Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani
Published: 1st, December 2025 GMT
Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za ta sanyar da sinadarin uranium dinta a kasuwar duniya ga wanda ta ga dama bayan da gwamnatin kasar ta mayar da hakar uranium ga kamfanin kasar a watan Yuni.
Hakar ma’adinan uranium a Nijar na daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali tsakanin gwamnatin soji data kwace mulki a shekarar 2023, da kuma kamfanin Orano, mallakin kasar Faransa wacce ke da kashi 90% a arzikin urinum da ake fitawar shekarun baya.
A wani rahoto da gidan talabijin din kasar ta Nijar ya watsa da yammacin ranar Lahadi, an ambato shugaban kasar, Janar Abdourahamane Tiani, na tabbatar da “hakkin kasar na baje hajarta da albarkatunta da kuma sayar da su ga duk wanda ke son siyan su, bisa ga ka’idodin kasuwanci, cikin cikakken ‘yancin kai.”
Tun lokacin da sojoji suka kwace mulki a juyin mulkin 2023, Nijar ta juya baya ga faransa wacce ta yi mata mulkin mallaka, tana mai zarginta da tallafawa kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji December 1, 2025 Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran December 1, 2025 Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Maduro Ya Gargadi Amurka Game Da Hankoron Mamaye Rijiyoyin Mai Na Venezuela December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Bada Sanarwan Rufe Sararin Samaniyar Kasar Venezuela Gaba Daya
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan rufe zirga zirgan jiragen sama kwata-kwata a kan sararin samaniyar kasar Venezuel daga yau, a cikin shirinsa na fara mamayar kasar.
Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Trump yana fadar haka a shafinsa na sadarwa True Social. Ya kuma bayyana cewa wannan sako ne ga dukkan kamfanonin jiragen sama da matuka jiragen sama.
Trump ya aika da wannan sakon ne bayanda kasashen Espaniya da Potigal suka bukaci dukkan kamfanonin jiragen sama na kasar da su daina wucewa ta sararin samaniyar kasar Venezuela.
Shugaban ya kara da cewa, sojojinsa a shirye suke su shiga farautar masu safarar miyagun kwayoyi a kasar ta Venezuela, a aikin sojojin kasa a cikin yan kwanaki masu zuwa.
A cikin watan satumban da ya gabata jiragen yakin Amurka sun bude wuta kan kwale-kwale sun fi 10 a tashoshin jiragen ruwa na Venezuela inda mutane kimani 80 suka rasa rayukansu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kamfanin Kera Jiragen Sama Na Airbus Ya Bukaci A Dawo Da Jiragen Sama Samfrin A320 Saboda Gyara November 29, 2025 An Kammala Gasar ‘Rayan’ Na AI Ta Kasa Da Kasa A Nan Tehran November 29, 2025 Iran da Kasashen Larabawa Sun Yi Allah wadai da kutsen sojojin Isra’ila a Kudancin Siriya November 29, 2025 MDD ta yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa November 29, 2025 Lebanon ta shigar da kara ga Kwamitin Tsaro bayan Isra’ila ta Gina katanga a Yankinta November 29, 2025 AU ta dakatar da Guinea-Bissau daga zama mamba a cikinta bayan juyin mulkin sojoji November 29, 2025 Najeriya : An yi jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 29, 2025 Larijani: Da’awar lalata karfin nukiliyar Iran wauta ce November 29, 2025 Babban banki Najeriya Ya Tura Dala Miliyan 50 Don Ƙarfafa Kasuwar Musayar Kudade November 29, 2025 Iran Da Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Hare-Haren Isra’ila A Kan Kasar Siriya November 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci