HausaTv:
2025-12-10@15:00:08 GMT

Sheikh Qassem: Duk da wahalhalun, Hizbullah tana da karfinta

Published: 10th, March 2025 GMT

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa, gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon na nan da karfinta, duk da asarorin da ta yi da kuma sadaukarwa.

A wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al Manar, Sheikh Qassem ya bayyana cewa, ‘yan gwagwarmaya a kasar Lebanon sun yi nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta kawo karshen hare-haren da Isra’ila a lokacin da suke kara jajircewa.

Ya jaddada cewa “a koyaushe ana ci gaba da tuntubar juna tsakaninsu da shugaban majalisar Nabih Berri, kuma ba mu yi wata tattaunawa a cikin rauni ba.”

Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa, muddin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta ci gaba da mamayar yankunan Lebanon, to dole ne a tunkare ta ta hanyar gwagwarmaya da ayyukan soji.

Shugaban na Hizbullah ya yi nuni da cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da Lebanon a fili take, babu wata boyayyiyar yarjejeniya da aka kulla, komai a bayyane yake.

Ya yi nuni da cewa, yarjejeniyar ta yi magana karara a kan “kudancin kogin Litani” sau biyar, yana mai cewa, “Wannan shi ne tsarin da ya kamata mu bi.”

“Wannan yarjejeniya wani bangare ne na kuduri mai lamba 1701 na Majalisar Dinkin Duniya na dakatar da ta’addancin Isra’ila,” in ji shi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila

Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana sabbin dabarun tsaron Amurka na cimma maradun gwamnatin Isra’ila ne.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce sabbin dabarun tsaron Kasa na Amurka (NSS) da ke bayyana ka’idojin Washington da muhimman manufofin harkokin waje a zahiri cimma maradun tsaro ne ga gwamnatin Isra’ila ne.

Esmaeil Baghaei ya yi wannan furucin ne a lokacin wani taron manema labarai, kwana biyu bayan gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta bayyana sabbin dabarun tsaron na NSS na 2025.

A kwanan ne gwamnatin Amurka ta sanar da sabbin dabarun tsaron na ta wanda ya tanadi har da soke bada mafaka ga ‘yan kasashen duniya 19.

Kasashe sun suka hada da Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia, Sudan, Burundi, Saliyo da kuma Togo, Afghanistan, Burma, Haiti, Iran, Yemen, Cuba, Laos, Turkmenistan, da Venezuela.

Matakin ya shafi ‘yan kasashen 19 da suka shiga Amurka a ranar 20 ga Janairu, 2021 ko bayan haka don tantance duk barazanar da ke akwai ga tsaron kasar da tsarin jama’a.”

Wannan shawarar ta zo ne bayan da Shugaba Donald Trump da Sakataren Tsaron Cikin Gida Kristi Noem suka yi kira da a tsaurara matakan tsaro kan shige da fice bayan harbin da aka yi wa wasu jami’an tsaron National Guard guda biyu a makon da ya gabata a Washington, D.C.

Wanda ake zargin, dan kasar Afghanistan ne mai shekaru 29 wanda aka ba shi mafaka a watan Afrilu, ya shiga Amurka a shekarar 2021 bayan janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan kuma ya taba yin aiki a wasu hukumomin gwamnatin Amurka, ciki har da CIA, a cewar kafofin watsa labarai na Amurka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167 December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166 December 7, 2025 Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya December 7, 2025 Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba December 7, 2025 Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa December 7, 2025 Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya December 7, 2025 Venezuela: Ba Mu Tsoron Kaudin Amurka Na Wuce Gona Da Iri December 7, 2025 Iran Ta Zama Zakaran  Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21 December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro
  • Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa
  • Australia ta Fara Aiwhatar da Dokar Hana Yara Amfani da Shafukan Sada Zumunta
  • Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi
  • Ministan Makamashi: Iran Tana Da Sanayya Ta Ilimi Na Samar Da Hadari Domin Yin Ruwan Sama
  • Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon
  • ‘Yan Bindiga 18 Sun Muta a Wata Arangama da Rundunar Operation Fansan Yamma
  • ASUU-SSU Ta Zargi VC Da KaryDokokin Jami’ar Jihar Sakkwato
  • Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah
  • Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila