‘Yan Nijeriya Na Karbar Sakamakonsu Da Hannun Hagu A Wajen Tinubu – Atiku
Published: 3rd, October 2025 GMT
Yayin da yake kira ga ‘yan kasa kan cewa, kada su karaya ko fitar da rai daga rabo, Atiku ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa; shekarar 2027, wata dama ce da za a iya amfani da ita wajen kawar da wannan mulki na zalunci, domin tabbatar da ganin gobenmu ta yi kyau.
“Babban kyawun demokuradiyya shi ne, ‘yancin samun damar kada kuri’a, duk wadanda ake zalunta; musamman mutanenmu a halin da ake ciki yanzu, za su samu damar kawar da wannan azzalumar gwamnati a zabe mai zuwa.
Atiku ya kara da cewa, a shekara 65; Nijeriya ta kasance kasa wadda ke cikin wani yanayi da ya yi kama da mai tafiya a cikin yimbu, sakamakon rashin shugabanci tsawon shekaru da dama da kuma almundahana da ta dabaibaye kasar.
Sai dai, ya bukaci ‘yan Nijeriya su ci gaba da kasancewa cikin kyakkyawan fata da kuma sa ran samun canji nagari a kowane irin lokaci, yana mai jaddada cewa; idan aka samu shugabanci nagari, kasar za ta iya canzawa daga yadda take zuwa wani yanayi mai ban sha’awa da ake iya gani tattare da wasu sauran kasashe.
Shugaban ‘yan adawar, ya kuma yi wa ‘yan Nijeriya kyakkyawan fatan murnar cika shekara 65 da samun ‘yancin kai, da kuma fatan samun zaman lafiya da dorewar tattalin arziki baki-daya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yan Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA