Aljeriya ta yi barazanar korar jami’an diflomasiyyar Faransa 12
Published: 14th, April 2025 GMT
Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa.
“Ina kira ga hukumomin Aljeriya da su yi watsi da wannan matakin, inda ya kara da cewa: “Idan har aka ci gaba da yanke shawarar korar wakilanmu, ba mu da wani zabi illa mu mayar da martani cikin gaggawa.”
Shekaru da dama, alakar diflomatoyyar da ke tsakanin Aljeriya da Faransa ta yi tsami.
A farkon watan Afrilu, ministan harkokin wajen Faransa ya je kasar Aljeriya, domin kokarin warware matsalolin da suka jefa kasashen biyu cikin tabarbarewar diflomasiyya.
Bayan ganawa da shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, Jean-Noël Barrot ya bayyana muradin kasashen biyu na “sake gina dangantakar abokantaka.”
A daidai lokacin da ake fuskantar tsamin dangantaka tsakanin Algiers da Paris, ofishin mai gabatar da kara na Faransa ya tuhumi, wasu ‘yan kasar Aljeriya uku, a ranar 11 ga Afrilu, ciki har da wani jami’in ofishin jakadanci, da zarginsu da hannu a sace wani dan adawar gwamnatin Algeria, Amir Boukhors, da aka sani da “AmirDZ na Paris” a cikin 2024.
Aljeriya ta yi kakkausar suka a ranar Asabar, 12 ga Afrilu, don nuna adawa da kamawa da tsare daya daga cikin jami’an ofishin jakadancinta a kasar Faransa tare da neman a gaggauta sakin shi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Aljeriya Aljeriya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Tashin Gobara A Kwale-Kwale Ya Lashe Rayukan Mutane 143 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango
Bala’in Kogin Congo: Kwale-kwale ya kama wuta, ya kashe mutane 143
A wani mummunan lamari da ya afku a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, akalla mutane 143 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kama da wuta a kogin Kongo da ke arewa maso yammacin kasar.
Akalla mutane 143 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kama da wuta a kogin Kongo da ke arewa maso yammacin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, kamar yadda majiyoyin hukuma suka bayyana.
“An gano rukunin farko na gawarwakin mutane 131 a ranar Laraba, kuma an sake gano wasu 12 a ranakun Alhamis da Juma’a,” ‘yar majalisar wakilan kasar Josephine Pacific Lokomo ta shaida wa kafar yada labaran Faransa.
A nasa bangaren, Joseph Lokondo, shugaban kungiyoyin farar hula na yankin, ya bayar da bayanai kan adadin wadanda suka mutu na wucin gadi, wanda ya kai mutane 145.