Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
Published: 2nd, November 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya , da kuma halin da yankin ke ciki da yi yuwar sake komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka.
Wannan bayani yazo ne adaidai lokacin da lamura ke kara zafi a yankin bayan yakin da aka yi tsakanin iran da kuma Israila, don haka bayanan na Araqchi wata sanarwa ce dake nuna shirin iran na mayar da martani amma kuma tabar kofar tattaunawar diplomasiya a bude.
Har ila yau ministan ya bayyana cewa iran a shirye take ta tunkari duk wani kalu-bale, kuma za ta mayar da martani mai karfi game da duk wani wuce gona da irin Isra’ila, don mun shirye fiye da kowanne lokaci a baya, kuma yayi gargadin cewa isra’ila za ta sake shan wani kayen idan ta kara shelanta yaki akan iran a nan gaba,
Yace isra’ila tana kokarin kara fadada rikicin yanki ne ta hanyar kai hari kan abubuwan manfetur din kasar iran, yace isra’ila ba za ta iya shiga wani yaki ba ba tare da samu amincewar Amurka ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan
Isra’ila ta amince da gina sabbin gidaje 1,300 a yankin Gush Etzion, kudu da Gabashin Urushalima da ta Mallake, wanda hakan ke nuna wani sabon ci gaba da fadada matsugunai ba bisa ka’ida ba a fadin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.
A cewar tashar talabijin ta Isra’ila Channel 14, Kwamitin tsare-tsare da Gine-gine na musamman da ke kula da matsugunan da ke Gush Etzion ya amince da wannan shawara a farkon wannan makon, inda ya shafi unguwar Har HaRusim, wadda ke kusa da matsugunan Alon Shvut, kudu maso yammacin Gabashin Urushalima da aka Mallake.
Shirin bai shafi gidaje ba kawai, har ma da gina makarantu, wuraren jama’a, wuraren shakatawa, da kuma babbar cibiyar kasuwanci da aka yi niyya don yi wa al’ummomin da ke makwabtaka hidima.
Majalisar Yankin Gush Etzion ta yi maraba da wannan mataki, tana mai ganin hakan a matsayin martani ga karuwar bukatar mazauna yankin.
Wannan sanarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da damuwar da ake da ita game da ayyukan Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan.
Jawabin Trump ya zo ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta amince da wasu kudirori biyu da nufin hade Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma yankin Ma’ale Adumim.
Irin wadannan matakai za su ware Gabashin Kudus daga yankunan Falasdinawa da kuma raba Yammacin Kogin Jordan zuwa yankuna biyu daban-daban, don haka za su kawo cikas ga yiwuwar hadewar kasar Falasdinu.
Majalisar Dinkin Duniya da yarjejeniya kasa da kasa sun sha nanata cewa matsugunan Isra’ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye haramtattu ne a karkashin dokokin kasa da kasa, gami da Yarjejeniyar Geneva ta Hudu.
Bugu da kari, kungiyar kare hakkin dan adam ta Peace Now ta bayyana shirin E1 a matsayin “mummunan rauni” ga samar da Falasdinu, tana mai jaddada cewa aiwatar da shi zai kawo cikas ga yunkurin kafa kasar Falasdinawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci