Lebanon: Wasikar Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma
Published: 1st, December 2025 GMT
A daidai lokacin ziyarar Paparoma Leo na XIV shugaban Katolika na duniya a kasar Lebanon, kungiyar Hezbollah ta fitar da wata sanarwa a hukumance da aka aike masa.
Kungiyar ta yi maraba da ziyarar Paparoma, ta kuma jaddada muhimmancin Lebanon a matsayin kasa mai bambance-bambance na addini da kabilu da akidu, wadda al’ummominta suke bukatar rayuwa tare juna a cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna a zamantakewa da siyasa.
A cikin wannan sakon, Hezbollah ta gabatar da Lebanon a matsayin gada wadda ta hada tsohon tarihi tsakanin Musulunci da Kiristanci da kuma tsakanin al’adu da akidu daban-daban.
Wasikar ta ambaci kalaman Paparoma John Paul II, wanda ya dauki Lebanon ba wai kawai a matsayin gida ba, a’a a ya dauki kasar ne a matsayin daya daga cikin wurare masu tasiri na addinai da aka saukar daga sama.
Hezbollah ta jaddada rawar da kasar ke takawa wajen samar da fahimta tsakanin addinai da al’adu. Wasikar ta nuna cewa rikicin duniya da ya samo asali daga rashin girmama hakkin dan adam, tare da hankoron bautar da shi da kuma tauye masa hakkokinsa, wanda kuma wannan Rashin adalcin ne ya share hanyar kaiwa zuwa ga tashe-tashen hankula da Rashin zaman lafiya a duk inda aka samu hakan.
Wani muhimmin bangare na wasikar ya yi ihara ne ga halin da ake ciki a Falasdinu. Hezbollah ta kira halin da ake ciki a Gaza da “kisan kare dangi a fili” sannan kuma ta bayyana ayyukan Isra’ila a Lebanon shi ma a matsayin “wani zalunci da ba za a yarda da shi ba,” kuma ta dauki wadannan matsalolin a matsayin sakamakon kwadayin gwamnatin Sihiyona na shimfida ikonta a kan albarkatu da filaye na wadannan al’ummomi. Ta kuma jaddada cewa goyon bayan manyan ƙasashe ga Isra’ila a bayyane take haƙƙoƙin al’ummomin yankin ne.
Hizbullah ta kuma nanata alƙawarinta na kasancewa tare da gwamnatin dimokuraɗiyya mai zaman kanta, kiyaye tsaron cikin gida, da kuma fuskantar duk wani zalunci ko mamaye, kuma ta bayyana adawarta da tsoma bakin ƙasashen waje da ke barazana ga ‘yancin kai na Lebanon.
Wasikar ta kuma jaddada abubuwan da suka shafi Musulmai da Kiristoci, kuma ta bayyana mabiyan tafarkin Almasihu a matsayin manzannin zaman lafiya da kare haƙƙin ɗan adam.
Hizbullah ta yi kira ga Paparoma da ya ɗauki matsayi bayyananne wajen nuna Rashin amincwarsa da duk wani rashin adalci da zaluncin Isra’ila a lokacin ziyararsa a Lebanon, da kuma nuna haɗin kai da goyon ga al’ummar Lebanon.
Wasikar ta kammalawa da cewa, Kungiyar Hizbullah na yin fatan alheri da fatan samun nasarar cimma burin tafiyar, na ganin an yada zaman lafiya da karfafa fahimtar juna tsakanin dukkanin Mabiya addinai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala November 30, 2025 MDD: Kasar Somaliya Tana Fuskantar Mawuyacin Yanayi Saboda Fari November 30, 2025 An Yi Ganawa A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Turkiya November 30, 2025 An yi gangami a fadin duniya a zagayowar ranar Falasdinu November 30, 2025 Cinikin Kasashen Waje na Iran Ya Zarce Dala Biliyan 76.5 November 30, 2025 Najeriya : Sojoji sun kubutar da yan mata 12 da mayakan ISWAP November 30, 2025 An sake zabar Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Kamaru November 30, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mika Sunaye Sabbin Jakadun Kasar su 32 Ga Majalisa Domin Tantancewa November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta Bukaci Isra’ila Da ta Kawo Karshen Mamayar Da Tayi wa Yankunan Falasdinawa
Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma yace babu ja da baya game da kudurin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai
Sakataren ya sake yin kira ne saboda ya nuna irin bukatar da ake da ita wajen kare hakkin falasdinawa da kuma matsa kaimi wajen warware rikicin ta hanyar siyasa, adaidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza da labanon da kuma kasar siriya,
Wannan bayanin yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman dar-dar da cin zarafin dan adam ke kara Kamari a yankin Gaza da kuma gabar yammacin kogin Jodan, inda hankalin duniya ya tashi sosai na kashe fararen hula da ake yi , da tilastawa dubbai tserewa , sun bukaci kara kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Alummar falasdinu sun da hakkin a kare musu hakkokinsu da yancinsu da kuma yi musu adalaci , da kuma hakkin tantance makomarsu da kansu, sai dai fiye da shekaru 2 ke nan an take musu hakokinsu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 163 November 29, 2025 Iran A Shirye Take Ta Maida Martani Mai Kan Kan Duk Wata Barazanar Tsaro November 29, 2025 Iran Ta Kakkabo Jiragen Yakin HKI Fiye Da 196 A Yakin Kwanaki 12 November 29, 2025 Trump Ya Bada Sanarwan Rufe Sararin Samaniyar Kasar Venezuela Gaba Daya November 29, 2025 Kamfanin Kera Jiragen Sama Na Airbus Ya Bukaci A Dawo Da Jiragen Sama Samfrin A320 Saboda Gyara November 29, 2025 An Kammala Gasar ‘Rayan’ Na AI Ta Kasa Da Kasa A Nan Tehran November 29, 2025 Iran da Kasashen Larabawa Sun Yi Allah wadai da kutsen sojojin Isra’ila a Kudancin Siriya November 29, 2025 MDD ta yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa November 29, 2025 Lebanon ta shigar da kara ga Kwamitin Tsaro bayan Isra’ila ta Gina katanga a Yankinta November 29, 2025 AU ta dakatar da Guinea-Bissau daga zama mamba a cikinta bayan juyin mulkin sojoji November 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci