2025-10-13@22:52:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4875

«Kwalejin Aikin Jinya»:

    BICTOR IKPEBA – 1997 Dan wasan Nijeriya Bictor Ikpeba, ne da ake yi wa lakabi da suna “Prince of Monaco,” Ikpeba ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Monaco ta samu nasarar lashe kofin Ligue 1 ta Faransa. Danwasan ya samu kuri’a 2, inda ya kare a mataki na 32 a cikin jerin...
    An kuma ce duk wani bincike da aka yi a sashen karatu da kundin tsofaffin ɗalibai bai nuna sunansa ba. Wannan binciken ya jefa shakku kan sahihancin takardun ilimin ministan, tare da tayar da ƙura kan yadda gwamnati ke tantance waɗanda ake bai wa manyan muƙaman gwamnati. Duk da cece-ku-ce da ake yi, har yanzu...
    Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar...
    Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren makamashi. Kamfanin ndillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar Hassan Salarieh yana fadar haka a yau Asabar ya kuma kara da cewa, an kammala bangare na farko...
    A ranar 3 ga watan ne hukumar ciniki ta duniya (WTO) ta gudanar da taron shekara-shekara na majalisar kula da harkokin cinikayya karo na uku a birnin Geneva na kasar Switzerland. Kasar Sin ta yi amfani da wannan dama domin daidaita wannan batu, inda ta fallasa tare da sukar matakin “harajin ramuwa” na Amurka daga...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ƙaddamar da shirin tallafa wa mata 1,400 da kayan sana’ar ɗinkin hula domin bunƙasa harkokin kasuwancinsu. A wajen bikin raba kayan, Gwamna Namadi ya ce ɗinkin hula tsohuwar sana’a ce da mata suka gad tun daga iyaye da kakanni, wadda ke taimaka musu wajen dogaro da kai da...
      Me Hakan Ke Nufi Ga Tawagar Nijeriya? Ga Yadda Tsayuwar Rukunin C Yake A ranar 9 ga watan Satumba ne tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta tashi da kunnen doki a wasan da ta buga da tawagar ta Afirka ta Kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya. Bayan wasan ne kasar...
    Ana ta rade-radin an baki sarauta, shin mene ne gaskiyar maganar? Alhamdulillah, maganar an bawa Zahra’u sarauta ba karya ba ne, hakkun haka ne an ba ni sarauta.   Mutane za su so su ji, shin daman Haj. Zahra’u ‘yar Ghana ce, tana da sarauta a Ghana? A’a! Ni ba ‘yar Ghana ba ce, ba...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda ya ke kawo maku kissoshin da suka zo cikin Alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan, wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan  na Aya. Shahida muttahari, kuma kuma cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddin Rumi....
    Akwai amfani saboda watarana wani abu zai taso mai muhimmanci, iyayensa ba sa kusa za su saukaka ta hanyar kiransu. Matsalar sa lalacewar karatu, koyan dabi’un marasa kyau da masu kyau, basu ko siya musu ba laifi ba ne, amma dai a tsananta saka musu ido dan gudun baraka da lalacewa. Ya zamo kiran mai...
    Dagacin garin Kirawa a Ƙaramar Hukumar Gwoza, a Jihar Borno, Abdulrahman Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sa ya tsere daga Najeriya zuwa Kamaru bayan harin Boko Haram. A farkon makon nan, mayaƙan Boko Haram sun kai hari garin Kirawa, inda suka kashe mutum biyu sannan suka ƙone fadarsa. ’Yan bindiga sun sace uwa da...
    Da farko za ki wanke tsamiya sai ki dafa ta ki tace sannan ki wanke danyar citta sai ki nika ta, sannan ki samu roba mai kyau sai ki tace tsamiya tare da cittar kisa suga da filebo sai ki juya sosai ki sa a firij ko ki sa masa kankara. Asha dadi lafiya. Hadadden...
    ’Yan bindiga sun sace wata matar aure da ’ya’yanta biyu a yankin Bareke-Egbe a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma da ke Jihar Kogi. ’Yan bindigar sun kai farmaki gidan wani manomi mai suna Tokpe Gody da misalin karfe 2 na dare ranar Juma’a, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su sace matarsa da ’ya’yansa biyu....
    “Rushewar wannan gada na haifar mana da matsala sosai. Gwamnati ta taimaka ta gyara,” in ji Wayu Bamga, mazaunin yankin. Nanlong Nyas ya ƙara da cewa, “Gyaran da aka yi bai daɗe ba kafin ruwa ya sake lalata gadar.” Wasu direbobi kamar Umar Sa’adu da Abubakar Haruna sun ce duk lokacin da suka isa wurin...
    ’Yan bindigar da ke addabar yankunan karkara sun kaƙaba sun ƙaƙaba musu haraji da ke kaiwa Naira miliyan 10 a Ƙaramar Hukumar Mashegu Jihar Neja. Rahotanni sun nuna cewa an umarci al’ummomin yankunan Babban Rami da Kaboji su su biya Naira miliyan biyu-biyu. Yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami an umarce su da su Naira...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa.   Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta...
    Nijeriya za ta zama kasa mai girma duk da kalubale — Afenifere Kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta nuna kwarin gwiwa cewa kasar za ta kasance mai girma. Sakon wannan kwarin gwiwa ya fito ne daga kakakin kungiyar Afenifere, Kwamared Jare Ajayi, a ranar Asabar yayin da LEADERSHIP Sunday ta tuntube shi a Akure, babban...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta amince da daftarorin zaman lafiya da shugaba Donald Trump ya gabatar, wanda ganin zai kai ga kawo karshen yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Zirin. A wata sanarwa da ta fitar kungiyar “ta bukaci janyewar dukkan sojojin Isra’ila, sannan ta saki dukkan Isra’ilawan da suke tsare...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadin cewa amincewa da takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Iran ba bisa ka’ida ba ya sabawa dokokin kasa da kasa, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su bijirewa haramtattun takunkuman. Jakadan Iran a Colombo Alireza Delkhosh ya bayyana cewa, gargadin na ministan harkokin...
    Kasashen duniya sun fara yabawa kungiyar Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump. Qatar mai shiga tsakanin Isra’ila da Hamas a yakin Gaza ta yaba da matakin da kungiyar ta dauka. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Maged al-Ansari, wanda kuma ya goyi bayan kiran da Donald Trump ya yi na tsagaita bude wuta...
    Mista Fall ya jagoranci tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta kunshi wakilai daga UNICEF, UNESCO, UNDP, UNFPA, da mata na Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron. Ya jaddada cewa canjin al’umma ya ta’allaka ne akan jarin dan’Adam musamman ta hanyar ilmantar da ‘ya’ya mata da karfafa wa mata.   Ya kara da cewa, “tare da...
    Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce Boko Haram sun fi sojojin Najeriya makamai, lamarin da ya sa yaƙin ya zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaron ƙasar nan. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin ƙaddamar da littafin Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce Boko Haram sun fi sojojin Najeriya makamai, lamarin da ya sa yaƙin ya zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaron ƙasar nan. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin ƙaddamar da littafin Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor...
    A wani sabon hari rahotanni sun ce an kashe wani manomi ɗaya yayin da wasu ’yan bindiga suka sace wasu biyar a Tungan-Gari da ke Ƙaramar hukumar Kontagora a gundumar Neja ta Arewa a jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, ’yan bindiga sun kai wa al’ummar garin hari ne da misalin...
    Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance. “Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00...
    Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da sabon Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da aka gina a garin Kumo, Ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne tare da halartar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da kuma Ministan Kula da Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate. NAFDAC...
    Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) a ranar Alhamis ta lalata magunguna da kayayyakin jabu, da wa’adin aikinsu ya ƙare da marasa inganci, da jabun magunguna da darajarsu ta kai Naira biliyan 15 a garin Ibadan na Jihar Oyo. Darakta-Janar ta Hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta sanar...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, har yanzu bai ayyana cewa ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba. Yayin da wasu ’yan siyasa kamar Peter Obi da Rotimi Amaechi suka nuna sha’awar tsayawa takara, Atiku ya ce “lokaci bai yi ba” domin yanke hukunci. Isra’ila ta kame dukkan jiragen ruwan da ke koƙarin...
    Kudubi yana tare da kwayar zarrar kowace halittar Allah, shi yake isar mata da sakon magana, wanda bai zauna da wadannan mazaje ba sai ya ji magana ce mai girma, sai ya ga kamar an maida shi Allah, ya ce mai aka bar wa Allah ragowa, abun ba haka yake ba, abun mammaki da mai...
    Yayin da yake kira ga ‘yan kasa kan cewa, kada su karaya ko fitar da rai daga rabo, Atiku ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa; shekarar 2027, wata dama ce da za a iya amfani da ita wajen kawar da wannan mulki na zalunci, domin tabbatar da ganin gobenmu ta yi kyau. “Babban kyawun demokuradiyya...
    Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan.   A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.   Ya kuma...
    Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar.   Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar.   Gwamnan...
    Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke Zariya.   Da yake jawabi, shugaban gidauniyar Malala, Mista Ziouddin Yousafzai ya yaba da kyakkyawar tarba da aka yi masa tare da tawagarsa, inda ya bayyana Masarautar Zazzau a matsayin...
    Hukumar Kwastam ta Kano/Jigawa ta kama jimillar kafso guda 261,750 na Polyglycine (miligiram 300) da allunan Tramadol hydrochloride 228,700 (miligiram 225) da aka boye a cikin buhunan jumbo guda biyar.   Shugaban hukumar kwastam na yankin Kano, Dalhatu Abubakar, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.   Ya ce an...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda...
    Ministar kula da shari’a da harkokin majalisar dokoki da hakkin mata ta kasar Sao Tome and Principe Vera Cravid ta yi kira a maida dangantakar dake tsakanin kasarta da kasar Sin a matsayin misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, domin dangantakarsu tana da tarihi mai zurfi da kuma samun ci gaba a zamanin...
    Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”.   Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a...
    Gomman matasa a Jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin bayyana goyon baya ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AI Bakori. Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun daga kwalaye da alluna dauke da sakonnin “A bar mana CP”, “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf ka...
    A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa.   Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano. Zanga-zangar...
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun jaddada aniyarsu ta watsi da duk wata barazanar makiya tare da alwashin mayar da martani mai tsanani fiye da harin alkawarin gaskiya da ya gabata A cikin wani sako mai kakkausar murya, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da...
    Rundunar ta kuma bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 11:15 na safe, wata tawagar rundunar ta kama wasu mutane biyu a filin tirela na Dangauro. Sanarwar ta kara da cewa, “An samu wadanda ake zargin dauke da buhu bakwai da ake zargin kayan maye ne wanda aka fi sani...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta yi wata babbar nasarar kama masu baiwa ’yan bindiga makamai da kama wani fitaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi da kuma dillalan makamai ba bisa ƙa’ida ba a wurare daban-daban a faɗin jihar. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da...
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli...
    Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu. Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar...
    Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu...