’Yan bindiga sun ƙaƙaba wa ƙauyuka harajin N10m a Neja
Published: 4th, October 2025 GMT
’Yan bindigar da ke addabar yankunan karkara sun kaƙaba sun ƙaƙaba musu haraji da ke kaiwa Naira miliyan 10 a Ƙaramar Hukumar Mashegu Jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa an umarci al’ummomin yankunan Babban Rami da Kaboji su su biya Naira miliyan biyu-biyu.
Yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami an umarce su da su Naira dubu 500, yayin da aka umarci ƙauyukan da ke kusa da Dajin Keji su tara Naira miliyan 10 gaba ɗaya.
Haka nan, ana ƙaƙaba wa al’ummar Khizi an kaƙaba musu harajin Naira miliyan shida, da wa’adin ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025.
Wata mata ta banka wa kanta wuta a Bauchi Sharri Jonathan ke wa Buhari don lashe zaɓen 2027 —Garba ShehuWani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa: “’Yan bindigar sun kashe mutane da dama kuma suna ci gaba da kai hare-hare. Sun kaƙaba haraji ga ƙauyukan da ke gefen dazukan Ibbi da gandun dabbobi na Kanji National Park.
“Muna roƙon gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki, saboda yawancinmu manoma ne, kuma sama da kashi 90 cikin 100 na amfanin gona bai ma kai girbi ba.”
Wata majiyar ta bayyana cewa da dama daga cikin manoma an kashe su ko an yi garkuwa da su a gonakinsu, yayin da matafiya ke fuskantar kwanton ɓauna a kan tituna, wasu kauyuka kuma ana kona su gaba ɗaya.
Rundunar ’yan sanda a Jihar Neja ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Haraji ƙaƙaba haraji Naira miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar.
A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira.
Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar.
A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto.
“Addu’o’inmu suna tare da waɗannan jarumai, iyalansu, da dukan al’ummar Amurka.”
A cewar rahotanni, Shugaba Donald Trump yana gidansa na hutu a Mar-a-Lago da ke Palm Beach, Florida, a lokacin da lamarin ya faru.
Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce cikin wata sanarwa: “Fadar White House ta san da wannan mummunan lamari kuma tana bin diddigi. Shugaban kasa ya samu cikakken bayani.”
’Yan sandan birnin Washington DC sun ce an kama wanda ake zargi da harbin.
Sojojin National Guard sun kasance a Washington DC tsawon watanni a matsayin wani bangare na matakin Trump na yaki da laifuka a babban birnin ƙasar.
A cikin wani rubutu a dandalinsa na Truth Social, Trump ya ce: “Dabban da ya harbi mambobin National Guard biyu, wanda dukkansu suka ji rauni mai tsanani kuma yanzu suna a asibitoci daban-daban, shi ma ya ji rauni sosai, amma duk da haka, zai ɗanɗana kuɗarsa.”