Gwamna Buni Ba Zai Shiga Hadakar Jam’iyyun Adawa ba – Mai Magana Da Yawunsa
Published: 27th, April 2025 GMT
Mai magana da yawun Gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana sakon a matsayin kirkirarre kuma marar tushe da makama, wanda yayi hannun riga da gaskiya, ta wane bangare a cikin wannan shaci-fadi.
Ya ce ba a taba yin makamancin wannan sakon ba, kuma mai wannan maganar bai taba zama makusancin Gwamna ba, ballantana ya iya gano ra’ayinsa ko ya iya hasashen yanayin siyasarsa.
“Gwamna Buni bai tsaya kawai dan jam’iyyar APC ba; ko kawai gwamnan APC ba. Shi ne APC gaba dayanta, saboda sanannen abu ne cewa APC ta ratsa jijiyoyin jininsa.
“Sannan gudunmawar da ya bayar wajen gina APC a matsayinsa na Sakatarenta na kasa sau biyu, kuma ya rike ragamar Shugaban kwamitin tsara taron jam’iyyar; ya bambanta shi da sauran yayan jam’iyyar, kuma ba abu bane mai yuwa ba ace ya bar jam’iyyar.” In ji shi.
Mai magana da yawun Gwamnan ya ce, marubucin sakon tare da masu daukar nauyinsa, ko shakka babu, yanayin salon siyasar Gwamna Buni ya na burgesu, sannan suna burin kasancewa irinsa, “amma kawai, wannan ya na iya zama kawa-zuci.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.
Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.
Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.
Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.
Usman Muhammad Zaria