Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran
Published: 1st, December 2025 GMT
Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya iso birnin Tehran a jiya lahadi kuma ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar iran Abbas Araqchi.
Ziyarar tasa ana saran za ta kara fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ganin cewa dukkan kasashen biyu suna taka rawa a batutun da suka shafi yanki dama duniya baki daya.
Bugu da kari bayan ganawarsa da Araqchi da musayar ra’ayoyi kan batutuwa daban daban, zai gana da sauran manyan jami’an gwammnatin kasar, da ake saran za su tattauna kan alakar dake tsakaninsu da kuma irin ci gaban da aka samu a yankin da dai sauran batutuwa na kasa da kasa.
Ana sa bangaren shugaban kasar iran Masud pezeshkiyan a lokacin ganawarsa da Hakan fidan ministan harkokin wajen kasar turkiya ya jaddada game da muhimmancin hadin kan kasashen musulmi cikin gaggawa, yace ya kamata kasashen musulmi su rike duba yanayi da yan uwansu suke ciki, kuma a nisanci tsaurara alamura, adaidai lokacin da suke fuskantar matsin lamba daga kasashen waje.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Shugaban Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Kokarin Da Take yi Na Karbe Ikon Kula Da Rijiyoyin Mai Na Kasar December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala November 30, 2025 MDD: Kasar Somaliya Tana Fuskantar Mawuyacin Yanayi Saboda Fari November 30, 2025 An Yi Ganawa A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Turkiya November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Asibitin Kula Da Masu Lalurar Ƙwaƙwalwa Na Kaduna Na Bunƙasa Ta Fannoni Daban-Daban
Asibitin Kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Kaduna na Jagorantar Sauye-Sauren Lafiyar ƙwaƙwalwa a Arewacin Najeriya — Farfesa Aishatu Armiya’u Ta Bayyana Muhimman Nasarori a Shugabanci da Ayyuka da Hadin Gwiwa
Shugabar gudanarwa kuma daraktar lafiya ta Asibitin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa dake Kaduna, Farfesa Aishatu Yusha’u Armiya’u, ta tabbatar da kudirin asibitin na ci gaba da jagorantar gyaran tsarin kula da lafiyar kwakwalwa a Arewa, inda ta ce an samu gagarumin ci gaba wajen fafutukar manufofi, kara yawan ayyuka, da karfafa hadin gwiwa tsakanin sassa daban-daban a cikin shekaru uku da suka gabata.
Farfesa Armiya’u ta bayyana cewa horon da ta samu a shirye-shiryen shugabancin harkokin lafiya na Africa ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta salon shugabancinta da kare muradun lafiyar kwakwalwa, da kuma gina ƙwarewa a fannin.
Ta bayyana shirin a matsayin ginshiƙi wajen karfafa mata kwarewar tsara manufofi da aiwatar da gyare-gyaren tsarin lafiya.
Sauya Fasalin Babban Asibitin na kasa dake Kaduna
A matsayinta na shugabar daya daga cikin manyan asibitocin kula da lafiyar kwakwalwa guda goma na tarayyar Najeriya, Farfesa Armiya’u ta jagoranci sauye-sauren da suka mayar da Asibitin Kaduna cibiyar kula da lafiya ta tunani da jiki, bincike, da horas da kwararru a hanya mai dacewa da al’adu.
A karkashin jagorancinta, asibitin ya kafa dimbin yarjejeniyar hadin gwiwa da kungiyoyin cikin gida da na waje don bunkasa lafiyar kwakwalwa ga al’umma.
Daya daga cikin manyan hadin gwiwar ita ce wadda ake yi da Hukumar Rigakafin Shan Miyagun Kwayoyi da Kula da Lafiyar ƙwaƙwalwa ta Jihar Kaduna wadda ta taimaka wajen samun ci gaba sosai a bangaren manufofi da ayyuka a jihar.
Manyan Nasarorin Manufofi a Jihar Kaduna
Ta hanyar hadin gwiwa da KADSAMHSA, asibitin ya bada goyon bayan fasaha wajen tsara dokoki da tsarin aiki da ake amfani da su wajen sauya fasalin kula da lafiyar kwakwalwa a fadin jihar. Muhimman nasarorin sun hada da:
Sanya magungunan psychotropic a cikin Jerin Muhimman Magungunan Jihar Kaduna na 2025, wanda zai tabbatar da samunsu a cibiyoyin lafiya na matakin farko da na biyu.
Taimakawa wajen tabbatar da dokar Lafiyar ƙwaƙwalwa ta Jihar Kaduna, da amincewa da wata manufa da ke haɗa lafiyar kwakwalwa da cibiyoyin kiwon lafiya na al’umma.
Shirin horaswa da ya kara yawan aikace-aikacensu a fadin jihar, wanda ya bai wa ma’aikatan lafiya 165 horo a manyan asibitoci 15, ciki har da masu kula da samari masu dauke da cutar HIV.
Ta kuma ce asibitin yanzu yana da tsofaffin dalibai 10 na Africa CDC Mental Health Leadership Programme — waɗanda aka horar a Ibadan, Nairobi, da Cairo — kuma kowannensu yana jagorantar muhimman ayyukan gyara.
Inganta Walwalar Ma’aikata da Ingancin Ayyuka
Farfesa Armiya’u ta jaddada cewa jin dadin ma’aikata na daga cikin manyan abubuwan fifiko, inda aka kirkiro sababbin shirye-shiryen da ke inganta lafiyar jiki, tunani da zamantakewa.
Wadannan sun hada da makon lafiya na kowane kwata, wasanni, tarukan zamantakewa, da ingantaccen tsarin inshorar lafiya.
Asibitin ya kuma hade kula da lafiyar jiki cikin ayyukan lafiyar kwakwalwa, tare da kyautata muhalli domin karfafawa da rage wariya.
Wadannan matakai sun kai ga samun babban gamsuwa daga marasa lafiya, inda sama da kashi 90 cikin dari suka bayyana jin dadi da kulawar da suka samu.
Fadada Ayyuka Ta Hanyar Karin Hadin Gwiwa
Asibitin na kara fadada tasirinsa ta hanyar aiki tare da rundunar sojoji, cibiyoyin ilimi, kungiyoyin farar hula, da sauran abokan hulda.
Wadannan hadin gwiwar na taimakawa wajen ba da dama ga karin al’umma su samu kula da lafiyar kwakwalwa a Arewa, tare da karfafa kula da marasa lafiya a cikin al’umma.
Shirye-Shiryen Gaba: Kirkire-Kirkire da Kula da Al’umma
Dangane da makomar asibitin, Farfesa Armiya’u ta bayyana cewa za a kara karfafa tsarin kula da lafiyar kwakwalwa na al’umma, habaka bincike da kirkire-kirkire, fadada amfani da kayan aikin lafiyar kwakwalwa na dijital, da gina karfin ma’aikatan lafiya domin biyan bukatun al’umma da ke ta ci gaba da sauyawa.
Ta jaddada himmar gina tsarin lafiyar kwakwalwa mai tausayi, wanda ba ya takaituwa ga manyan cibiyoyi kawai, kuma ya dace da al’adu — wanda za a iya yada shi a fadin kasar.