’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 12 da ɓacewarsu a Borno
Published: 1st, December 2025 GMT
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno.
Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam.
Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida.
Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu daraja da suka ɓace tun 2012, lokacin da ’yan Boko Haram suka ƙona gidaje da shaguna da yawa a cikin al’ummarmu.”
Ta jaddada cewa, “babu daga cikin zinare da aka samu ya ɓace ko ya lalace a lokacin mamayar Malam Fatori da ’yan ta’adda suka yi fiye da nawa.”
Wani babban jami’in Majalisar Ƙaramar Hukumar Abadam da ya sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya yaba wa ’yan sandan da aka tura don kare rayukan mutane da kadarorinsu a yankin Tafkin Chadi.
Bayan gano tsabar zinare na naira miliyan 23, jami’in ya lura cewa martanin ’yan sanda a ayyukan yaƙi da ta’addanci da ake ci gaba da yi wani abin karfafa gwiwa ne ga sojoji da sauran hukumomin tsaro a yankin Tafkin Chadi, wanda ya ƙunshi qananan hukumomi takwas da ke yankin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon ta shigar da kara ga Kwamitin Tsaro bayan Isra’ila ta Gina katanga a Yankinta
Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon ta sanar a ranar Juma’a cewa ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da gina katanga biyu na siminti a cikin yankin Lebanon da ke kudu da garin Yaroun (yankin Bint Jbeil).
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar ta ce tawagar Jakadancin Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ne ta shigar da ƙarar gaban membobi 15 na kwamitiin Tsaron.
Labanon ta yi kira ga kwamitin Tsaro da Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya da su ɗauki matakan gaggawa don hana Isra’ila keta hurumin Lebanon.
A cewar ƙarar, keta hurumin ya kunshi gina katanga biyu da Isra’ila ta yi a kudu maso yamma da kudu maso gabashin Yaroun, a cikin iyakokin Lebanon da aka amince da su a duniya.
Gina wadannan katanga ya kunshi kwace wani bangare na Lebanon kuma ya zama keta Kudurin kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701 da yarjejeniyar tsagaita wuta ta 2024, ta tanada in ji sanarwar.
Tawagar MDD a yankin wato UNIFIL ta bukaci Kwamitin Tsaro da ya tilasta wa Isra’ila ta rushe katangar biyu tare da tabbatar da cewa ta janye nan take daga kudu da Layin Shuɗi daga duk yankunan da har yanzu take mamaye da su a Lebanon, gami da mashigar kan iyaka guda biyar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka AU ta dakatar da Guinea-Bissau daga zama mamba a cikinta bayan juyin mulkin sojoji November 29, 2025 Najeriya : An yi jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 29, 2025 Larijani: Da’awar lalata karfin nukiliyar Iran wauta ce November 29, 2025 Babban banki Najeriya Ya Tura Dala Miliyan 50 Don Ƙarfafa Kasuwar Musayar Kudade November 29, 2025 Iran Da Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Hare-Haren Isra’ila A Kan Kasar Siriya November 29, 2025 Ziyarar Da Larijani Ya Kai Pakistan Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kara Dankon Zumunci November 29, 2025 Shaikh Niam Qasem: Hizbullah ce Za ta Mayar Da Martani Lokacin Da Ya Dace Kan Kisan Kwamandanta November 29, 2025 Iran Za ta Kauracewa taron fasalta kasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya na shekara ta 2026 November 29, 2025 China Ta Gargadi Amurka Akan Batun Yakar Kasar Venezuela November 28, 2025 Palasdinu: Kwamandoji Biyu Na Rundunar “Sarayal-Quds” Sun Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan November 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci