A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa.

 

Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano.

Zanga-zangar ta ranar Alhamis ta kasance cikin kwanciyar hankali da bin doka da oda, inda masu zanga-zangar ke jaddada muradin su na CP Bakori ya ci gaba da rike mukaminsa da kuma ci gaba da aikinsa ba tare da cikas na siyasa ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu

Jam’iyyar PDP ta kori Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose da tsohon sakataren jam’iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu.

PDP ta yanke wannan hukunci ne a babban taron jam’iyyar da ake gudanarwa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Gwamnati, UNICEF da ’yan jarida sun haɗa don yaƙar cututtukan da aka manta da su a Gombe Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na yankin Kudu, Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, sannan Samaila Burga, shugaban PDP na Jihar Bauchi, ya mara masa baya.

A baya, tsagin jam’iyyar da ke goyon bayan Wike sun kai ƙara kotu don a hana gudanar da taron.

Amma PDP ta samu hukuncin da ya ba ta damar ci gaba da taron daga Kotun Ƙoli ta Jihar Oyo.

Kwana biyu kafin taron, Mao Ohuabunwa, Shugaban Majalisar Amintattu (BoT) na ɓangaren Wike, ya ce duk wanda ya tafi Ibadan don taron hutu ya je yi, domin doka ba za ta aminta da shi ba.

A cewarsa, Anyanwu ya riga ya fitar da sanarwar ɗage taron.

Ohuabunwa ya ce: “Mun zauna a matsayin kwamitin zartarwa na ƙasa na PDP, muka duba abubuwan da muka yi. Mun yadda da bin hukuncin kotu game da taron Ibadan. Don haka ba mu da hannu a taron.

“Ibadan wurin jama’a ne, mutane na iya zuwa don kowane abu amma ba don babban taro ba. Duk wanda ya tafi can da sunan taro ya ɗauki hakan a matsayin shaƙatawa kawai.

“Ba za mu amince da take haƙƙin kundin tsarin mulki da wasu mutanen ke yi da sunan babban taro ba.”

Muƙaddashin shugaban tsagin, Abdulrahman Muhammad, shi ma ya kira wakilansu da su guji zuwa taron.

Ya ce tsagin nasu zai ci gaba da haɗa kan mambobi a jihohi 36 da Abuja domin ƙarfafa jam’iyyar.

Muhammad ya ce: “Muna kiran dukkanin wakilai su guji zuwa taron Ibadan.”

A nasa jawabin, Wike ya gode wa mambobin jam’iyyar saboda yadda suke tsayawa wajen kare jam’iyyar a yankunansu.

Ya ce su a ɓangarensu za su ci gaba da bin doka kuma ba za su bari a tsoratar da su ba.

Wike, ya kuma ce ba zai taɓa yaudarar waɗanda ke goyon bayan kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.

Ya ce: “Ina farin ciki da yadda kuke nuna damuwa game da jam’iyyar a yankunanku. Zan ci gaba da goyon bayanku, ba zan yaudare ku ba.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
  • Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi
  • Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
  • ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 
  • Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi
  • NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116 
  • ’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
  • Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba
  • Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo
  • PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu