HausaTv:
2025-10-13@15:47:19 GMT

Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan(a) 145

Published: 4th, October 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda ya ke kawo maku kissoshin da suka zo cikin Alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan, wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan  na Aya. Shahida muttahari, kuma kuma cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddin Rumi.

Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirarar ImamAl-Hassan Al-Mujtaba (a) jikan manzon All..(s) kuma dan Fatimah (a) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun yimaganar yakin Nahrawan, inda Imam Amirulmumina(a) ya yaki khawarijawa, wadanda su ne suka bata masa nasaran da yake kusan samu kan rundunar sham,rundunar Mu’awiya dan Abu Sufyan bayanda da suka daga mushafin Alkur’ani wai suna bukatar a alkur’ani ya shiga tsakaninsu. Sun yi haka ne a lokacinda sun ga cewa an kusan samun nasara a kansu.

Imam Ali (a) ya fada masu cewa makircine aka yi maku, ko koma ko karasa nasarar da muka samu, sai suka ki, banda haka suka bayyana tawaye suka yi barazanar kashe shi kamar yadda suka kashe Uthman.

Sannan sun ki amincewa da wadanda ya gabatar masu, a matsayin wakilinsa a alkalancin da za’a yi a Daumata jandal,  wato Abdullahi dan Abbas da kuma Malikul Ashtar. 

Sannan suka tilasta masa  amincewa da Abu Musa Al-ashari a matsayin wakilinsa a alkalancin da aka yi daga baya. Sun san cewa Abu musa makiyinsa ne, shi gwamnansa ne a kufa wanda ya yi masa, tawaye ya kuma tube shi.

Bayan haka alkalan suke bi son zuciyarsu a alkalanci, suka tube Imam Ali (a) kamar yadda yake tsammanin zai faru. Sannan basu bai ishesu ba sai da saka samar da wata akida suna kafirata musulmi daga cikin har da shi amirulmuminina (a), da farko sun ki shiga kufa tare da amirul muminina (a), sai da ya je da kansa ya yi jayayya da su a cikin yan mintoci ya kure su, sannan suka amince suka shiga kufa.

Amma tunda basa da gaskiya, sun kuma tara jahilai suna yaudararsu, suna ingiza mabiyansu kin amirulmuminina, da sauran muminai.

Sannan daga karshe suka tara mutane 12 a Nehrawan  suka kashe mutane ba tare da wani dalili ba.

Kuma da alamun suna da wasu wadanda suke aikiwa mu’awiya a cikinsu. Don duk abinda suke yi a cikin musulmi wanda yake karfafa Mu’awiya ne ya kuma, mai sauran musulmi baya. Sun kashe Abdullahi dan Habbabul Art sahabin manzon All..(s) da kuma matansa dauke da tsohuwar ciki ba tare da dalili ba.

Sun kashe wasu matan uku su ma ba tare dawani dalili ba. Anan ne Amirul muminina(a) ya ga  cewa sun fi mu’awiya hatsari, sai ya karkatar da rundunarsa ta yakar mu’awiya zuwa Nahrawan ya yi magana mai kyau da su, ya tunatar da su kurakuransu tun siffin har zuwa Nehran.

Amma don da al-amarinsu babu hankali acikinsa, sai yaki da mutuwa kawai suke magana, babu magana ta masu hankali daimani . Sai suka farwa rundunar Imam Ali (a) a Nahrawan suka kashe su gaba daya indabanda mutane 9.

Asali su dubu 12,000 a lokacinda Imam Ali (a) ya yi masu magana mutum 8000  daga cikinsu suka tuba suka dawo cikin rundunar Imam Ali(a). Amma 4000 suka dake kan bata,  da kuma jahilci. Sune aka kashe gaba daya sai mutum 9.

Sannan mun bayyanacewa manzon All..(s) yayi maganar bayyanar Khawarijawa kafin bayyanarsu, da kuma wasu daga cikin sahabbansa da zasu kasance cikinsu.

Bayan yakin Nahrawan sun ya raba makamansu a cikin mayakansa da kuma dawakansu. Sannan sauran dukiyoyinsu wadanda suka hada da bayinsu ya barwa magadansu.

Daga nan sai tawayen da sojojin Imam (a) suka yi, don kafin yakin Nehrawan anniyarsa ita ce komawa sham don yakar Mu’awiya dan Abu sufyan .

Amma bayan yakin Nahrawan, sai gajiya ta bayyana a fili ga sojojin, saboda yake-yaken da suka yi a siffin yasa na kashe da dama daga cikinsu. Sojojin sun zama basa son yaki kuma.

To amma yaya Imam(a) zai yi ga Mu’awiya yana kara karfi, idan kuma ya dakatar da yaki to kuma mu’awiya zai zo ya mamaye ko ina har da kufa idan sun ki fita.

Daga karshe ya samu labarin wasu sojojin nasa sun gudu daga inda suke a Nahrawan zuwa kauyuka na kusa don kada a tafi da su Siffin.

Daga karshe Ash’as dan Kai Alkindi ya fito fili ya fadawa Amirul muminina(a) , yana cewa:

(Ya shugaban mumuminai, korimmu sun kare, takubbammu sun rasa kaifinsu, haka ma kawukan masummu dun lalace, ka koma da mu zuwa mazaunimmu, don mu sake tanadi mai kyau, mai yuwa kuma shugaban muminai ya kara yawammu, ya maye gurbin wadanda suka  mutu daga cikimmu wannan zai fi dacewa da mu,  ….) bayan maganar wannan mutum makiri, sai wasu daga cikin sojojin Imam suka sulale suka fice daga rundunar a cikin dare suka je suka boye a cikin kauyukan da suke kewaye da inda suka.

Daga nan Imam (a) ya tabbatar da cewa sun fice daga ikonsa ba kuma abinda zai iya yi, don haka ya ga ba makawa sai ya koma Kufa, sai kawai ya jagoranci sauran suka koma Kufa.

Kuma tun daga lokacin Imam Ali (a) ya kasa samun kan sojojinsa don yakar Mu’awiya dan Abu Sufyan. Yayi kiransu a khudubobinsa a masallacin kufa, yayi kiransu a bayyana a kebe a boye a bayyana ba wanda ya amsa masa sai wadanda ba za’a rasa ba, wadanda ba zai iya fita yaki da su kadai ba.

Sannan babban dalilin da ya sa Imam(a) bai da wadanda zasu amsa kiransa na fitan yaki , shi ne ya rasa mafi yawan sahabbansa masu Ikhlasi, wadanda suka san matsayinsa, kuma basa saba masa a cikin umurninsa a yake-yaken Jamal da Siffin da kuma  Nahrawan.

Manyan-manyan sahabban manzon All..(s) wadanda da su ne Musulunci ya kafu a zamanin manzon All..(s), cikin muhajiru da Ansar, wadanda suka yi shahada a wadan nan yake-yake guda uku, da suna nan da sojojinsa ba zasu saba masa ba.

Imam(a) yayi bakin cikin rabuwa da su, ya yi kukan rashin a wurare da dama, yakan bayyana haka.

Daga ciki wata rana ya haw kan mimbari yana khuduba sai ya ambacesu yana cewa:

{Me ya cutar da yan’uwammu wadanda aka zubar dajininsu a Siffin, duk da cewa basa raye a yanzu, ? sun yi hakuri ne da ci da shan gurbatacce, Hakika sun riski All..ya cika masu ladansu, ya kuma sanyasu a gidan aminci, bayan tsoro a duniya, ina yan uwana wadanda suka kama hanya, kuma suka wuce a kan gaskiya,? Ina Ammar? Ina dan Attayyihan? Ina Zuzshahadatain, ?   ina masu kama da su daga cikin yan’uwansu, wadanda suka kulla alkawali kan kan mutuwa kan tafarkin All..aka yanka kawukansu aka bawa fajirai!}.

Sannan yasanya hannayensa a kan goshinsa yana kuka.

Imam Ali (a) ya yi bakin ciki sosai a kan rashin wadan nan sahabbansa, sahabban manzon All..(s) wadanda suka kasance masan Al-kur’ani mai girma wadanda kuma suka aikata abinda ke cikinsa.

Suna biyayya gareshi ba sa saba masa kamar yadda suna sani a addinin musulunci. Wadannan sahabbansa da ya ambata, suna daga cikin wadanda suka gabatar da rayukansu a wadannan yake-yake don daukaka gaskiya a kan karya. Kamar yadda kuka sani an kashe dukkan mutane a yakin jamal da yakin siffin amma a Nahrawan mutun 9 kacal aka kashe. A jamal da siffin an kashe dubban musulmi a bangarorin biyu. Malaman tarihi sun yi ta sabani kan adadin mayakan Imam Ali (a) a yake-yaken Jamal da Siffin da kuma Nahrawan. Amma an kashe dubban musulmi a yakokin biyu. Da wuya ka sami gidan da bai rasa kowa nasa ba.

Daga cikin wadanda Imam ya amtaba a cikin wadanda suka yi shahada akwai Ammar dan yasir wanda yake dan shekara kimani 90 a duniya a lokacinda ya je yakin Siffin. Ya musulta tun farkon bayyanar addinin musulunci a Makka. Ya halarci dukkan yakoki tare da manzon All..(s). Sannan manzon All..(s) ya ce: Azzalumar runduna ce zata kashe Ammar zai gashi an kashe shi a hannun sojojin Mu’awiya, wanda ya tabbatar da gaskiyar Imam Ali (a).

Ga Zuzshahadataini, sunansa Khuzaima dan Thabit Al-ansari, shi ma yahalarci dukkan yake-yaken farkon musulunci tare damanzon All..(s) shi ma ankashe shi a siffin. An ce da ya ga ankashe Ammar dan yasir A yakin Siffin, sai ya ce na ji manzon All..(s) yana cewa, azzaluman rundunace zata kashe Ammar, sai ya zare takubinsa, ya shiga yaki bai fita ba har aka kashe shi.

Don haka Imam Ali (a) ya rasa masoya da dama a yake-yaken Jamal da Siffin, wadanda da suna nan daransu dabai fada cikin rashin biyayya da kuma rashin da’an da mutanen Kufa suna nusa masabayan yakin Nahrawan ba.

Masu sauraro a nan zamu dasaaya sai kumawata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahmatullahi wabarakatuhu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Raytuwa: Sirar Imam Hassan(a) 144 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan (a) 145 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar ImamHassan(a) 143 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan (a) 142 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa Sirar Imam Hassan (a) 141 October 4, 2025 Araqchi Ya Ce: Bai Kamata Dokar Kasa Da Kasa Ta Zama Abin Wasa A Hannun Amurka Ba October 4, 2025 Guterres Ya Yi Tsokaci Dangane Da Martanin Kungiyar Hamas Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Gaza October 4, 2025 Trump Ya Bukaci Gwamnatin Isra’ila Da Ta Daina Kai Hare-Hare Kan Zirin Gaza October 4, 2025 Babban Jami’in Kungiyar Hamas Ya Karyata Batun Mika Fursunonin Isra’ila Cikin Sa’o’i 72 October 4, 2025 Turkiyya Ta Yi Watsi Da Bukatar Shugaban Amurka Kan Daina Sayen Iskar Gas Daga Rasha October 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yakin Nahrawan a yake yaken wadanda suka masu sauraro

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata  

Ministan kula da harkokin al’umma na kasar Sin Lu Zhiyuan, ya ce cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5-5 na 14 tsakanin 2021 zuwa 2025, walwalar yara da tsoffi a kasar, ta samu gagarumin ci gaba.

Lu Zhiyuan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a cewa, yayin wa’adin shirin, an samar da wani cikakken tsarin bayar da kariya da kulawa ga yara mabukata, wanda ya shafi yaran da ba sa gaban iyayensu saboda wasu dalilai, da yaran da iyayensu suka yi nesa da gida, da yaran da suka kaura, inda a yanzu dukkansu ke cin gajiyar hidimomin kariya da kulawa na kasar.

Har ila yau a wa’adin, kasar Sin ta kammala gyarawa da sake fasalin kayayyakin moriyar tsoffi ga iyalai miliyan 2.24 dake da tsoffin da suke fuskantar matsaloli.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta kuma samar da tsare-tsaren hidimomin kula da tsoffi guda 500 a cikin unguwanni da wasu unguwanni masu dacewa da zaman tsoffi guda 2,990 da kuma dakunan cin abinci 86,000 ga tsoffin. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya October 10, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal October 9, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Falasdinawa Sun Gano Gawakin Wadanda HKI Ta Kashe A gaza  Fiye Da 320 Cikin Kwanaki Biyu Kacal
  • An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje
  • Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
  • Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  • Tarihin Hassan Usman Katsina (1)
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno
  • Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata