Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta
Published: 1st, December 2025 GMT
Hukumomi a Gaza sun ce akalla Falasdinawa 357 ne sukayi shahada yayin da wasu 903 suka jikkata a hare-haren Isra’ila tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
Yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da yara, in ji ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza a cikin wata sanarwa.
A cewar ofishin, sojojin Isra’ila na kuma tsare da mutane 38 ba bisa ka’ida ba.
ofishin ya ce ya lissafa laifukan tsagaita wuta guda 591, ciki har da harbi kai tsaye kan fararen hula, gidajensu, da tantuna, da kuma bama-bamai da rushe gidaje.
Sanarwar ta ce, wadannan laifukan, suna “nufin mamayar na wargaza yarjejeniyar da kuma haifar da mummunan yanayi wanda ke barazana ga tsaro da kwanciyar hankali a yankin Gaza.”
Ofishin ya yi kira ga Shugaban Amurka Donald Trump, da masu shiga tsakani da kuma masu ba da garantin tsagaita wutar, da kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da su dauki matakai masu inganci don kawo karshen hare-haren Isra’ila da kuma tilasta wa Tel Aviv ta bi dukkan ka’idojin yarjejeniyar.
Yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce Turkiyya, Masar, da Qatar suka shiga tsakani tare da goyon bayan Amurka, ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba don kawo karshen hare-haren Isra’ila na shekaru biyu da suka kashe mutane sama da 70,000, galibi mata da yara, tare da jikkata sama da 170,000 tun daga watan Oktoban 2023.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas : Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta December 1, 2025 Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani December 1, 2025 Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji December 1, 2025 Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran December 1, 2025 Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Maduro Ya Gargadi Amurka Game Da Hankoron Mamaye Rijiyoyin Mai Na Venezuela December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hare haren Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala
Jaridar Washington Post ta buga rahoto akan Shirin Donald Trump na aikewa da sojoji zuwa Gaza, tare da cewa tana fuskantar matsala, domin har yanzu ana Magana akan yadda za a raba ‘yan gwgawarmaya da makamansu.
Jaridar ta ci gaba da cewa; Da akwai damuwa a cikin manyan biranen kasashen duniya danagne da yiyuwar a bukaci sojojin da za a aika su yi amfani da karfi akan Falasdinawa.
A ranar 17 ga watan Nuwamba ne dai kwamitin tsaro na MDD ya fitar da kuduri na amincewa da Shirin da Trump yake da shi akan abinda ya kira zaman lafiya a Gaza.
Kasar Indonesia ta yi alkawalin aikewa da sojojin da za su kai 20,000 domin aikin tabbatar da zaman lafiya. Sai dai kuma kasar tana bukatar ganin an rage yawan aikin da sojojin za su yi.
Ita ma kasar Azerbaijan wacce ta yi alkawalin aikewa da sojoji zuwa Gaza, tana yin bitar abinda ya kamata su yi.
Sai dai har yanzu babu wata kasar larabawa wacce ta yi alkawalin aikewa da sojoji zuwa Gaza a karkashin Shirin an Trump.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD: Kasar Somaliya Tana Fuskantar Mawuyacin Yanayi Saboda Fari November 30, 2025 An Yi Ganawa A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Turkiya November 30, 2025 Iran ta bayyana halin da Falasdinawa ke ciki da rauni mufi da aka wa dan adam a doron kasa November 30, 2025 An yi gangami a fadin duniya a zagayowar ranar Falasdinu November 30, 2025 Cinikin Kasashen Waje na Iran Ya Zarce Dala Biliyan 76.5 November 30, 2025 Najeriya : Sojoji sun kubutar da yan mata 12 da mayakan ISWAP November 30, 2025 An sake zabar Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Kamaru November 30, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mika Sunaye Sabbin Jakadun Kasar su 32 Ga Majalisa Domin Tantancewa November 30, 2025 Hizbullah Ta Bukaci Shugaban Cocin Katolika Na Duniya Yayi Tir Da Hare-haren Isra’ila November 30, 2025 Iran: Kalaman Da Trump Yayi Na Rufe Sararin Samaniyar Kasar Venuzuwela Ya Sabama Doka. November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci