Aminiya:
2025-11-18@12:50:32 GMT

Gwamna Fubara ya kori duk Kwamishinonin jihar

Published: 2nd, October 2025 GMT

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa.

A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli da ta yanke na baya-bayan nan.

Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku

Gwamnan, a yayin wani zama da ya yi da hadimansa domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ya gode wa jami’an da ke barin gado bisa ayyukansu da kuma gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnan Jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara, ya godewa ’yan muƙarrabansa bisa ayyukansu da kuma gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.

“Gwamnan ya bayyana mahimmancin ’Yancin kan Nijeriya, ya kuma yi kira ga dukkan ’yan Nijeriya da su yi aiki tare da Shugaban Ƙasa domin gina ƙasa mai zaman lafiya da tsaro da wadata da kyakkyawar makoma ga kowa da kowa.

Gwamnan ya sauke dukkan kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da hukuncin Kotun Ƙoli ya shafa na naɗin nasu nan take.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwamishinoni Siminalayi Fubara

এছাড়াও পড়ুন:

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

A gobe Lahadi ne za a wallafa makalar babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, game da ingiza gina sabbin ginshikan samar da ci gaban kasa masu inganci, daidai da yanayin da kasar ta Sin ke ciki.

Za a wallafa makalar ta Xi Jinping, wanda shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar ne a mujallar Qiushi fitowa ta 22 a bana, muhimmiyar mujallar kwamitin kolin JKS. (Saminu Alhassan)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo November 15, 2025 Daga Birnin Sin An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka November 15, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan  November 15, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
  • GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
  • Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
  • Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba
  • Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya
  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP
  • Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci
  • PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu