Leadership News Hausa:
2025-11-03@03:58:35 GMT

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazanar Sa Ga Nijeriya

Published: 3rd, November 2025 GMT

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazanar Sa Ga Nijeriya

Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa.

Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in ji shi.

A ƙarshe, yayi kira ga ƴan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da juriya, yana mai cewa lokaci ne da ya kamata a fifita zumunci fiye da rarrabuwar kai.

Yan uwa ƴan Nijeriya, lokaci ne da muke buƙatar haɗin kai fiye da komai. Allah ya taimaki Nijeriya,” in ji Kwankwaso.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba November 2, 2025 Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 

Fadar Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa nan da wasu kwanaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya.

Mai ba wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan

A cewar Daniel Bwala, shugabannin biyu — Tinubu da Trump — sun yi tarayya da juna kan fahimta ta haɗin kai wajen yaƙi da ta’addanci da duk wata barazana ga bil’adama.

“A bayan nan Shugaba Trump ya taimaka wajen ba da izinin sayar wa Nijeriya makamai, kuma Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar yadda ya kamata wajen yaƙi da ta’addanci, kuma muna da sakamakon da za mu iya nunawa,” in ji Bwala.

Ya ƙara da cewa duk wani saɓanin fahimta kan ko ‘yan ta’adda a Nijeriya na kai hari ne ga Kiristoci kaɗai ko kuma mabiyan addinai daban-daban, “za a tattauna kuma a warware su” a yayin ganawar shugabannin biyu, wadda za ta gudana “ko dai a Fadar Shugaban Kasa ta Abuja, ko a Fadar White House da ke Washington.”

Sanarwar ta zo ne bayan barazanar Shugaba Trump ta kai farmaki a Nijeriya, inda ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta fara tsara yadda za a kai hari kan ƙasar, saboda abin da ya kira “kisan gillar da ake yi wa Kiristoci” a Nijeriya.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, Trump ya ce Amurka “a shirye take ta turo sojojinta da manyan makamai zuwa Nijeriya don kare Kiristoci,” yana mai cewa idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma “mai yiwuwa ta shiga ƙasar don kawar da ‘yan ta’adda masu zafin kishin Musulunci.”

Barazanar Trump ta jawo cece-kuce bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya, ba tare da ya bayyana takamaiman inda ya samo waɗannan alƙaluman ba.

Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai kiyaye dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.

“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso
  • Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
  • Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede