Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Published: 2nd, November 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar.
A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne.
Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da kasashen duniya ke ba ta musamman kan batun hakkin dan’adam da hakkin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a kasar ba haka ba ne.
Duk yan Najeriya suna da yancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.” Inji sanarwar.
Shi dai shugaban Amurka Donald Trump Ya ce kiristanci na fuskantar babbar barazana a Najeriya,”, inda ya kara da cewa ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata wannan kisan gillar.
“Saboda haka ya ayyana Najeriya kasar da ake da damuwa a kanta.”
Bugu da ƙari, Trump ya ce ya bai wa ‘yan majalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin fara bincike kan hakan kuma su kai masa rahoton sakamakonsa.
Gwamnatin Najeriya dai ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka da kasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci