Hamas ta amince da daftarin zaman lafiya na Trump, amma tare da wasu sharudda
Published: 4th, October 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta amince da daftarorin zaman lafiya da shugaba Donald Trump ya gabatar, wanda ganin zai kai ga kawo karshen yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Zirin.
A wata sanarwa da ta fitar kungiyar “ta bukaci janyewar dukkan sojojin Isra’ila, sannan ta saki dukkan Isra’ilawan da suke tsare a hannunta, masu rai da matattu.
Kungiyar, ta kuma ce sakin zai faru “idan har an tabbatar da yanayin tsarin musayar.”
Don haka, kungiyar ta ce a shirye take ta shiga tattaunawa da masu shiga tsakani domin cimma manufar.
Haka zalika, Hamas ta ce ta amince da mika ragamar mulkin zirin ga wata hukumar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Duk da haka, kungiyar ta bayyana cewa sauran tanade-tanaden da aka ambata a cikin shirin na Trump dole ne a amince da su “ta hanyar cikakken tsarin kafa kasar Falasdinawa wanda Hamas za ta kasance a cikinta kuma za ta ba da gudummawa.”
Tuni dai shugaba Trump wanda ya gabatar da daftarorin guda 20 a farkon makon nan, ya wallafa a shafinsa na Truth cewa Hamas a shirye take don samun zaman lafiya mai dorewa, ya kuma shaidawa Isra’ila cewa dole ne ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta bukaci kasashen duniya su bijirewa haramtattun takunkuman Amurka October 4, 2025 Kasashen duniya na yabawa Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump October 4, 2025 Gaza : Ana ci gaba da tir da Isra’ila kan kai farmaki akan jiragen ruwan agaji October 4, 2025 Madagaska : Shugaba Rajaolina ya ce ‘’ana zanga-zanga ne da nufin tsige shi “ October 4, 2025 Washington Ta Bada Dalar Amurka Miliyon 230 Don Kwace Damarar Hizbullah October 3, 2025 Mutane 5 Sun Mutu Bayan Hari Kan Wurin Bautar Yahudawa A London October 3, 2025 Iran: Larijani Ya Yi Tir Da Kasashen Yamma A Kokarin Tursasawa Iran October 3, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adam Sun Nuna Damuwarsu Da Halin Wadanda HKI Ta Tsare October 3, 2025 Kasar Beljium Ta Ce Bata Amince A Yi Amfani Da Kudaden Rasha Don Yaki Da Ita A Ukraine Ba October 3, 2025 Jam’iyyar PPRD Ta yi Tir Da Hukuncin Kisa Da Aka Yankewa Kabila Na Congo October 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi tir da matakin Australiya na alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci
Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Ostiraliya na ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “mai tallafawa ta’addanci,”
“Matakin da gwamnatin Ostiraliya ta dauka wani abu ne mai laifi ne mai hadari, wanda aka tsara a karkashin gwamnatin Sahayoniya don karkatar da hankalin jama’a daga kisan kare dangi da aka yi a Gaza,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis.
Gwamnatin Ostiraliya ta sanya IRGC a matsayin “mai tallafawa ta’addanci” bisa zarge-zargen da ba su da tushe na cewa IRGC ta shirya kai hare-hare kan Al’ummar Yahudawa na Ostiraliya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da wannan shawarar da babbar murya, tana mai Allah wadai da ita da kuma rashin adalci.
“Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki wannan matakin a matsayin haramtacciyar hanya.”
“Wannan matakin rashin da’a da babban kuskure da gwamnatin Australiya ta aikata bisa zargin da ba shi da tushe da hukumomin tsaro na gwamnatin Saihoyoniya suka kirkira,” in ji ta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ramaphosa ya soki kalaman Trump na cewa ba zai gayyaci shi a taron G20 November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci