Aminiya:
2025-11-18@12:32:40 GMT

An gudanar da zangar-zangar goyon bayan Kwamishinan ’Yan Sanda a Kano

Published: 3rd, October 2025 GMT

Gomman matasa a Jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin bayyana goyon baya ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AI Bakori.

Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun daga kwalaye da alluna dauke da sakonnin “A bar mana CP”, “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf ka kyale mana CP.

Mun kama wani mahaifi kan yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa Iraƙi — NAPTIP Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku

Zanga-zangar na zuwa ne dai bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya caccaki  Kwamishinan ’Yan Sandan kan ƙaurace wa farerin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Larabar da ta gabata.

Yayin da yake jawabi a bikin da aka gudanar a filin wasa na Kofar Mata, gwamnan ya nuna ɓacin ransa kan abin da ya kira “halin rashin kishin ƙasa da kwamishinan ke nunawa a jihar.”

Gwamnan ya zargi kwamishinan da janye jami’an ’yan sanda daga filin taron a daidai lokacin da ake dab da farawa, inda ya buƙaci shugaba Bola Tinubu ya cire shi daga muƙamin.

Gwamnan ya ce, “A ƙarshen jawabina, ina kira ga dukkan hukumomin tsaro da su ci gaba da sadaukar da kansu wajen tabbatar da zaman lafiya a jihohin ƙasar nan, ciki har da Kano.

“Amma musamman hukumomin tsaro a Kano, bai kamata su tsoma kansu cikin siyasar bangaranci ba, domin hakan ba zai amfani kowa ba a Kano da ma Najeriya ba.

“Ina so in yi amfani da wannan dama a matsayina na ɗan Najeriya, ɗan Kano, kuma Babban jami’in tsaron Jihar Kano, in yi Alla-wadai da halin rashin ƙwarewa da nuna bangaranci da Kwamishinan ’Yan Sanda na yanzu ke nunawa,” in ji gwamnan.

Gwamna Yusuf ya ce rashin halartar Kwamishinan da jami’ansa a bikin wani mataki ne da aka yi da gangan, kuma ya ce hakan ya jawo wa jihar kunya a rana mai tarihi.

“Kamar yadda kuke gani, a wannan rana ta tarihi ta bikin ’yancin kai na Najeriya, ya yanke shawarar ya janye daga jerin faretin tare da jami’ansa.

“Wannan mataki ne da ya shafe shi da mutanensa. A matsayina na Babban Jami’in Tsaro na Kano, a madadin gwamnati, ba mu ji dadin wannan hali da Kwamishinan ’Yan Sanda ya nuna ba,” in ji shi.

Haka kuma, gwamnan ya ƙara da cewa zai rubuta ƙorafi a madadin gwamnati da al ummar Kano zuwa ga shugaban ƙasa ta hanyar ofishin bai ba shi shawara kan harkokin tsaro.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Kano

এছাড়াও পড়ুন:

Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

 

Ɓangaren Shari’a a Nijeriya, yana da alhakin bayyana dokoki, kare kundin tsarin mulki, da kuma tabbatar da adalci. An tsara tsarin shari’a a karkashin jagorancin Kotun Ƙoli inda Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) ke kula da ita, sannan Kotun Ɗaukaka Ƙara da Manyan Kotuna a matakin jiha da tarayya.

 

Daga cikin manyan haƙƙoƙin da suka rataya akan ɓangaren Shari’a, akwai fassara kundin tsarin mulki da dokoki don amfani da su a shari’o’i. Sulhunta masu saɓani da kare haƙƙin ‘yan ƙasa da kuma tabbatar da cewa, sauran sassan gwamnati suna aiki a cikin iyakokin kundin tsarin mulki.

 

Amma, mu tambayi kanmu, wai me ke faruwa a ɓangaren Shari’a, ake samun hukuncin Shari’a ɗaya masu karo da juna?

 

An samu ruɗani a Kano a ranar Talata, 29 ga Mayu, 2024 bayan wani umarnin kotu guda biyu masu karo da juna game da taƙaddamar da ta taso kan sarautar Masarautar Kano tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi na II da Aminu Ado Bayero, sarkin da aka sauke.

 

Yayin da Mai Shari’a S. Amobeda na Babbar Kotun Tarayya, Kano, ya umarci Sufeto Janar na ‘Yansanda, Kayode Egbetokun, da Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kano, Hussain Gumel, da su tabbatar da cewa, an bai wa Aminu Ado Bayero dukkan haƙƙoƙin gata da ake bai wa sarakuna, nan take kuma, Mai Shari’a Amina Aliyu ta Babbar Kotun Jihar Kano ta hana ‘yansanda, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), da Sojojin Nijeriya korar Muhammadu Sanusi na II, Sarkin Kano da aka dawo da shi kan kujerar sarautar.

 

Taƙaddamar dai ta fara ne a lokacin da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Bayero daga kan sarautar Masarautar Kano, tare da wasu Sarakuna huɗu na Rano, Bichi, Karaye da Gaya inda kuma ya mayar da Lamido Sanusi a matsayin Sarki bayan soke dokar da tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya yi amfani da ita wajen sauke shi daga kujerar mulki a shekarar 2020.

 

Da yake magana kan halin da ake ciki a Kano, wani lauya mazaunin Abuja, Kennedy Khanoba, yayin da yake tattaunawa da Jaridar PUNCH ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya bar doka ta yi aiki, a ajiye maganar siyasa a gefe, yanzu doka tana hannun gwamnan jihar.

 

Har ila yau, Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) ta nuna rashin jin daɗi game da hukunce-hukuncen da ke karo da juna daga kotuna.

 

Ƙungiyar lauyoyin ta yi wannan kira ne yayin da take yi wa ‘yan jarida bayani kafin Makon Shari’a na 2025, inda ta kuma yi kira da a yi gyare-gyare don daidaita shari’o’in kafin zaɓen dake tafe a ƙasar.

 

Sai dai, shugaban na NBA reshen Akure, ya yi karin haske da cewa, “wani lokacin, yanke hukuncin masu karo da juna, suna tasowa ne daga bambance-bambancen ra’ayoyin alkalai” kuma ya amince cewa Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) tana ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yanayi. Yayin da wasu masu ruwa da tsaki a ɓangaren Shari’a ke zargin ke zargin ɓangaren zartarwa da tsoma baki a Shari’o’in da suke da wani ra’ayi na musamman akai.

 

To, ko meye ke haifar da wannan hukunce-hukuncen masu bugu da juna?

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7 November 15, 2025 Manyan Labarai Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso November 15, 2025 Manyan Labarai NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama November 15, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi
  • ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshe 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano
  • NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
  • Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba
  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo
  • Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso