Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar.

 

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar.

 

Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da shirin raba kudaden ya jaddada cewa baya ga biyan kudaden NECO, gwamnatin jihar tana biyan dalibai sama da 155 tallafin karatu na kasashen waje da sama da dalibai 30,000 a fadin kasar nan.

 

 

Shima da yake nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Dokta Danladi Jatau wanda shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi Mista Abel Yakubu Bala ya wakilta ya yaba da yunkurin kawo sauyi da gagarumar gudunmawar da gwamnan jihar ya bayar a fannin ilimi tare da bayyana cewa ayyukan da gwamnan ke yi a fannin na samar da sakamako mai kyau yana mai kira da a ci gaba da gudanar da shi.

 

Ya ce Majalisar Dokokin Jihar za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon bayan da ya dace ga manufofin Gwamnatin Jihar a fannin Ilimi.

 

A nata bangaren, babbar sakatariyar hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Nasarawa, Hajiya Sa’adatu Yahaya ta bayyana cewa sama da dalibai dubu goma sha shida da dari bakwai ne za su ci gajiyar wannan Shirin da ya lakume sama da naira miliyan dari biyar.

 

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta John Mamman wanda ya bayyana muhimmancin shirin ilimi na Gwamnatin Jihar ya bukaci daliban da suka amfana da su yi amfani da kudaden alawus din yadda ya dace

 

Shugaban kungiyar daliban jihar Nasarawa NASSA na kasa, Kwamared Abimiku Ovy David ya yabawa Gwamna Abdullahi Sule bisa wannan karimcin tare da bada tabbacin cewa alawus-alawus din zai taimaka musu wajen tafiyar da karatunsu tare da jaddada aniyar daliban na ci gaba da zama jakadu nagari a jihar a duk inda suke.

 

COV/Aliyu Muraki/Lafia.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamnatin jihar Gwamnatin Jihar jihar Nasarawa alawus alawus

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka

Wani matashi mai shekaru 27, Chukwuebuka Eweni, ya shiga hannun ’yan sanda a birnin New Orleans na ƙasar Amurka, kan zargin kashe mahaifinsa har lahira tare da jikkata ’yan uwansa mata guda biyu a gidansu da ke unguwar Pebble.

Mahaifin matashin malami ne a fannin kimiyyar kwamfuta a Jami’ar Southern ta New Orleans.

Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16

Iyayen matashin waɗanda asalin ’yan Najeriya ne, sun bayyana lamarin a matsayin abin mamaki da ban tsoro.

Sun shaida cewar Chukwuebuka na fama rashin lafiyar ƙwaƙwalwa amma bai taɓa aikata wani mummunan abu ba.

Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin ’yan matan da aka jikkata an sallame ta daga asibiti, yayin da ɗayar ke kwance tana samun kumawar likitoci.

Rundunar ’yan sandan New Orleans ta tabbatar cewa Chukwuebuka yana hannu kuma ana duba lafiyarsa, kafin kammala bincike.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:59 na daren ranar 11 ga watan Nuwamba, 2025.

’Yan sanda sun samu kiran agajin gaggawa, inda suka garzaya gidan da lamarin ya auku suka tarar da mahaifin matashin kwance cikin jini, sannan wasu biyu sun ji rauni.

Yanzu dai ana tuhumar Chukwuebuka da laifuka biyu da suka shafi kashe mahaifinsa da kuma ƙoƙarin kashe ’yan uwansa mata guda biyu.

Ofishin Korer na Orleans Parish, zai bayyana musabbabin rasuwar mahaifin matashin bayan kammala binciken gawar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
  • NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116 
  • ’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
  • Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka
  • Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
  • Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP
  • PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu