Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya
Published: 4th, October 2025 GMT
Me Hakan Ke Nufi Ga Tawagar Nijeriya?
Ga Yadda Tsayuwar Rukunin C Yake
A ranar 9 ga watan Satumba ne tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta tashi da kunnen doki a wasan da ta buga da tawagar ta Afirka ta Kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya. Bayan wasan ne kasar Afirka ta Kudu ta kara zama a saman teburi da maki 17 cikin wasa takwas da ta buga a Rukunin C.
Tawagar Jamhuriyar Benin ke biye mata da maki 14, sai kuma Nijeriya da ke mataki na 3 da maki 11.
Sai dai kuma Nijeriya ta kasance tana da maki daya ne da na Rwanda da ke mataki na 4, sai kuma kasar Lesotho da ke da maki 6 a mataki na 5, sai kuma Zimbabwe ta karshe da maki 4.
Kasashe tara ko 10 ne za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya na 2026, wadda kasashe 48 za su fafata kuma kasashen Amurka da Medico da Canada za su karbi bakunci.
Canjin Da aka samu Bayan Hukunci
A ka’idar wasannin neman gurbin, duk tawagar da ta kare a mataki na daya daga kowane rukuni guda tara na nahiyar Afirka ce za ta samu gurbi kai-tsaye. Daga baya sai a zabo hudu mafiya kokari da suka kare a mataki na 2, inda za a fitar da daya daga cikinsu sannan ta kara da wata tawagar daga nahiyar.
Yanzu da aka rage wa Afirka ta Kudu maki uku, zai zama tana da maki 14 kenan, dai-dai da tawagar kasar Benin, ita kuma kasar Lesotho ta samu karin maki uku zuwa maki tara maimakon shida a baya kafin a kara mata maki uku.
Yanzu wasa biyu ne suka rage wa kowace tawaga, inda Nijeriya take bukatar samun nasara a wasannin guda biyu. Idan ta samu nasara a wasannin da za ta buga da Lesotho da Benin, zai zama Nijeriya da maki 17 ke nan jimilla.
Sai dai kuma hakan zai ta’allaka ne da wasannin sauran kungiyoyin, domin idan Afirka ta Kudu ko Benin daya daga ciki ta ci wasa daya, ta yi canjaras a wasa daya, za ta koma maki 18. Amma idan ta yi rashin nasara a wasa daya, ta ci daya za ta tsaya da maki 17 ne, daidai ke nan da idan Nijeriya ta samu nasara a wasanninta biyu na gaba.
Ita Benin yanzu damarta ta karu, kuma akwai wasa tsakanin Nijeriya da Benin, wasan da za a iya kira da raba gardama domin shi ne wasan Nijeriya na karshe a rukunin na C.
Ke nan Nijeriya ta fi bukatar samun nasara a wasanninta biyu na gaba, sannan Afirka ta Kudu da Benin su rasa wasanninsu biyu na gaba, inda za ta kara da maki 17, su kuma suna 14. Haka kuma idan Nijeriya da Afirka ta Kudu suka karkare da maki daya, Super Eagles na bukatar kwallaye fiye da Afirka ta Kudu haka ita ma Benin. Yanzu haka Afirka ta Kudu na da yawan kwallaye +8, yayin da Nijeriya ke da +2.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
Sojoji a Guinea-Bissau sun ce sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.
Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take.
’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSSWannan na zuwa ne kwana uku bayan ƙasar ta gudanar da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa.
A yau ne aka wayi gari ana ji. harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya tashi hankalin mutane.
Daga bisani kuma dakarun soji suka rufe babban titin da ke zuwa fadar shugaban ƙasar.
A cewar majiyar AFP, sojojin sun karanta sanarwar ƙwace mulkin ƙasar a hedikwatar rundunar da ke babban birnin ƙasar, Bissau.
Cikakken rahoto na tafe…