Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC
Published: 30th, April 2025 GMT
Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta ce guguwar sauyin sheƙa ta jiga-jigan ’yan siyasa da ke ficewa daga jam’iyyar NNPP alama ce da ke nuna cewa tasirin tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a siyasance na ƙara disashewa.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar matasan ta KASASCO ta fitar a ranar Talata, ta ce a halin yanzu jam’iyyar APC ba ta buƙatar dawowar Kwankwaso cikinta saboda tasirinsa a siyasance na ci gaba da gushewa.
Darekta Janar na KASASCO, Kwamared Yahaya Usman Kabo, ya ce jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Abbas ta yi tsayuwar daka da kafa tubalin samun nasara a Zaɓen 2027 da ke tafe, la’akari da cewa tana da Sanatoci biyu da kuma wakilci mai ƙarfi a matakin jiha da tarayya.
Ya bayyana cewa guguwar sauyin sheƙa da ke kaɗawa a jam’iyyar NNPP na da nasaba da tasirin jiga-jigan jam’iyyar da suka tsaya kai da fata wajen tabbatar da nasararta a Zaɓen 2023.
Sai dai ya ce a yanzu jiga-jigan jam’iyyar ta NNPP na ficewa daga cikinta zuwa APC saboda zargin rashin adalci da mayar da su saniyar ware da ’yan Kwankwasiyya suka yi.
Aminiya ta ruwaito cewa daga cikin jiga-jigan NNPP da suka sauya sheƙa zuwa APC a bayan nan akwai Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da Kabiru Alhassan Rurum da Abdullahi Sani Rogo da Zubairu Hamza Massu.
Akwai kuma Abbas Sani Abbas da Baffa Bichi da kuma Sha’aban Ibrahim Sharada.
Ya ce “sauyin sheƙar waɗannan jiga-jigan ’yan siyasa ta karya garkuwar jam’iyyar a Kano. Saboda haka yanzu APC ta warware duk wasu matsalolin cikin gida da take fuskanta domin tabbatar da nasarar a 2027.”
APC ta ce tana da yaƙinin samun nasara a zaɓen da take tafe wanda take fatan bai wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u miliyan biyu a Jihar Kano.
Sai dai ta ce dawowar Kwankwaso jam’iyyar babu abin da zai haifar sai kawo ruɗani a cikinta.
“A yanzu Kwankwaso ba shi da wani tasiri a siyasance, shi ya sa yake neman mafaka da babu inda zai same ta face a jam’iyyar APC.
“Sai dai yana da kyau ya fahimci cewa APC ba wuri ba ne na samun mafaka kuma ba ta buƙatar irinsu [Kwankwaso] da babu abin da za su kawo wa jam’iyyar face ruɗani.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Abdullahi Umar Ganduje Rabi u Musa Kwankwaso jam iyyar APC jam iyyar a a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta bayan sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Illiya Damagum.
Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Anyanwu, wanda yake ɗan tsagin Nyesom Wike, ya ce an dakatar da Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar saboda zargin rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin bin hukuncin kotu.
Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike“Mun yanke shawarar dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ilya Damagum, saboda rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin mutunta hukuncin kotu,” in ji Anyanwu.
“An dakatar da shi na tsawon wata guda, kuma dole ne ya gurfana gaban kwamitin ladabtarwa.”
Anyanwu, ya kuma yaba da hukuncin kotu wanda ya soke babban taron jam’iyyar na ƙasa, inda ya bayyana cewa wannan nasara ce ga mambobin PDP baki ɗaya.
“Muna jinjina wa ɓangaren shari’a bisa wannan hukunci da ya nuna adawa da zalunci da rashin bin doka. Wannan nasara ce ga kowane ɗan jam’iyyar PDP,” in ji shi.
Sauran da aka dakatar sun haɗa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba; mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu, Taofeek Arapaja.
Akwai kuma sakataren kuɗi na ƙasa, Daniel Woyenguikoro; jagoran matasan jam’iyyar, Sulaiman Kadade da mataimakin sakataren jam’iyyar na ƙasa, Setonji Koshoedo.
Sanarwar Anyanwu, na zuwa ne bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da shi da wasu magoya bayan Wike, lamarin da ya ƙara ba tsananta rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP.
Anyanwu, ya kuma sanar da naɗa Alhaji Abdulrahman Mohammed, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban jam’iyyar.