Shugaban Kasar Iran Ya Aike Da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Papa Roma Farancis
Published: 21st, April 2025 GMT
A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya.
Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce ta kalubalantar yadda ake take hakkin bil’adama a duniya, musamman mai dai yadda ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa a Gaza.
Fizishkiyan ya kuma kara da cewa; Wadannan matakan da Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa za su wanzar da ambatonsa a cikin zukatan masu rayayyen lamiri da kuma wadanda suke yin kira da tabbatr da ‘yanci a duniya.
Shugaban kasar na Iran ta kitse sakon nashi da cewa; A madadin ni kaina da kuma al’ummar Iran ina yin jinjina ga mamacin wanda ya yi fafutuka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.
A yau Litinin ne dai Fadar Vatican ta sanar da rasuwar Papa Roma Farancis wanda shi ne dan asalin yankin Latin na farko da ya jagoranci majami’ar .
Fadar ta kuma sanar da zaman makoki na kwanaki 9, sannan kuma ta sanar da cewa nan da makwanni biyu zuwa uku za a fara shirye-shiryen zabar sabon Papa Roma.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta
A jiya Litinin ne dai gwamnatin kasar Holland ta sanar da hana wa minstocin tsaron kasa Itmir Bin Gafir, da na kudi, Bitsirael Smotrich shiga cikinta.
Kasar ta Holland ta zargi wadannan mutanen biyu da cewa suna ingiza sojojin HKI da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da kuma fadada yawan matsugunan ‘yan sahayoniya a yankunan da aka ce nan ne za a kafa Daular Falasdinawa.
Haka nan kuma gwamnatin kasar ta Holland ta kira yi jakadan HKI a birnin Hauge domin gargadinsa akan yanayin da ake ciki a Gaza, da cewa babu yadda za a iya ci gaba da jurewa akansa, ko kare dalilin jefa yankin cikin wannan halin.”
Wannan matakin na kasar Holland ya zo ne gabanin wani taro da tarayyar turai za ta yi a yau Talata domin jingine aikin tare da HKI a fagen nazari da bincike na ilimi, saboda ta ki tsagaita wutar yaki a Gaza.
Tun da fari, Fira ministan kasar Holland Dick Schoof ya wallafa a sharin X cewa; A yayin taron da kasashen turai za su yi, Kasarsa za ta yi matsin lamba akan ganin an dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da HKI, haka nan kuma kakaba takunkumai akan shigar da kayanta na kasuwanci zuwa kasuwannin turai.
Fira ministan na kasar Holland ya ce, ya fada wa shugaban HKI Ishaq Herzog wannan matakin da suke son dauka ta hanyar tarayya turai.