HausaTv:
2025-11-02@21:51:04 GMT

Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani

Published: 2nd, November 2025 GMT

Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba suna cewa ba za su gudanar da tattaunawa ba ne, amma tattaunawar dole ta kasance ta gaskiya

Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Ali Larijani, ya tabbatar da cewa: Ba za a iya kwantar da hankalin makiya ta hanyar yin sassauci da rashin gindaya sharaɗi ba.

Da yake jawabi a wani taron masana ilimin bil’adama a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ‘yan kwanaki da suka gabata, Larijani ya bayyana cewa: “Hanya madaidaiciya ta gyara halayen makiyansu tana cikin ƙarfafa haɗin kan ƙasa, kuma tushenta shine gyare-gyaren tattalin arziki da dawo da kwanciyar hankali ga rayuwar mutane.”

Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba za a iya kwantar da hankalin makiya ta hanyar yin sassauci da rangwame kan hakki ba gami da rashin gindaya sharaɗi ba, yana mai ƙarawa da cewa: “Mutanen da suka amince kan wajabcin inganta sinadarin Uranium, yanzu suna cewa bai kamata Iran ta yi ba; su masu neman duk wata dama ce kan cimma munanan manufofinsu.”

Larijani ya nuna cewa: Babu ƙarshen buƙatun Amurka, kamar yadda suke cewa: “Bayan hana inganta Uranium, zasu bukaci rage karfin makaman kasar Iran tare da bukatar yin ayyukan kasa kamar yadda suka Sanya ake yi a yankin.” Ya bayyana: “Yana ganin akwai buƙatar juriyar ƙasa kan waɗannan buƙatun, kuma Iran da al’ummar kasarta dole ne su tsaya su kalubalanci duk wata mummunar manufa kansu.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza November 2, 2025 Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande da shugaban CMG Shen Haixiong, sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo.

A cewar ministan na Nijeriya, cikin shekaru 5 da suka gabata, dubban matasan kasar sun ci gajiyar tallafin karatu da shirye-shiryen horo da na musaya da Sin ta samar, kuma wannan hadin gwiwa da ake yi a aikace ya kara fahimta da aminci tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, a shirye ma’aikatarsa take ta karfafa hadin gwiwa da sassa masu ruwa da tsaki na kasar Sin wajen ci gaba da fadada shirye-shiryen musaya da na hadin gwiwa da suka shafi matasa.

A nasa bangare, Shen Haixiong ya ce a matsayinta na babbar kafar yada labarai dake watsa shirye shiryenta ga sassa daban daban na duniya, tashar talabijin ta CCTV dake karkashin CMG da abokan huldarta, za su yayata shawarar Sin ta jagorantar harkokin duniya da gabatar da tafarkin Sin na zamanantar da kanta da karfinta na kirkire kirkire a sabon zamani ga al’ummar duniya. (Mai fassara: FMM)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung  November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3