Iran Ba Ta Da Niyyar Tattaunawa Da Amurka A Fili Bainar Jama’a Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Published: 22nd, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba su da niyyar gudanar da tattaunawa da Amurka a fili
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba ta da niyyar yin shawarwari da Amurka a fili a bainar jama’a.
Araghchi ya rubuta a shafinsa na Twitter da safiyar yau Talata cewa, “Lokacin da ya amince da gabatar da muhimmin jawabi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, har yanzu Iran da Amurka ba su sanya ranar da za a yi shawarwarin zagaye na gaba ba, wanda za a fara a matakin kwararru a ranar Laraba da kuma babban mataki a ranar Asabar.
Ya kara da cewa, “Kamar yadda ya jaddada a cikin jawabinsa da ya shirya, ko kadan Iran ba ta da niyyar yin shawarwari a fili a bainar jama’a.” Araghchi ya ci gaba da cewa, “A cikin jawabinsa, ya kuma bayyana karara cewa wasu ‘kungiyoyin masu sha’awa na musamman’ na kokarin yin magudi tare da bata tsarin diflomasiyya ta hanyar bata sunan masu tattaunawan tare da yin kira ga gwamnatin Amurka da ta gabatar da bukatu mafi tsanani da girma.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.
Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.
Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya ce an tsara wannan asusu ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.
Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.
Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a wuraren.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.