Aminiya:
2025-11-18@15:20:07 GMT

An kama masu kai wa ’yan bindiga makamai da ƙwayoyi

Published: 2nd, October 2025 GMT

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta yi wata babbar nasarar kama masu baiwa ’yan bindiga makamai da kama wani fitaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi da kuma dillalan makamai ba bisa ƙa’ida ba a wurare daban-daban a faɗin jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis,  jami’an ’yan sanda da ke aiki da sashen bayanan sirri sun kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Franklin Ozo a Zariya.

Gwamna Fubara ya kori duk Kwamishinonin jihar Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa

An kama shi da ƙunshin ƙwayoyin Exol guda 500, na miliyoyin Naira.

“Bincike na farko ya nuna cewa, an ba da umarnin kai haramtattun ƙwayoyi zuwa garin Kidandan da Giwa, inda aka yi niyyar kai wa ‘yan bindiga,” in ji Hassan.

“A halin yanzu wanda ake zargin yana tsare yayin da ake ci gaba da bincike.”

A ranar ne jami’an tsaro na sashin yakƙi da masu garkuwa da mutane suka bi diddigi tare da kama wani wanda ake zargi mai suna Alhaji Sani wanda aka fi sani da ‘Dan Gude’ a ƙauyen Doka Ilu da ke ƙaramar hukumar Giwa.

An same shi da bindiga ƙirar AK-47, harsashi guda biyu  da kuma wata ƙunson harsashi na AK-47.

‘Yan sanda sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano inda makaman ya fito da kuma gano waɗanda ke da hannu a ciki.

Yayin da aka fi mayar da hankali a kai a kan samemen ’yan bindigar, rundunar ta kuma samu nasarori a wasu ɓangarori da suka haɗa da kama wasu mutane uku da ake zargin masu safarar yara ne a Narayi Kaduna, lamarin da ya kai ga ceto yara biyu da kuma ƙwato shanu 60 da tumaki 25 da ɓarayin suka sace tare da taimakon wani ɗan bindiga da ya tuba.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Rabi’u Muhammad ya yaba wa nasarorin da aka samu, yana mai jaddada cewa katse hanyoyin samar da muggan ƙwayoyi da makamai ga ’yan bindiga shi ne babban abin da ya sa a gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Giwa yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025 Manyan Labarai Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon November 17, 2025 Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
  • GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
  • Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka
  • ’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
  • Da amincewar hukumomi nake tattaunawa da ’yan bindiga — Sheikh Gumi
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
  • Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato
  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran