Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-12-01@12:32:39 GMT

Najeriya Ta Kara Ƙaimi Wajen Kawar da Cutar HIV Nan da 2030

Published: 1st, December 2025 GMT

Najeriya Ta Kara Ƙaimi Wajen Kawar da Cutar HIV Nan da 2030

Daga Bello Wakili 

Najeriya ta ƙarfafa ƙoƙarinta na kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030, inda Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ’yan Najeriya, shugabanni da jami’an lafiya su haɗa hannu wajen cimma wannan manufa.

Yayin jawabi a bikin ranar Yaki da Cutar AIDS ta Duniya ta 2025 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu ta jaddada cewa za a iya kawar da cutar HIV a Najeriya idan aka ci gaba da yin aiki cikin tsari, haɗin kai da kuma samun tallafi.

Ta ce duk da cewa an samu cigaba a fannoni na rigakafi, magani da kulawa, ana buƙatar ci gaba da dagewa domin tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya na samun kariya.

Ta yi nuni da muhimmancin yaki da wariya, hantara da nuna bambanci, abubuwan da har yanzu ke hana mutane neman taimako.

Ta kuma jaddada aikin da ake yi a matakin ƙasa na dakile yaduwar cutar daga uwa zuwa jariri, faɗaɗa magungunan yara masu dauke da HIV, da dorewar shirye-shiryen al’amuran da suka shafi cutar ta HIV a cikin gida.

Uwargidar Shugaban Ƙasar ta yabawa Shirin Ƙasa na Yaƙi da Cutar AIDS da STDs saboda ci gaban da aka samu, tare da tallafin Global Fund.

Oluremi Tinubu ta lura cewa ko da yake masu tallafawa daga waje na taka muhimmiyar rawa, gwamnatin tarayya ta amince da dala miliyan 200 domin ƙarfafa shirye-shiryen HIV, tarin fuka da zazzabin cizon sauro.

Ta kuma yaba wa cigaban da Hukumar Kula da  Cutar HIV ta Kasa (NACA) ke samu wajen haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da dogon tsari da ɗorewar shirin ƙasa na dakile cutar ta HIV.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Asibitin Kula Da Masu Lalurar Ƙwaƙwalwa Na Kaduna Na Bunƙasa Ta Fannoni Daban-Daban

Asibitin Kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Kaduna na Jagorantar Sauye-Sauren Lafiyar ƙwaƙwalwa a Arewacin Najeriya — Farfesa Aishatu Armiya’u Ta Bayyana Muhimman Nasarori a Shugabanci da Ayyuka da Hadin Gwiwa

Shugabar gudanarwa kuma daraktar lafiya ta Asibitin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa dake Kaduna, Farfesa Aishatu Yusha’u Armiya’u, ta tabbatar da kudirin asibitin na ci gaba da jagorantar gyaran tsarin kula da lafiyar kwakwalwa a Arewa, inda ta ce an samu gagarumin ci gaba wajen fafutukar manufofi, kara yawan ayyuka, da karfafa hadin gwiwa tsakanin sassa daban-daban a cikin shekaru uku da suka gabata.

Farfesa Armiya’u ta bayyana cewa horon da ta samu a shirye-shiryen shugabancin harkokin lafiya na Africa ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta salon shugabancinta da kare muradun lafiyar kwakwalwa, da kuma gina ƙwarewa a fannin.

Ta bayyana shirin a matsayin ginshiƙi wajen karfafa mata kwarewar tsara manufofi da aiwatar da gyare-gyaren tsarin lafiya.

Sauya Fasalin Babban Asibitin na kasa dake Kaduna

A matsayinta na shugabar daya daga cikin manyan asibitocin kula da lafiyar kwakwalwa guda goma na tarayyar Najeriya, Farfesa Armiya’u ta jagoranci sauye-sauren da suka mayar da Asibitin Kaduna cibiyar kula da lafiya ta tunani da jiki, bincike, da horas da kwararru a hanya mai dacewa da al’adu.

A karkashin jagorancinta, asibitin ya kafa dimbin yarjejeniyar hadin gwiwa da kungiyoyin cikin gida da na waje don bunkasa lafiyar kwakwalwa ga al’umma.

Daya daga cikin manyan hadin gwiwar ita ce wadda ake yi da Hukumar Rigakafin Shan Miyagun Kwayoyi da Kula da Lafiyar ƙwaƙwalwa ta Jihar Kaduna wadda ta taimaka wajen samun ci gaba sosai a bangaren manufofi da ayyuka a jihar.

Manyan Nasarorin Manufofi a Jihar Kaduna

Ta hanyar hadin gwiwa da KADSAMHSA, asibitin ya bada goyon bayan fasaha wajen tsara dokoki da tsarin aiki da ake amfani da su wajen sauya fasalin kula da lafiyar kwakwalwa a fadin jihar. Muhimman nasarorin sun hada da:

Sanya magungunan psychotropic a cikin Jerin Muhimman Magungunan Jihar Kaduna na 2025, wanda zai tabbatar da samunsu a cibiyoyin lafiya na matakin farko da na biyu.

Taimakawa wajen tabbatar da dokar Lafiyar ƙwaƙwalwa ta Jihar Kaduna, da amincewa da wata manufa da ke haɗa lafiyar kwakwalwa da cibiyoyin kiwon lafiya na al’umma.

Shirin horaswa da ya kara yawan aikace-aikacensu a fadin jihar, wanda ya bai wa ma’aikatan lafiya 165 horo a manyan asibitoci 15, ciki har da masu kula da samari masu dauke da cutar HIV.

Ta kuma ce asibitin yanzu yana da tsofaffin dalibai 10 na Africa CDC Mental Health Leadership Programme — waɗanda aka horar a Ibadan, Nairobi, da Cairo — kuma kowannensu yana jagorantar muhimman ayyukan gyara.

Inganta Walwalar Ma’aikata da Ingancin Ayyuka

Farfesa Armiya’u ta jaddada cewa jin dadin ma’aikata na daga cikin manyan abubuwan fifiko, inda aka kirkiro sababbin shirye-shiryen da ke inganta lafiyar jiki, tunani da zamantakewa.

Wadannan sun hada da makon lafiya na kowane kwata, wasanni, tarukan zamantakewa, da ingantaccen tsarin inshorar lafiya.

Asibitin ya kuma hade kula da lafiyar jiki cikin ayyukan lafiyar kwakwalwa, tare da kyautata muhalli domin karfafawa da rage wariya.

Wadannan matakai sun kai ga samun babban gamsuwa daga marasa lafiya, inda sama da kashi 90 cikin dari suka bayyana jin dadi da kulawar da suka samu.

Fadada Ayyuka Ta Hanyar Karin Hadin Gwiwa

Asibitin na kara fadada tasirinsa ta hanyar aiki tare da rundunar sojoji, cibiyoyin ilimi, kungiyoyin farar hula, da sauran abokan hulda.

Wadannan hadin gwiwar na taimakawa wajen ba da dama ga karin al’umma su samu kula da lafiyar kwakwalwa a Arewa, tare da karfafa kula da marasa lafiya a cikin al’umma.

Shirye-Shiryen Gaba: Kirkire-Kirkire da Kula da Al’umma

Dangane da makomar asibitin, Farfesa Armiya’u ta bayyana cewa za a kara karfafa tsarin kula da lafiyar kwakwalwa na al’umma, habaka bincike da kirkire-kirkire, fadada amfani da kayan aikin lafiyar kwakwalwa na dijital, da gina karfin ma’aikatan lafiya domin biyan bukatun al’umma da ke ta ci gaba da sauyawa.

Ta jaddada himmar gina tsarin lafiyar kwakwalwa mai tausayi, wanda ba ya takaituwa ga manyan cibiyoyi kawai, kuma ya dace da al’adu — wanda za a iya yada shi a fadin kasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran
  • Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran.
  • Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku
  • Shugaban Najeriya Ya Mika Sunaye Sabbin Jakadun Kasar su 32 Ga Majalisa Domin Tantancewa
  • Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32
  • Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo
  • Ziyarar Da Larijani Ya Kai Pakistan Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kara Dankon Zumunci
  • Asibitin Kula Da Masu Lalurar Ƙwaƙwalwa Na Kaduna Na Bunƙasa Ta Fannoni Daban-Daban