‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Garin Eruka Na Jihar Kwara
Published: 1st, December 2025 GMT
Daga Ali Muhammad Rabi’u
’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda, kuma ya faru ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin tarayya ta samu ’yantar da mambobin Cocin Christ Apostolic Church (CAC) 38 da aka yi garkuwa da su a yankin.
Majiyar da ta yi magana da Rediyon Najeriya ta ce ’yan bindigar sun farmaki Aasaru ne a wani daji da ke kan hanyar Koro.
Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarta, jami’an ’yan sanda daga sashin Eruku sun karɓi korafi a ranar Lahadi cewa wasu mutane huɗu dauke da makamai sun kutsa wata gona a kan hanyar Koro, Eruku, inda suka sace wani Mista Aasanru mai shekaru 40.
Ejire-Adeyemi ta ce ana cigaba da ƙokari wajen ganin an kubutar da manomin da aka sace.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
An Kammala Gasar ‘Rayan’ Na AI Ta Kasa Da Kasa A Nan Tehran
An kammala gasar gina manhajan komfuta ta kasa da kasa farko a jami’ar Amir Kabir take nan Tehran .
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an gudanar da gasar ne tsakanin kasashe 30 daga yankuna daban daban na duniya, kuma an kammala gasar a jiya Jumma’a 28 ga watan Nuwamban da muke ciki.
Gasar Rayan dai ita ce gasa na manhajan AI ko kirkirarren fasaha mafi girma a duniya. Gasa wanda yake samar da mahaja ya kula da ita tare da amfani da fasahar AI.
Gasar sharar fage ta Rayan wanda aka gudanar a dukkan jihohon Iran ya sami halattar mutane 30,000 daga kasashe 137 a duniya. Amma a gasa ta karshe da aka kammala mutane kimani 100 ne daga kasashen 30 suka sami halattar gasar.
Kasashen da suka halarci gasar sun hana da Amurka, Russia, China, India, Italy, Argentina, Chile, Poland, Romania, Singapore, Vietnam, Colombia, Armenia, Pakistan, Bangladesh, Afghanistan, Australia, Belarus, Serbia, Ethiopia, Ukraine, Taiwan, Kazakhstan, Slovakia, da kuma Iran.
Ministan fasaha da technoloji Hussain Afsheen yace Raya ta fi karfin gasa, sai dai shiri ne na adana fahinta da fasaha.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Kasashen Larabawa Sun Yi Allah wadai da kutsen sojojin Isra’ila a Kudancin Siriya November 29, 2025 MDD ta yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa November 29, 2025 Lebanon ta shigar da kara ga Kwamitin Tsaro bayan Isra’ila ta Gina katanga a Yankinta November 29, 2025 AU ta dakatar da Guinea-Bissau daga zama mamba a cikinta bayan juyin mulkin sojoji November 29, 2025 Najeriya : An yi jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 29, 2025 Larijani: Da’awar lalata karfin nukiliyar Iran wauta ce November 29, 2025 Babban banki Najeriya Ya Tura Dala Miliyan 50 Don Ƙarfafa Kasuwar Musayar Kudade November 29, 2025 Iran Da Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Hare-Haren Isra’ila A Kan Kasar Siriya November 29, 2025 Ziyarar Da Larijani Ya Kai Pakistan Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kara Dankon Zumunci November 29, 2025 Shaikh Niam Qasem: Hizbullah ce Za ta Mayar Da Martani Lokacin Da Ya Dace Kan Kisan Kwamandanta November 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci