuja domin tattauna makomar jam’iyyar APC da kasa baki daya.
Shugaban matasan Jihar Kogi Sani Ogu Salisu, shugaban rusasshiyar kungiyar shugabannin matasan jihar ta CPC, da sakataren kungiyar Iyke Uwakwe ne suka bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
Sun yi kira ga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jam’iyyar CPC da su goyi bayan tattaunawar masu ruwa da tsaki a karkashin jagorancin Sanata Tanko Al-Makura kan sake fasalin jam’iyyar APC.
Shugabannin matasan CPC sun bukaci shugaban majalisar wakilai Hon. Abbas Tajudeen, Gwamna Umar Bago na Jihar Neja, Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina, da ‘yan Majalisar Dokoki na kasa da na jiha, da kuma jiga-jigan zababbun shugabannin kananan hukumomin CPC na goyon bayan Tinubu/Shettima da masu ruwa da tsaki a karkashin Al-Makura.
“Ku hada hannu da masu ruwa da tsaki a karkashin jagorancin Al-Makura domin sake dawo da martabar jam’iyyarmu don kare kalubalen da ke gabanmu, su kyale jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima gabanin zaben 2027.
“Wannan tallafin yana da matukar muhimmanci ga hadin kan jam’iyya, kokarin sake fasalin zai inganta dimokuradiyyar cikin gida, hadin kai, da zaman lafiya a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya, hadin kai da tsari mai kyau zai kara mana damar samun nasara a zaben 2027. Ta hanyar goyon bayan gwamnatin Tinubu/Shettima, za mu iya tabbatar da ci gaba a ayyukan ci gaban kasa.
“Mun yi imanin cewa aiki tare da goyon bayan tattaunawar masu ruwa da tsaki a karkashin Al-Makura zai karfafa jam’iyyarmu da kuma ba mu damar samun nasarar zabe.
“Muna kira ga masu ruwa da tsaki da su hada hannu da mu domin gina jam’iyyar APC mai karfi da kuma kyakkyawar makoma ga Nijeriya,” in ji su, inda suka kara da cewa shugaban matasan jam’iyyar na kasa, Hon. Abubakar Maikudi, da su koma jihohinsu daban-daban da kuma hada kan jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Hakazalika, Tompolo ya nuna goyon bayansa ga sake zaben Shugaban Kasa Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.
Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise News a ranar Asabar, Ibe-Ebidouwei na Ijaw Nation kuma Grand Patron na PBAT Door-2-Door Mobement 2027, ya bayyana Tinubu a matsayin gogaggen shugaba da gogewa wajen daukaka Nijeriya zuwa ga mafi girma.
Tompolo ya ce “Tinubu mutum ne nagari, yana da gogewa wajen yin komai da kuma kai kasar nan zuwa wani mataki mai girma.”
Ya jaddada cewa, ya kamata a mutunta wa’adin shekaru hudu na Tinubu, tare da yiwuwar sake tsayawa takara na wasu shekaru hudu, inda ya kwatanta wa’adin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na shekaru takwas. “Ba ma son kowa ya kawo matsala, a bar shi ya kammala wa’adinsa na kundin tsarin mulkin kasar guda biyu, sannan za mu kada kuri’a ga wani ya karbi mulki a 2031,” in ji shi.
Tompolo ya bayyana shirin fara yakin neman zabe a fadin kasar, ciki har da ziyarar jihohin arewa, domin samun goyon bayan Tinubu a wa’adi na biyu.
“Za mu yi namu bangaren, har ma mu fita daga kan iyakokinmu zuwa yankin arewacin Nijeriya mu tattauna da ’yan’uwanmu domin ya samu wa’adi na biyu,” in ji shi.
Ya kuma yi nuni da cewa sarakunan gargajiya a fadin yankuna sun amince da yunkurin sake tsayawa takara da Tinubu ya yi, inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa goyon bayan da ake samu zai tabbatar da ci gaba da shugabancin shugaban kasa.
Da yake jawabi game da damuwa kan yiwuwar tashin hankali, Tompolo ya yi watsi da ikirarin duk wata kungiya da ke da “tashin hankali,” yana kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su goyi bayan gwamnatin Tinubu.
“Muna kira ga kowa da kowa, kuma da yardar Allah kowa zai tallafa mana,” in ji shi.
Da yake tsokaci kan al’amuran siyasa a Jihar Ribas, Tompolo ya bayyana kwarin gwiwar warware takaddamar da ta kunno kai tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da aka dakatar da kuma wanda ya gada, Nyesom Wike.
“Zababben gwamnan Jihar Ribas zai dawo,” in ji shi, yana mai nuni da dawowar Fubara kan mukaminsa.
Tompolo ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai je Abuja domin ganawa da shugaba Tinubu da Wike domin magance matsalolin da ke addabar Jihar Ribas.
“Shugaban mu ya dade yana kare dimokuradiyya, babu yadda zai yi ya durkusar da ita,” in ji shi.
Kalaman fitaccen dan kabilar Ijaw na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara tabarbarewa yayin da Nijeriya ke kara fuskantar babban zaben 2027.
Tompolo babban mai ba da shawara ne ga ci gaba da jagorancin Tinubu da kwanciyar hankali a Jihar Ribas.
Lokaci ne da mulki zai koma arewa ta tsakiya – Gamayyar kungiyoyin siyasa
Kungiyar North Central Renaissance Mobement (NCRM), gamayyar kungiyoyin da ke jagorantar yunkurin neman shugabancin kasar zuwa yankin siyasa, ta bayyana cewa 2027 lokaci ne da shugabanci zai dawo yankin.
Sai dai gwamnonin yankin da shugaban kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya da kuma gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule suka wakilta, sun bukaci kungiyar da ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin ladabi, da’a, da kuma nutsuwa.
Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da gamayyar kungiyoyin karkashin jagorancin Farfesa K’tso Nghargbu, suka gudanar da taron tuntuba da shi domin neman goyon bayansa kan dawo da shugabancin yankin.
Ya bukaci kungiyar da ta ci gaba da bin doka da oda na sake farfado da yankin da ba ta taba samar da zababben shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ta hanyar dimokradiyya ba, domin samun goyon bayan da ake bukata.
Gwamnan da wasu fitattun mutane sun bayyana gamsuwarsu da irin kimar mutanen da Nghargbu ke jagoranta na ganin an amince da yankin Arewa ta Tsakiya, dangane da sauran shiyyoyin siyasar kasa da ke da karfin ikon kasar tun bayan samun ‘yancin kai.
NCRM ta kuma yi shawarwari daban-daban da tsofaffin ‘yan majalisar dokokin kasar da suka hada da Sanata Solomon Ewuga, Sanata Suleiman Asonya Adokwe, da mataimakin shugaban majalisar sarakuna da sarakunan Jihar Nasarawa, Sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo Yamusa.
A yayin ganawar, kungiyar ta nemi goyon baya kan yunkurin da take yi na tabbatar da shugabancin kasa ko mataimakin shugaban kasa a 2027 tare da samun amsoshi masu karfafa gwiwa wadanda suka amince da ajandar Arewa ta tsakiya a daidai lokacin da ya dace.
Har ila yau kungiyar ta gabatar da takardar cimma matsaya ga fitattun ‘yan Nijeriya ciki har da Sarkin Keffi, wanda ya albarkaci dandalin tare da bukata su da su jajirce da sadaukar da kai wajen cimma manufofinsu.
Shugaban kungiyar, Farfesa Nghargbu, ya ce kokarin kungiyar na da nufin sake rubuta tarihin siyasar kasar, wanda a baya-bayan nan ya hana shiyyar Arewa ta tsakiya damar yin takarar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a kwanakin baya kungiyar ta bayyana cewa idan har jam’iyyar APC ta zabi bai wa Shugaban Kasa Bola Tinubu ‘yancin kin fara ayyana tikitin takara a 2027, to dole ne abokin takararsa ya fito daga yankin Arewa ta tsakiya, yayin da sauran jam’iyyu za su tsayar da ‘yan takarar shugaban kasa daga shiyyar.
“Bayan tarihin Arewa ta Tsakiya daga manyan ma’aikatun kasa guda biyu ya zarce duk wani ikirari na mayar da siyasa saniyar ware daga kowane yanki na geopolitical. Muna ba da shawara mai karfi cewa bukatun adalci, da hadin kai na siyasa ka iya fara haduwa da jagororin jam’iyyar adawa, PDP, da kuma jam’iyyar APC mai mulki, wajen zaben ‘yan takarar su na shugaban kasa da mataimakinsa a 2027.
“Duk sauran jam’iyyun siyasar da ke da muradin shugabancin kasar nan a cikin shekaru biyu su ma su yi taka-tsan-tsan daga wannan adalcin siyasar da ake sa ran mutanen Arewa ta Tsakiya ke nema, irin wannan mataki a lokaci guda zai biya bukatun duk wani hazikin dan siyasa da ake sa ran kowace jam’iyya da hannunta a kan al’ummar kasa.
“A kan haka ne mu ‘yan Arewa Central Renaissance Mobement (NCRM) muke nema, domin tabbatar da gaskiya, daidaito da adalci, a mika ofishin Shugaban Nijeriya ga Arewa ta Tsakiya a 2027,” in ji ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: masu ruwa da tsaki a karkashin yakin neman zabe Arewa ta tsakiya Arewa ta Tsakiya jam iyyar APC yan Nijeriya tabbatar da Jihar Ribas a jam iyyar goyon bayan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Ta ƙaddamar Da Sabon Shafin Intanet Don Inganta Sayayya A Tsakanin Ma’aikatunta
Ministan ya ce sabon gidan yanar na intanet zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da suka daɗe suna dagula harkokin sayayya a gwamnati, kamar yadda ake fama da rashin ingantattun tsare-tsare, ƙarancin ƙwararru da rashin tsarin horaswa na dindindin.
Ya ce: “Ƙaddamar da wannan sabon shafin ba kawai cigaba ba ne a fannin fasaha; wata babbar hanya ce ta sauya fasalin aiki gaba ɗaya wadda ke magance manyan ƙalubale a tsarin sayen kaya na gwamnati, irin su cikas da ke yawan faruwa, rashin ingantattun hanyoyin sayayya, ƙarancin ma’aikatan da suka dace, da kuma rashin ingantaccen tsarin gina ƙwarewa.
“Waɗannan matsaloli sun daɗe suna hana a yi amfani da dukiyoyin gwamnati yadda ya kamata tare da kawo cikas ga cigaban tattalin arziki gaba ɗaya a ƙasar nan.”
Ya ce wannan sabon tsari zai bai wa jami’an sayayya damar samun horo, takardun shaida, da kuma damar yin aiki da ƙwarewa, daidai da matakin duniya.
Idris ya ce: “Za a tabbatar da cewa mu jami’an gwamnati muna sayen kaya ba kawai bisa doka ba, har ma ƙwararru ne kuma masu iya gogayya a matakin duniya.”
Idris ya yaba wa Darakta-Janar na BPP, Dakta Adebowale Adedokun, bisa jajircewa da hangen nesan sa wajen inganta tsarin sayayya a Nijeriya.
Ya ce wannan gidan yana hujja ce ta jajircewar sa wajen ganin an sabunta tsarin sayayya a ƙasar nan.
Ministan ya kuma buƙaci ‘yan ƙasa da su fahimci cewa sabon gidan yanar ba kawai don gwamnati ba ne, har ma wata hanya ce da za su iya amfani da ita wajen neman ingantattun ayyuka da gaskiya.
“Don haka ina kira ga dukkan hukumomi da jami’an gwamnati da su rungumi wannan shiri gaba ɗaya, kuma ina kira ga kafafen yaɗa labarai, musamman, da su taimaka wajen yaɗa amfanin sa da kuma sa ido kan yadda ake aiwatar da shi,” inji shi.
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack; Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Mista Wale Edun; Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa; Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim; Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (rtd); da Darakta-Janar na FRCN da NTA, Dakta Mohammed Bulama da Kwamared Abdulhamid Dembos.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp