Babu Dalilin Da Zai Sanya Wasu Mambobin PDP Ficewa A Jam’iyyar A Bauchi
Published: 3rd, May 2025 GMT
“Ka san idan za ka yi la’akari da sauran jihohin da suke barin jam’iyyarsu su shiga wata jam’iyya ni a tunanina tsoro ne karawa da babban jam’iyyar adawar da ke jihar ba, yanzu misali a Jihar Delta shi gwamnan jihar ya san daker ya ci zabe a 2023 sannan kuma yana da yakinin idan bai fita daga PDP ya shiga APC ba ba zai iya samun nasara a 2027 ba; to mu in ka yi la’akari da hakan a jam’iyyar mu ta PDP a Jihar Bauchi tun da ake mulki sau daya APC ta samu galba a 2015 sakamakon maja wanda ya ci ko’ina.
“Balle kuma yanzu da gwamna Bala Muhammad Abdulkadir ke gudanar da kyawawan ayyuka da kawo ci gaba da kyautata wa jama’a da inganta fannoni daban-daban wanda al’ummar jihar gaba daya sun yi gamsu da kokarinsa ba wani dalilin da wani zai ji sha’awar ficewa daga jam’iyyar.”
Ya nuna cewa duk da matsalolin da jam’iyyun siyasa ke fuskanta a Nijeriya bai takaita ga PDP zalla ba, amma ba su ji dadin yadda wasu fitattun mutane ke ficewa daga jam’iyyar ba ciki har da gwamnan jihar Delta, da tsohon gwamnan da ‘yan majalisu tarayya da na jihohi, da shugabannin kananan hukumomi a ce sun bar jam’iyyar PDP ba karamin rashi ba ne.
Sai dai ya tabbatar da cewa wannan matakin ba zai shafi nasarar da jam’iyyar ta saba samu a jihar Delta ba, ya tabbatar da cewa PDP ce za ta yi nasara a Delta a zaben 2027 da ke tafe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
A zantawar Sule Lamido da BBC, ya bayyana cewa; an yi masa kora da hali a hedikwatar jam’iyyar ta PDP.
Ya kara da cewa, ya je hedikwatar jam’iyyar PDP ne; domin karbar fom na takarar shugabancin PDP, sai ya samu ofishin da ya kamata ya karba a kulle, da ya tambaya sai aka ce da shi, a hannun gwamnan Adamawa kadai zai samu fom din.
Lamido ya ci gaba da cewa, ba ya fata a kai ga matakin da za a hana shi shiga takarar, “domin ina tunanin rigimar cikin gida ce, sannan kuma za mu iya samun maslaha a cikin gidan. Amma idan hakan bai yiwu ba, daga nan kuma na san me zan yi,” in ji shi.
Haka zalika, Sule Lamido ya ce; a shirye yake ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar a zaben da za a yi lokacin babban taron jam’iyyar a watan Nuwamban wannan shekara a birnin Ibadan na Jihar Oyo.
Bugu da kari, Lamidon ya sha alwashin tafiya kotu idan har aka ki sayar masa da fom din tsayawa takarar.
Kazalika, rahotanni sun tabbatar da cewa; tuni tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki ya yanki nasa fom din, a daidai lokacin da aka ki sayar wa da tsohon gwamnan na Jigawa fom din takarar shugabancin jam’iyyar ta hamayya, wato PDP.
Har wa yau, Jam’iyyar PDP ta sanar da dage tantance dan takara daga ranar Talata zuwa wani lokaci nan gaba, duk da cewa; jam’iyyar ba ta fadi dalilin yin hakan ba.
Haka nan, sanar da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin dantakarar maslaha daga Arewacin Nijeriya ya bar baya da kura, inda wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso yammacin kasar, shiyyar da Turaki ya fito suka yi watsi da matakin da gwamnoni suka dauka.
Kazalika, shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Sakkwato, Muhammad Bello Aliyu na cikin shugabannin da suka yi fatali da matakin da gwamnonin suka dauka, saboda a cewarsa, ba a ba su damar zama su tattauna ba, gabannin tsayar da Turakin. Kana kuma, an sake samun wasu jiga-jigan jam’iyyar daga Jihar Kebbi da suka yi fatali da wannan maslahar.
Dangane da wanan sabuwar rigima ko rikici, malami a kwalejin ilimi ta share fagen shiga jami’a da ke Kano kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Dakta Kabiru Sa’id Sufi ya ce; ana neman fama karaya ne a yunkurin gyara targade.
“Mun dauka cewa, tunda aka zo batun zaben shugabanci, matsalolin da jam’iyyar ke ciki sun kusa zuwa karse, musammman ganin har an yi kokarin rarraba mukamai zuwa shiyya-shiyya, amma kuma sai hakan ya bar baya da kura.
“Yanzu haka, an fara samun korafi daga bangarori da dama, ciki har da daga wadanda ake ganin ba su da wata matsala.”
Haka nan, ya kara da ce; hana Sule Lamido sayen fom din takarar shugabancin jam’iyyar, wani babban al’amari ne, domin kuwa a cewar tasa; hakan ya kara haifar da rashin gamsuwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.
Ya ce, “Akwai da ma wasu da suke ganin an lasa musu zuma a baki a Arewacin kasar na tsayawa takara, sai daga baya suka gane cewa, ba da gaske ake ba. Idan aka duba, za a ga akwai rashin gamsuwa daga bangarori da yawa. Ko bangaren Shekarau ma, sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al’amuran.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA