Aminiya:
2025-12-01@08:02:56 GMT

N750,000 kuɗin bikin yaye ɗaliban Jami’ar MAAUN ya tayar da ƙura a Kano

Published: 1st, December 2025 GMT

Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha  (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai.

Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai, kafin ta ba shi takardar shaidar kammala karatu da gabatar da bayanansa domin samun damar halartar aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC).

Sai dai kuma, Hukumar Karɓar Ƙorafi ta Jihar Kano (PCACC) ta umarci iyayen ɗaliban cewa su dakata da biyan kuɗin har sai ta kammala bincike kan ƙorafin da suka gabatar mata a kan lamarin.

Sanarwar da Shugaban Sashen Ayyuka na PCACC, Salisu Saleh, ya fitar bayan samun ƙorafi daga iyayen ɗaliban, ta umarci hukumar gudanarwar Jami’ar MAAUN da ta jingine shirinta na riƙe takardar kammala karatun ɗaliban ko tura sunayensu domin shirye-shiryen NYSC, saboda rashin biyan kuɗin.

’Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a Sakkwato Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano Sojoji sun ceto ’yan mata 12 da ISWAP suka sace a Borno

A gefe guda kuma, hukumar gudanarwar Jami’ar MAAUN ta dage a kan cewa, za ta gudanar da bikin yadda ta riga ta tsara, wanda bai gamsu ba ya tafi kotu.

Mai mallakar Jami’ar MAAUN, Farfesa Abubakar Adamu Gwarzo, ya shaida wa wakilinmu cewa jami’ar za ta gudanar da taron bikin yaye ɗaliban nata kamar yadda ta tsara a cikin wannan wata na Disamba, 2025.

Ya jaddada cewa jami’ar zaman kanta take, don haka tana da ikon sanya kuɗin bikin yaye ɗalibanta.

A cewarsa, kuɗin da MAAUN ta sanya bai kai abin da wata jami’a mai zaman kanta a Jihar ba ta sanya, amma bai ambaci suna ba. Don haka ya kalubalanci Hukumar kan rashin dakatar da biyan kuɗaɗen a ɗaya jami’ar ba.

Ya ce, “Za mu gudanar da bikin a watan Disamba a kamar yadda muka tsara, kuma za mu gayyaci ’yan jarida su ɗauki rahoto.”

Wata wasiƙar ƙorafi a madadin ɗalibai ta nuna damuwa kan yunƙurin tattaunawa da ɗalibai a ɗaiɗaikunsu domin neman ragin kuɗin da jami’ar ta sanya.

Ta bayyana cewa wannan ya saɓa wa abin da aka tsara cewa tattaunawar za ta ƙunshi iyayen ɗalibai da hukumomin jami’ar da kuma wakilan gwamnati.

A yayin da iyaye ke jiran samun tabbacin tsarin da aka yi a hukumance, hukumar gudanarwar Jami’ar MAAUN ta nace cewa babu gudu, babu ja da baya wajen gudanar da taron kamar yadda ta riga ta tsara — duk wanda bai gamsu ba ya tafi kotu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jami ar MAAUN MAAUN kuɗin bikin yaye Jami ar MAAUN

এছাড়াও পড়ুন:

Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya buƙaci Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya daina siyasantar da harkar tsaro a jihar.

Ya ce kamata ya yi gwamnan ya mayar da hankali kan matsalolin da ke damun jihar.

Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali

Barau, ya yi wannan bayani ne bayan gwamnatin Kano ta zarge shi da yin magana inda ya nemi gwamnatin ta mayar da hankali kan tsaro.

Ya ce matsalolin tsaro a ƙasar nan, ciki har da hare-haren ’yan bindiga a wasu yankunan Kano, suna buƙatar haɗin kai daga kowa.

A cikin wata sanarwa daga mai taimaka masa, Ismail Mudashiru, ya fitar, Barau ya ce zargin gwamnatin ba gaskiya ba ne.

Ya ƙalubalanci gwamnatin ta nuna bidiyon da ya yi maganar da za ta iya haddasa matsalar tsaro.

Ya ce wannan zargi ƙarya ne kuma na da nufin ɓata masa suna.

Ya ƙara da cewa bai taɓa yin wata magana da za ta kawo tangarɗa ga harkar tsaro ba.

A maimakon haka, ya ce yana aiki tare da sauran jami’ai domin inganta tsaro a Kano da sauran sassan Najeriya.

Barau, wanda shi ne Mataimakin Kakakin ECOWAS, ya buƙaci Gwamna Abba da ya “farka daga bacci” ya jagoranci jihar yadda ya kamata.

Ya ce a baya Kano na gogayya da Legas wajen ci gaba, amma rashin kyakkyawan shugabanci ya janyo mata koma baya.

Ya ce ya bai wa rundunonin ’yan sanda motocin aiki, ya bai wa jami’an ’yan sanda babura a Kano ta Arewa, sannan ya gyara wasu sassan hedikwatar ’yan sanda ta Kano.

Haka kuma, ya gina ofisoshin ’yan sanda a wurare daban-daban, ya tallafa wa hukumar DSS, sannan ya taimaka wajen kafa makarantu na horar da jami’an NSCDC, Hukumar Ayyukan ’Yan Sanda, da Hukumar Shige da Fice a wasu yankunan Kano.

Ya ce ya sanya fitilu masu amfani da hasken rana a yankinsa domin taimaka wa zirga-zirga da daddare.

A cewarsa, waɗannan ayyukan suna nuna irin gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta tsaro, don haka ya kamata gwamnatin jihar ta yi koyi da shi maimakon ɓata masa suna.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano
  • Kuɗin Cizo ya tilasta rufe fitacciyar sinima a Faransa
  • An Kammala Gasar ‘Rayan’ Na AI Ta Kasa Da Kasa A Nan Tehran
  • Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba
  • Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano
  • Yadda ’yan mata ke kufancewa da kasuwancin fara a Kano
  • DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali
  • Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali