Aminiya:
2025-11-02@16:04:09 GMT

Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 

Published: 2nd, November 2025 GMT

Fadar Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa nan da wasu kwanaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya.

Mai ba wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan

A cewar Daniel Bwala, shugabannin biyu — Tinubu da Trump — sun yi tarayya da juna kan fahimta ta haɗin kai wajen yaƙi da ta’addanci da duk wata barazana ga bil’adama.

“A bayan nan Shugaba Trump ya taimaka wajen ba da izinin sayar wa Nijeriya makamai, kuma Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar yadda ya kamata wajen yaƙi da ta’addanci, kuma muna da sakamakon da za mu iya nunawa,” in ji Bwala.

Ya ƙara da cewa duk wani saɓanin fahimta kan ko ‘yan ta’adda a Nijeriya na kai hari ne ga Kiristoci kaɗai ko kuma mabiyan addinai daban-daban, “za a tattauna kuma a warware su” a yayin ganawar shugabannin biyu, wadda za ta gudana “ko dai a Fadar Shugaban Kasa ta Abuja, ko a Fadar White House da ke Washington.”

Sanarwar ta zo ne bayan barazanar Shugaba Trump ta kai farmaki a Nijeriya, inda ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta fara tsara yadda za a kai hari kan ƙasar, saboda abin da ya kira “kisan gillar da ake yi wa Kiristoci” a Nijeriya.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, Trump ya ce Amurka “a shirye take ta turo sojojinta da manyan makamai zuwa Nijeriya don kare Kiristoci,” yana mai cewa idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma “mai yiwuwa ta shiga ƙasar don kawar da ‘yan ta’adda masu zafin kishin Musulunci.”

Barazanar Trump ta jawo cece-kuce bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya, ba tare da ya bayyana takamaiman inda ya samo waɗannan alƙaluman ba.

Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai kiyaye dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.

“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Daniel Bwala Kiristocin Najeriya wa Nijeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

Shugaba Bola Tinubu ya yi wa sabbin Shugabannin Sojoji ado da karin girma domin su dace da sabbin muƙamansu. Sabbin shugabannin rundunar sojin kasar da aka yi wa ado sun hada da Laftanar Janar, wanda yanzu ya zama Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS); da kuma Manjo Janar yanzu ya koma Laftanar Janar Emmanuel Undiendeye Undiendeye a matsayin Babban Hafsan Tsaro na farin kaya (CDI). Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda  Sauran su ne Manjo Janar, wanda yanzu ya zama Laftanar Janar Waidi Shaibu a matsayin Babban Hafsan Soja (COAS); Air Vice Marshal, wanda yanzu ya zama Air Marshal Kevin Aneke a matsayin Babban Hafsan Sojan Sama; da kuma Rear Admiral, wanda yanzu ya zama Vice Admiral Idi Abbas a matsayin Babban Hafsan Sojan Ruwa. Shugaba Tinubu ya sanar da maye gurbin Shugabannin Rundunar tsaron ne a ranar Juma’ar da ta gabata, wani mataki da aka danganta da bukatar sake mai da hankali da kuma karfafa tsaron kasa. Bayan haka, Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin Shugabannin Rundunar tsaron da su dauki mataki mai tsauri kan barazanar tsaro da ke tasowa a fadin kasar, yana mai gargadin cewa ‘yan Nijeriya na tsammanin ganin sakamako, ba uzuri ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda  October 30, 2025 Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
  • Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai