Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji
Published: 1st, December 2025 GMT
Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) za ta aika da wata babbar tawaga zuwa Bissau a wannan Litinin.
Tawagar, wacce shugaban ECOWAS na yanzu ke jagoranta, Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, ta hada da shugabannin kasashen Senegal, Cape Verde, da Togo, ko wakilansu don ganawa da sabbin hukumomi, da manyan ‘yan siyasa da na farar hula, don tattauna sharuddan komawa ga tsarin mulki.
“Sakon zai kasance mai karfi,” in ji wata majiya kusa da tawagar ta ECOWAS.
Kafin nan sojojin da suka kwace mulki a Giunea Bissau sun sanar da cewa zasuyi mulkin rikon kwarya na shekara daya.
Tunda farko dama Kungiyar ta (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar ta Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.”
Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Ita ma Kungiyar Tarayyar Afirka, AU ta sanar da dakatar da kasar Guinea-Bissau daga zama mamba a kungiyar bayan hambarar da shugaban kasar, Umaro Sissico-Embalo da sojoji suka yi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran December 1, 2025 Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Maduro Ya Gargadi Amurka Game Da Hankoron Mamaye Rijiyoyin Mai Na Venezuela December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala November 30, 2025 MDD: Kasar Somaliya Tana Fuskantar Mawuyacin Yanayi Saboda Fari November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta nemi hukumomin tsaro su gaggauta bincikar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan zarginsa da kalaman tayar da hankali.
Wannan na zuwa ne bayan kammala zaman majalisar zartarwa na 34 da aka yi ranar Alhamis a Fadar Gwamnatin Kano.
Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi CAF Tayi Watsi Da Alƙalan Wasan Nijeriya a Kofin Afrika Na 2025Zaman ya mayar da hankali kan maganganun da Ganduje da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin suka yi, inda suka ce Kano na ƙara fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga.
Ganduje ya bayyana aniyar ɗaukar mutum 12,000 aiki wanda hukumar Hisbah ta sallama daga aiki, a wata ƙungiya mai alaka da ake kira da “Khairul Nas”.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce waɗannan maganganu na iya kawo koma baya ga harkar tsaro da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi.
Majalisar ta kuma nuna damuwarta cewa ƙasa da awanni 48 bayan yin waɗannan maganganu, aka sake kai hari wasu yankuna na jihar.
Gwamnatin jihar ta sake godewa Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro kan goyon bayan da suke bayarwa wajen yaƙi da matsalolin tsaro.
Haka kuma ta yi gargaɗin cewa ba za ta bari wani ko wata ƙungiya ta kafa haramtacciyar rundunar tsaro ba a Jihar Kano.
A ƙarshe, gwamnatin ta roƙi jami’an gwamnati da’yan siyasa su guji yin maganganun da ka iya tayar da hankali.
Ta kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da doka a faɗin Kano.