Isra’ila ta aike da tawaga zuwa Doha domin ci gaba da tattaunawar sulhun Gaza
Published: 10th, March 2025 GMT
Gwamnatin Isra’ila ta tura wa tawaga zuwa kasar Qatar a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Isra’ilar da masu shiga tsakani ciki har da Amurka.
Wannan ya biyo bayan tattaunawar kai tsaye da ba a taba yin irinta ba tsakanin Hamas da wakilin Amurka Adam Boehler dake kula da mutanen da akayi garkuwa da su.
Wakilin na Amurka ya sha bayyanawa a baya baya nan cewa Ya yi imanin cewa za a iya cimma yarjejeniya a makonni masu zuwa.
Ya kuma ce Hamas ta shirya tsagaita bude wuta na tsawon shekaru biyar zuwa goma sannan kuma kungiyar ta kwance damara.
Tunda farko dai kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, “suna kira ga masu shiga tsakani a Masar da Qatar, da kuma gwamnatin Amurka, da su tabbatar da cewa ‘yan mamaya sun mutunta yarjejeniyar, da ba da damar shigar da kayayyakin jin kai, da kuma ci gaba da tafiya mataki na biyu na tsagaita.
A nata bangaren dai Isra’ila na son tsawaita wa’adin zangon farko na tsagaita bude wuta har zuwa tsakiyar watan Afrilu, kuma ta bukaci ficewar Hamas daga yankin Falasdinu da ta ke mulki tun shekara ta 2007, da kuma dawo da ragowar mutanen da taka garkuwa da su.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm
Biyo bayan sanarwar hadin gwiwa bayan taro kan tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin Sin da Amurka a birnin Geneva a ranar 12 ga watan Mayun 2025 wato sanarwar Geneva, da tarukan da aka yi a birnin London a ranekun 9 da 10 ga watan Yunin 2025, da wanda aka yi a Stockholm a ranekun 28 da 29 ga watan Yulin 2025, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin da gwamnatin Amurka, sun waiwayi alkawuran da suka dauka karkashin sanarwar hadin gwiwa ta Geneva, kuma sun amince cewa daga ranar 12 ga watan nan na Agusta, za su fara aiwatar da matakai kamar haka:
Amurka za ta ci gaba da gyara matakan karin haraji kan kayayyakin kasar Sin, ciki har da na yankin musammam na Hong Kong da na Macau, wanda tana cikin umarni shugaban kasar mai lamba 14257 na ranar 2 ga watan Afrilun 2025, ta hanyar dakatar da maki kaso 24 na karin har na tsawon kwanaki 90, daga ranar 12 ga watan Agustan bana, yayin da za a ci gaba da aiwatar da karin harajin kaso 10 kan wadannan kayayyaki bisa tanade tanaden wannan umarni.
Ita kuma a nata bangare, kasar Sin za ta ci gaba da gyara matakan karin haraji kan kayayyakin Amurka da aka tanada cikin umarni mai lamba 4 ta 2025, na babbar hukumar kwastam ta majalisar gudanarwar kasar, ta hanyar dakatar da maki kaso 24 na karin har tsawon kwanaki 90, daga ranar 12 ga watan Agustan bana, yayin da za a ci gaba da aiwatar da karin harajin kaso 10 kan wadannan kayayyaki. Haka kuma, Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakan dakatarwa ko cire matakan ramuwa da ba na haraji ba da ta dauka kan Amurka, kamar yadda bangarorin biyu suka amince cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar a Geneva. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp