Iran ta bukaci kasashen duniya su bijirewa haramtattun takunkuman Amurka
Published: 4th, October 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadin cewa amincewa da takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Iran ba bisa ka’ida ba ya sabawa dokokin kasa da kasa, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su bijirewa haramtattun takunkuman.
Jakadan Iran a Colombo Alireza Delkhosh ya bayyana cewa, gargadin na ministan harkokin wajen kasar na kunshe ne a cikin wasikun da ya aike wa takwarorinsa na Sri Lanka da Maldives.
Araghchi ya yi kira ga takwarorinsa na kasashen da su dau mataki mai tsanani kan takunkumin da Amurka da kasashen yammacin Turai suka kakaba iran, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar a ranar 28 ga watan Satumba sake dawo da takunkuman da aka kakaba wa Iran, shekaru 10 bayan dage takunkumin a matsayin wani bangare na yarjejeniyar kasa da kasa mai cike da tarihi kan shirin nukiliyar Tehran.
Wannan matakin na ya zo ne bayan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ki amincewa da kudurin tsawaita dage takunkuman da watanni shida da kasashen China da Rasha suka gabatar.
Kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Jamus ne wadanda suka sanya hannun kan uarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015 ne suka bukaci dawo da takunkuman kan Iran da ake kira “snapback” a watan da ya gabata, bisa zargin Iran da rashin basu haske kan shirinta na nukiliya.
Takunkumin na Majalisar Dinkin Duniya sun tabadi tashe kadarorin Iran a ketare, da dakatar da kwangilar sayen makamai da Iran, da kuma shirin makamanta masu linzami.
Iran, tare da Rasha da China, sauran kasashe biyu da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015, sun ce tsarin yana da nasaba da siyasa kuma ba shi da tushe na doka a karkashin dokokin kasa da kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen duniya na yabawa Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump October 4, 2025 Gaza : Ana ci gaba da tir da Isra’ila kan kai farmaki akan jiragen ruwan agaji October 4, 2025 Madagaska : Shugaba Rajaolina ya ce ‘’ana zanga-zanga ne da nufin tsige shi “ October 4, 2025 Washington Ta Bada Dalar Amurka Miliyon 230 Don Kwace Damarar Hizbullah October 3, 2025 Mutane 5 Sun Mutu Bayan Hari Kan Wurin Bautar Yahudawa A London October 3, 2025 Iran: Larijani Ya Yi Tir Da Kasashen Yamma A Kokarin Tursasawa Iran October 3, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adam Sun Nuna Damuwarsu Da Halin Wadanda HKI Ta Tsare October 3, 2025 Kasar Beljium Ta Ce Bata Amince A Yi Amfani Da Kudaden Rasha Don Yaki Da Ita A Ukraine Ba October 3, 2025 Jam’iyyar PPRD Ta yi Tir Da Hukuncin Kisa Da Aka Yankewa Kabila Na Congo October 3, 2025 Iran: Mas’ud Pezeshkiyan Ya Isa Birnin Bandar Abbas Dake Kudancin Kasar October 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi tir da matakin Australiya na alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci
Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Ostiraliya na ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “mai tallafawa ta’addanci,”
“Matakin da gwamnatin Ostiraliya ta dauka wani abu ne mai laifi ne mai hadari, wanda aka tsara a karkashin gwamnatin Sahayoniya don karkatar da hankalin jama’a daga kisan kare dangi da aka yi a Gaza,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis.
Gwamnatin Ostiraliya ta sanya IRGC a matsayin “mai tallafawa ta’addanci” bisa zarge-zargen da ba su da tushe na cewa IRGC ta shirya kai hare-hare kan Al’ummar Yahudawa na Ostiraliya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da wannan shawarar da babbar murya, tana mai Allah wadai da ita da kuma rashin adalci.
“Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki wannan matakin a matsayin haramtacciyar hanya.”
“Wannan matakin rashin da’a da babban kuskure da gwamnatin Australiya ta aikata bisa zargin da ba shi da tushe da hukumomin tsaro na gwamnatin Saihoyoniya suka kirkira,” in ji ta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ramaphosa ya soki kalaman Trump na cewa ba zai gayyaci shi a taron G20 November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci